Connect with us

LABARAI

Ranar Ashura: Muzaharar Shi’a Ta Rikide Tashin Hankali A Bauchi

Published

on

A muzaharar da su ka gudanar a garin Bauchi jiya ta ranar Ashura, an samu rigima a tsakanin ‘yan sanda da kuma almajiran Sheikh Ibraheem Zakzaky, wadanda a ka fi sani da ’yan Shi’a, inda muzaharar ta rikide ta zama tashin hankali.
Lamarin ya samo asali ne tun bayan da ‘yan sandan suka tare gabar masu muzaharar ta Ashura wanda mabiya Mazhabar Shi’a suka saba gudanarwa duk shekara a fadin duniya.
Hatsaniyar ta fara auku ne da wuraren karfe 10 na safiyar jiyan tun daga shataletalen Kasuwar Central Market suka nausa titin unguwar Malam Goje ana ci gaba da fafatawa har zuwa kwanar Tashan Babiye da ke kwaryar jihar.

Wani ganau ya shaida ‘yan jarida cewar ‘yan Shi’ar sun fito sanye da bakaken kaya da tutoci suna tafiya ne sai tawagar jami’an ‘yan sandan suka bude musu ruwan tiyagas da alburusai. Ganau wanda ya nemi a sakaye sunansa, ya shaida cewar ‘yan sandan sun bude wa masu muzaharar ranar Ashurar ruwar tiyagas daga baya suka yi amfani da harsasai masu rai domin tarwatsa su.
Babu wata hukuma da ta tabbatar da adadin wadanda suka mutu, sai dai wasu ‘ya’yan kungiyar ta shi’a sun yi ikirarin ‘yan sandan sun kashe musu mambobinsu guda biyu da jikkata musu mutune kusan 20.
Wakilinmu ya shaida mana cewar a gefe guda kuma mambobin ‘yan uwa musulman suna kuma kara kiran gwamnati da ta sake musu shugabansu Malam Zakzaky wanda yake tsare a hannun DSS tun a watan Disamban shekarar 2015.
Bayanai sun tabbatar da cewar ‘yan sandan sun jikkata mambobin da dama gami da kame wasu da daman gaske daga cikinsu. Ganau wanda ya nemi ‘yan jarida su rufe sunansa, ya shaida cewar ‘yan shi’a da daman gaske ne ya ga lokacin da ‘yan sandan suka kame su.

Ya ce, “Tun da sanyin safiya ‘yan shi’a suka fito suna gudanar da muzaharar tasu, sai ‘yan sanda suka kulle hanya suka bude ruwar tiyagas a kansu domin tarwatsa su.
“Tun daga titin Santaral suka kulle hanyar amma ‘yan shi’ar suka dage sai da suka bude hanyar da ‘yan sandan suka rufe su ka cigaba da tafiyarsu.
“Sannan, ‘yan sandan sun bude musu ruwar harsasai da dama daga cikinsu sun jikkata. Sannan da kuma yawansu ne ‘yan sanda suka kamasu,” A cewar shi.

Ya kara da cewa, “Ina wuraren kasuwar santaral tun daga karfe 10 har zuwa 12 na ga shaguna da dama an kulle domin jama’a suna tsoron rasa rayukansu.
Hakan ya faru ne a sakamakon yadda tiyagas ya yi ta shiga gidajen da shagunan mutane da suke kusa da wurin,” a fadin shi.
Wakilinmu ya tuntubi jami’in hulda da jama’a na Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi DSP Kamal Datti Abubakar inda ya tabbatar da cewar sun kame mambobin Shi’a guda 28 da suka fito gudanar da wannan muzaharar, ya shaida cewar tun usuli sai da aka hana ‘yan uwa musulman gudanar da wannan jerin gwano ta ranar Ashurar amma suka ki ji.
Ya ce, tun a farko sun bi matakan da suka dace wurin ganin ba a kai ga samun matsalar ba, inda ya tabatar da cewar za kuma su dauki matakan da suka dace wajen ganin an shawo kan matsalolin.

A cewar DSP Datti, “Abun da ya faru daga bangaren ‘yan sanda mun yi kokarin wajen ganin ba akai ga samun wannan matsalar ba, ta hanyoyin da muka bi, mun shigo da shugabannin sarakuna mu ka nemi da su yi wa shugabannin bangaren ‘yan shi’a da cewar su yi hakuri su fasa abun da su ke son yi a yau (jiya) duk da sun kirasu sun yi mu su magana, amma dai ba su ji shawarar ba, har suka fito muzahararsu.
“Bayan da suka fito ne kuma jami’an ‘yan sanda su ka tarwatsasu inda aka kame mutum 28 daga cikinsu,” a cewarshi.
Sai dai ya shaida cewar babu tabbacin da zai bayar na rasa rayuka a daidai wannan lokacin da a ka tuntube shi, “Gaskiya mu dai a rahotonmu da ke hanun ‘yan sanda mu na da mutum 28 da muka kama, ba mu da rahoton mutuwar wani har zuwa yanzu,” A cewar shi.
Ya fadi kan cewar za su dauki matakan da suka dace wajen ganin an shawo kan matsalar cikin ruwan sanyi ba tare da kara zuwa irin wannan matakin ba.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: