Connect with us

LABARAI

Tsaro: Osinbajo Ya Kaddamar Da Atisayen Farauta A Adamawa

Published

on

Mataimakin shugaban kasa, wato Fasto Yemi Osinbajo, ya kaddamar da atisayen Farauta a jihar Adamawa a wani mataki na magance matsalar tsaro da ke addabar jihar. Osinbajo a yayin kaddamar da atisayen, ya mika motoci kirar Hilux guda 60 da kuma babur guda 50 a madadin gwamnatin jihar Adamawa.

Rahotanni sun tabbatar da cewa; za a mika wa wadannan ababen hawan ne ga atisayen Farauta da gamayyar jami’an tsaro a jihar ke gudanarwa. Da yake jawabi a taron a birnin Yola, ya jinjinawa gwamnatin jihar bisa yadda take kokarin ganin ta magance matsalar tsaro da kare rayuka da dukiyoyin al’lumma.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!