Connect with us

LABARAI

Goyon Bayan Ganduje Ya Sa KSSSSMB Ta Tallafawa Musabakar RABIDA – Dr. Shehu

Published

on

Shugaban Hukumar Kula da Manyan Makarantun Sakandare na Kano Dr. Bello Shehu ya bayyana cewa kasancewar Al’kur’ani mai girma na dukkannin Musulmi ne kuma rike shi da kuma yi ma sa hidima na kawo gagarimin cigaba kamar yadda Kasar Saudiya ta samu a yanzu ya sa Hukumarsa ta Kano State Senior Secondary School Management Board (KSSSSMB) ta tsaya tsayin daka ta yi rawar gani na bada masauki da horar da su da kuma duk wasu kayayyaki na taimakawa wadannan dalibai da Kyaututtuka da KSSSSMB ta yi bisa samun hadin kai da goyan baya daga Mai Girma Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ga dalibai su ka fafata gasar Karatun Al’kur’ani Mai Girma da Kungiyar RABIDA ta shirya a Makarantar Zahra Sabo Nanono a Nan Kano.
Dan haka Dr. Bello Shehu ya yabawa yan Kwamiti da suka shirya wannan abu na alkairi a kan cewa sun can-canci yabo kan wannan namijin kokari wajen daukaka wannan hanya dake Zaburar da yara wajen neman sani da kuma haddar Al’kur’ani Mai Girma inda yace suma Iyayen yaran sun cancanci yabo da suka sa yayansu a wannan hanya mai daraja Duniya da Lahira.
Dr. Bello Shehu ya bayyana cewa makasudin bayyanar shi a wannan taro shine karfafa Guiwar yara masu wannan Musabaka kuma ya kara da cewa kada yara dalibai su dauka cewa wadannan kyaututtuka daga KSSSSMB na kekunan dinki da sauran taimako daga dinbin Jama’a su dauka cewa an biya sune a wannan ihisanine daga Gwamnati ne da Al’umma domin ya zamana an karfafamusu Guiwa su a kan wannan aiki na alkairi da Allah yayi musu gam-dakatar a rayuwa.
Haka kuma yayabawa babbar Sakatariyya a ma’aikatar Ilimi Hajiya Lauratu Disu kan irin dawainiya da tallafi da goyan baya ta yadda aka samu hadin kai a wannan aiki da Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya Fice a kansa.
Taron dai ya samu Halartar Wakilin Sarkin Kano da Wakilai daga Jihar: Sokoto, Kaduna, Zamfara da wasu Jihohin da suka shiga Wannan Gasar Musabaka ta RABIDA kar kashin kungiyar Gwani Shehu.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: