Connect with us

MANYAN LABARAI

Kotu Ta Tabbatar Da Nasarar Buhari A Zaben 2019

Published

on

Kotun sauraron kararrakin zabe a Nijeriya ta yi watsi da karar da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya shigar a gabanta, yana kalubalantar zaben Shugaba Muhammadu Buhari.

Kotun mai alkalai biyar karkashin jagorancin Mai Shari’a Muhammad Garba ta tabbatar da Shugaba Buhari na jam’iyyar APC mai mulkin kasar a matsayin halastaccen wanda ya lashe zaben watan Fabrairun 2019.

Sakamakon da hukumar zaben kasar, INEC, ta fitar ya nuna cewa Shugaba Buhari, mai shekara 76, ya samu kuri’a miliyan 15 da dubu 200 yayin da Alhaji Atiku Abubakar, mai shekara 72, na jam’iyyar PDP ya samu kuri’a miliyan 11 da dubu 300.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: