Connect with us

LABARAI

Ranar Laraba Za Mu Raba Gidajen Sauro A Kano- Gwamnati

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ce a ranar Larabar nan za su fara raba gidajen sauro miliyan 8.4 ga gundumomi 484 a kafatanin kananan hukumomi 44 na jihar Kano. John Ocholi da Dr Bashir Lawan, mataimakin Daraktan dake sashen kula da cututttuka da kuma jagoran shirin na jihar, sune suka bayyana hakan a ziyarar da suka kai wa Sheikh Harun Ibn-Sina, Babban Kwamandan Hisbah na jihar Kano.

Kakakin hukumar, Alhaji Lawan Ibrahim shi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata. Inda ya ce jami’an sun ayyana cutar Maleriya a matsayin wata babbar cuta da ta addabi al’umma.

Sun ce batun raba gidajen sauro za a yi shi ne domin magance cutar Maleriya a fadin jiharnan a wani mataki na magance cutar Maleriya da gwamnatin tarayya ta bullo da shi tare da tsare-tsaren da NMEP suka fito da shi.

.




Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: