Connect with us

LABARAI

Makarantar Usuman Bin Affan Ta Yi Bikin Cika Shekaru 23

Published

on

Makarantar Talafawa Al’umma ta Usman Bin Affan da ke Masallacin Juma’a na Marigayi Sheik Jafar Mahmud Adam dake Unguwar Gadan kaya karkashin Jagorancin Daraktan Makarantar Sheik Aliyu Yunus Muhammad ta shirya Bikin cika shekaru 23 da kafuwar Makarantar tare da raba kyaututtuka ga daliban Makarantar a matakai daban daban na azuzuwan Sakandare, Furamare dana Nazere wadanda suka taka rawa wajen kokari a aji ko zuwa a kan lokaci, tsafta da makamantansu wanda ya jawowa daliban kyaututtuka daga Hukumar Makarantar a taron da akayi a ranar Asabar data gabata a harabar makarantar a birnin Kano.
A jawabinsa na maraba shugaban Makarantar Sheik Aliyu Yunus yace wannan Makaranta bata kudibace ta al’ummace na aikin sa kai a matsayin sadakatul jariya kuma makaranta ce da ake yaye dalibai daka iya zuwa ko’ina suyi karatu a kowane fanni na karatu a kowane fanni na ilimi kamr fannin kimiya da fasaha, Tattalin Arziki, Tarihi, ko kuma fannin Arabiya da Addinin Musulunci da sauransu wanda wannan makaranta ce tafarko mai irin wannan tsarin indakuma yabukaci al’umma ta kwaikwayi wannan tsari da kuma taimakawa irin waddannan Makarantu da suka yi fice wajen samawa dalibai Kyakyawar makoma na karanta fannin da mutum ya zaba ya zurfafa iliminsa.
Daga cikin Manyan Baki da suka halaci wannan Biki akwai shugaban Taro Sheik Abdulwahab Abdallah wanda ya bayyana muhimmancin ilimantar da al’umma da cigaban da ake samu Duniya da Lahira sakamakon Ilimi.
Shi kuwa daya daga cikin Iyaye Makusanta na Makarantar Alhaji Alhassan Ahmad Panshekara ya bayyana wannan makaranta ta Usman Bin Affan a Matsayin Zakaran Gwajin Dafi wajen Samawa yayan mu da kannen mu ilimi mai nagarta wanda kan ba yara zama shugabanni na gari masu Ilimi zamani da kuma wayewa da kishin Addininmu na Musulunci a wannan zamani inda kuma ya bukaci kowa ya bada gudun mawarsa wajen cigaban ilimi Kasa da Al’umma mai cike da tausayi dakuma tattalin zaman lafiya.
Haka kuma akwai Mamba na hukumar wannan makaranta Alhaji Ibrahim Danyaro wanda yace wannan makaranta ammata kya-kyawan tsari ta yadda duk dalibinta yanada wayewa ta zamani da kuma yadda zai wakilci Addini a duk inda yasamu kansa na rayuwa.
Inda shima. Dr. Naziru Yasayyadi Gwale Fitace a fannin yiwa Ilimi hidima na yaba da kokari da kwazon daliban wannan makaranta. Wanda kuma ya shawarci al’umma musamman iyayen yara dasu jajirce wajen sauke nauyin da ya haukansu na tarbiya da ilimi.
Dr. Bashir Fantiya da Farfesa Zunnuraini na daga cikin manyan baki a wannan biki. shi kuwa Daraktan Makarantar ta Usman Bin Affan Malam Muhammad Abubakar yace suna iya kokarinsu na ganin sungina daliban wannan makaranta yadda zasu zamo Shugabanni, Malamai Masu aiki da ilimi da sanin mutunci da girman al’umma koda kuwa wadanda ba’a cikin wannan Addinin suke ba ana ilimantar da daliban tsanin darajar mutum koda kuwa wanene wanda wani Jigone dake kawo zaman lafiya a tsakanin al’ummar Najeriya.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: