Connect with us

LABARAI

Gwamnatocin Najeriya Sun Raba Naira Triliyon 3.84 A Farkon

Published

on

Gwamnatin tarayya, gwamnatocin Jihohi da kananan hukumomin kasar nan sun kasafta naira Triliyon 3.84 a tsakaninsu a tsakankanin watan Janairu zuwa watan Yuni na wannan shekarar.
Kamar yanda kididdigar ta nuna, a tsakanin lokacin da ake Magana a kai, Jihohi guda Tara su ke wakiltar kasha 25 na dukkanin Jihohin kasar nan da suka sami sama da abin da suka samu a shekarar 2018.
Lissafin ya nuna cewa, gwamnatin tarayya ta karbi naira Triliyon 1,599, sannan Jihohi 36 na kasar nan sun karbi naira Triliyon 1,335, sannan kananan hukumomin kasar nan guda 774 sun kasafta naira bilyan 792 a tsakaninsu a daidai lokacin da ake Magana a kansa.
Abin da aka samu na naira Triliyon 3.84 a farkon wannan shekarar din, ya gaza kadan a kan abin da aka samu na naira Triliyon 3.94, a irin wannan lokacin a shekarar 2018, amma ya daran ma naira Triliyon 2.78 da aka samu a farkon shekarar 2017.
Hakanan kuma, abin da aka samu a farkon kwata na shekarar 2013 zuwa kwata ta Biyu ta 2019, shi ne mafi karanta tun daga farkon kwata ta hudu ta shekarar 2017 a lokacin da aka samu naira Triliyon 1.700. lissafin ya nuna cewa, lokuta uku na shekarar 2018 ya kunshi jimillan raba sama da naira Triliyon 2 ne.
Lissafin da aka gudanar ta hanyar amfani da kididdigan da aka samu daga ofishin babban akanta na kasa da kuma hukumar kasafta tattalin arzikin kasa ta FAAC, ya nu na cewa, “A farkon kwatar shekarar 2019, jimillan naira Triliyon 1.599 ne aka kasafta wa gwamnatin tarayya.
Wanda hakan ke wakiltar kashi 41,61 na jimillan abin da aka samu a tsakanin wannan lokacin. Wannan adadin kuma shi ne kasa da naira Triliyon 1.652 da aka samu a farkon kwatan shekarar 2018, amma kuma ya daran ma naira Triliyon 1.098 da aka samu a farkon kwatan 2017.
Don haka abin da gwamnatin tarayya ta samu a farkon kwatan shekarar 2019 ya gaza da kasha 3.22 na abin da ta samu a farkon kwatan shekarar 2018, amma kashi 45.56 sama da abin da ta samu a farkon kwatan shekarar 2017.”
Hakanan kuma, jimillan abin da gwamnatocin Jihohi suka samu a farkon kwatan 2019 shi ne, naira Triliyon 1.335, in an kwatanta da naira Triliyon 1.375 da naira Bilyan 923 a shekarar 2018 da 2017 bi da bi. Jihar Delta ta ci gaba da samun kaso mafi tsoka a tsakankanin dukkanin Jihohin kasar nan a wajen rabon, inda ta kwashi naira bilyan 108.7, sa’ilin kuma da Jihar Osun ta karbi kaso mafi kankanta na naira bilyan 10.09. bambancin da ke tsakanin wadannan Jihohin na kudin shigan shi ne naira bilyan 98.6. Jihar ta Delta ta karbi naira bilyan 41.66 ne a farkon kwatan shekarar 2017, amma sai abin yah aura zuwa naira 101.19 a farkon kwatan 2018.
Wannan yana wakiltar kasha 142.89 na samun kari. Kananan hukumomin kasar nan guda 774 sun karbi jimillan naira bilyan 792 a farkon kwatan 2019, in an kwatanta da naira bilyan 795 da 549 a jere da suka samu a farkon kwatan shekarun 2018 da 2017.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!