Connect with us

RIGAR 'YANCI

Ina Takarar Shugabancin Chanchaga Ne Don Ceto Al’umma – Hon. Kabiru

Published

on

An nemi jama’a da su tabbatar sun kare kuri’unsu ta hanyar zaben nagartattun ‘yan takarar da zasu rike amanar dukiyarsu, dan takarar shugabancin karamar hukumar Chanchanga a inuwar ADP, Hon. Kabiru Muhammed ne ya yi kiran bayan kammala zaben fidda gwani na ‘yan takarkarun shugabancin kananan hukumomi mai zuwa.
Hon. Kabiru ya cigaba da cewar lokaci ya yi da jama’a za su yiwa kansu zaben mutanen da za su jagoranci kananan hukumomi masu amanar da za su kare masu muradunsu ta hanyar ayyukan raya kasa, wanda zai anfani jama’a.
Maganar yawaitar fitowar ‘yan takarkarun shugabancin kananan hukumomi a fadin jihar bai da nasaba da baiwa kananan hukumomi kudaden su kai tsaye da gwamnatin tarayya tace za ta yi.
Jama’a sun gaji da irin karairayin da aka dinga yi masu wanda yasa da daman matasan mu na zaune kara zube duk da cewar muna da arzikin za a iya anfani da shi wajen samar da gurabun aiki ga jama’a kuma har ita gwamnatin tayi anfani da wannan damar wajen samun kudaden shiga.
Karamar hukumar Chanchaga na bukatat matasa masu kwazo da hikima da kwarewa wajen assasa abubuwan da za su zama alheri ga kasa, idan ka duba a jihar nan mu na da hanyoyin samun kudaden shiga, amma rashin tsari mai inganci ya sa mu ka fi zama koma baya a cikin sauran kananan hukumomin jihar, ba lallai sai mun jira kudaden da ke fitowa daga gwamnatin tarayya ba, zamu yi anfani da hikima da kwarewa wajen hada kai da masana dan inganta karamar hukumar Chanchaga.
Hon. Kabiru ya jawo hankalin matasa da su marawa tafiyar ADP baya wajen ganin an samar da sauyin da zai inganta rayuwar su, ina da tabbacin bangar siyasa da maula da gwamnatin ke alakanta matasan mu suna haka ne dan zama basu da wani shirin inganta rayuwar matasan, dan haka lokaci yayi da mata da matasa zasu ki baiwa goyon baya ga duk wanda ya ke bai da shirin inganta rayuwarsu.
A karamar hukumar nan a na mulki, amma kamar ba shugabanci, hanyoyi sun lalace, da damar unguwannin a karamar hukumar nan ba ka iya shiga musamman a lokacin damana saboda rashin hanya, an bar matasa zube ba karatu ba aiki, shi ya sa ADP ta kuduri aniyar kawo canji a rayuwar jama’a.
“Ina kira ga hukumar zabe ta jiha kamar yadda ta ba mu tabbacin gudanar da zabe bisa adalci, da ta tabbatar tayi hakan, domin duk wani abinda ta ke bukata mun kammala shi,” in ji shi.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: