Connect with us

LABARAI

Kaduna Zuwa Abuja: ’Yan Sanda Sun Tabbatar Da Sace Mutane Shida

Published

on

Rundunar ‘yan sanda ta Jihar Kaduna, ta tabbatar da sace wasu mutane shida a kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna, wadanda ake kyautata zaton wasu masu garkuwa da mutane ne sanye da tufafin Sojoji suka sace su a ranar Lahadin nan.
Cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar a ranar Litinin da dare, Kakakin rundunar, Yakubu Sabo, cewa ya yi rundunar tana kan kokarin ganin ta ceto mutanan da aka sace.
“Rundunar ‘yan sanda ta sami rahoton mai bata rai daga babban jami’in ‘yan sanda da ke Rijana, cewa a ranar 7 ga watan 9, 2019, da misalin karfe 2330 ta sami wani kiran gaggawa, inda aka shaida mata cewa wasu mutane sanye da tufafin sojoji dauke da makamai sun tsare motar Bas mai lamba ABJ 905 DC a wani waje kusa da Rijana da ke kan babbar hanyar ta Kaduna zuwa Abuja, inda suka sace mutane shida da ke cikin motar zuwa cikin daji.
“Jami’anmu masu zagaye a wajajen sun hanzarta kai dauki zuwa wajen inda suka fafata da barayin mutanan wanda a sakamakon hakan wata mai suna, Rofiat Tijjani 17 da da kuma wani wanda duk cikansu suna da zama ne a Tudunwada Kaduna, sun sami kubuta daga hannun barayin, a lokacin da suke kokarin tserewa.
Tuni ma har an wuce da wadanda su ka kubuta din da kuma motar na su zuwa ofishin ‘yan sanda. “Har yanzun muna kan kokarin ganin mun ceto sauran mutane hudu din ne mu kuma kamo barayin. Hakan dai yana zuwa ne a daidai lokacin da ayyukan sata da yin garkuwa da mutane suke sake bayyana a kan babbar hanyar da kuma wasu sassa na Jihar Kaduna bayan da suka lafa a ‘yan watannin da suka gabata.
Sama da mutane 10 ne da suka hada har da wani dan majalisar Jiha da kuma wani Soja aka sace a makwanni biyu da suka gabata a cikin Jihar. A kwanan nan ‘yan sandan sun kama sama da mutane 25 da a ke tuhuma da yin garkuwa da mutane da kuma kashe wasu da dama.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!