Connect with us

RIGAR 'YANCI

Ganduje Ya Sake Nadin Sani Dawaki Shugaban Asusun Amintattun Hukuma Fansho

Published

on

Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya amince da sake Nadin Alhaji Sani Dawaki Gabasawa a matsayin shugaban amintattun na assusun Hukumar Fansho na Jihar Kano wanda aikinsa ya fara nan ta ke.
Da ya ke bayyana gamsuwarsa da kokarin shugaban a lokacin nadinsa na farko a matsayin shugaban amintattun hukumar ta fansho, Gwamna Ganduje ya jinjina wa Sani Dawaki bisa yadda ya gudanar da kyakkyawan shugabanci tare da aiwatar da aikin da a ka damka amanarsa a hannunsa wanda ya haska kaykkyawar makoma a harkokin gudarwar hukumar a Jihar Kano.
“Alokacin jagorancin wannan hukuma a farko, ya yi abinda ya nuna cancantar sake samun damar shugabantar wannan hukuma. Muna matukar farin ciki da ganin irin nasarorin da aka cimma a baya, ka yi abin a yaba kwarai da gaske, kamar yadda ka nuna ma na tabbacin cigaba da wannan kyakkyawan aiki,” in ji Ganduje.
Saboda haka sai Gwamna Ganduje ya bukaci sabon shugaban hukumar da ya yi amfani da sabbin fasahohi irin na zamani wajen gudanar da ayyukansa.
“Idan aka dubi yadda sabbin fasahun zamani suka bayyana, mu na fatan kai ma za ka yi amfani dasu ta hanyar inganta aiwatar da aikace-aikacen hukumar,” a cewarsa.
Gwamna Ganduje ya tabbatar ma sa da cewa zai cigaba da bai wa hukumar fanshon goyon baya domin samun damar ingantawa, jajircewa tare da tabbatar da gudnar da abubuwa abayyane na harkokin hukumar fanshon a Jihar Kano.
“Haka zaliki ina kara kiran shugaban hukumar da ya yi aiki bilhakki da gaskiya don tabbatar da abinda aka sanshi akansa. Wanda zai tafi kafada da kafada da jin dadin ‘yan fanshonmu.” Kamar yadda babban Daraktan yada Labaran Gwamna Abba Anwar ya shaiawa LEADERSHIP A YAU.

Ina Takarar Shugabancin Chanchaga Ne Don Ceto Al’umma – Hon. Kabiru
An nemi jama’a da su tabbatar sun kare kuri’unsu ta hanyar zaben nagartattun ‘yan takarar da zasu rike amanar dukiyarsu, dan takarar shugabancin karamar hukumar Chanchanga a inuwar ADP, Hon. Kabiru Muhammed ne ya yi kiran bayan kammala zaben fidda gwani na ‘yan takarkarun shugabancin kananan hukumomi mai zuwa.
Hon. Kabiru ya cigaba da cewar lokaci ya yi da jama’a za su yiwa kansu zaben mutanen da za su jagoranci kananan hukumomi masu amanar da za su kare masu muradunsu ta hanyar ayyukan raya kasa, wanda zai anfani jama’a.
Maganar yawaitar fitowar ‘yan takarkarun shugabancin kananan hukumomi a fadin jihar bai da nasaba da baiwa kananan hukumomi kudaden su kai tsaye da gwamnatin tarayya tace za ta yi.
Jama’a sun gaji da irin karairayin da aka dinga yi masu wanda yasa da daman matasan mu na zaune kara zube duk da cewar muna da arzikin za a iya anfani da shi wajen samar da gurabun aiki ga jama’a kuma har ita gwamnatin tayi anfani da wannan damar wajen samun kudaden shiga.
Karamar hukumar Chanchaga na bukatat matasa masu kwazo da hikima da kwarewa wajen assasa abubuwan da za su zama alheri ga kasa, idan ka duba a jihar nan mu na da hanyoyin samun kudaden shiga, amma rashin tsari mai inganci ya sa mu ka fi zama koma baya a cikin sauran kananan hukumomin jihar, ba lallai sai mun jira kudaden da ke fitowa daga gwamnatin tarayya ba, zamu yi anfani da hikima da kwarewa wajen hada kai da masana dan inganta karamar hukumar Chanchaga.
Hon. Kabiru ya jawo hankalin matasa da su marawa tafiyar ADP baya wajen ganin an samar da sauyin da zai inganta rayuwar su, ina da tabbacin bangar siyasa da maula da gwamnatin ke alakanta matasan mu suna haka ne dan zama basu da wani shirin inganta rayuwar matasan, dan haka lokaci yayi da mata da matasa zasu ki baiwa goyon baya ga duk wanda ya ke bai da shirin inganta rayuwarsu.
A karamar hukumar nan a na mulki, amma kamar ba shugabanci, hanyoyi sun lalace, da damar unguwannin a karamar hukumar nan ba ka iya shiga musamman a lokacin damana saboda rashin hanya, an bar matasa zube ba karatu ba aiki, shi ya sa ADP ta kuduri aniyar kawo canji a rayuwar jama’a.
“Ina kira ga hukumar zabe ta jiha kamar yadda ta ba mu tabbacin gudanar da zabe bisa adalci, da ta tabbatar tayi hakan, domin duk wani abinda ta ke bukata mun kammala shi,” in ji shi.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!