Connect with us

LABARAI

PAACA Ta Shirya Taro Kan Rashawa A Kano

Published

on

Cibiyar Tabbatar da adalci da dai daito a tsakanin al’umma ta Afirka Karkashin Jagorancin Ezenwa Nwagwu Daraktan Zartarwa na Cibiyar ta PAACA Peering Advocacy and Advancement Center in Africa ta shirya taron wayar da kan shugabannin Al’umma na Kano yadda za’a yaki cin hanci da rashawa a tsakanin Al’umma tundaga Matakan Shugabancin Al’umma zuwa kasa kamar yadda Daraktan zartarwa MR Ezenwa Nwagwu ya tabbatar da haka a lokacin taron na rana daya wanda akayi a ranar laraba da ta gabata a Birnin Kano.
Shugabannin Al’ummar da akatara a wannan taro dan wayar da kansu akan yadda zasu yaki cin hanci da rashawa a tsakanin Al’ummar da suke shugabanta sun hada sarakunan Gargajiya, Limamai, da Shugabannin Kiristoci da sauran masu ruwa da tsaki akan yaki da cin hanci da rashawa kamar wakilai daga Hukumar EFCC, ICPC da dai makamantan su yadda za’a kawar da wannan dabi’a data addabi Najeriya dama sauran wasu Kasashen Duniya.
Haka zalika a taron an shirya mahawara da tambayoyi a tsakanin shugabannin al’umma akan irin kalubalan dake cikin wannan aiki na yaki da cin hanci da rashawa da kuma irin matsalolin da ake fuskanta musamman irin abu yashafi shugabanci na siyasa da kuma banbancin jam’iyu dakan kalla abun a matsayin hamayyar siyasa duk lokacin da akayi musu hannunka mai sanda dan yin gyara a wani abu da ya sabawa doka.
Masana Shugabannin al’umma da Wakilan Hukumomi ne suka gabatar da bayanai akan yadda cin hanci da rashawa yake da kuma illarsa wajen kawo cikas ga cigaban Kasa da Al’ummarta.
Kadan daga cikin wanda sukayi jawabi a wurin akwai shugaban Majalisar Malalai ta Kano Sheik Ibrahim Khalil wanda ya bayyana cin hanci da rashawa da cewa yafi kala 100 inda yace duk wanda ya koyi bayan barna, ha’inci, Kin gaskiya, Munafunci, Rashin adalci, Rashin Mika Hakki ga mai shi da makamantansu suna daga cikin cin hanci da rashawa a tsakanin al’umma.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!