Connect with us

LABARAI

Tsohon Editan LEADERSHIP Ya Zama Kakakin Tambuwal

Published

on

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya aminta da nada Muhammad Ahmad Bello a matsayinsa Mashawarcinsa na musamman kan yada labarai da hulda da jama’a. Kafin wannan mukamin Bello wanda ya kwashe sama da shekaru 20 yana aikin jarida ya yi aiki da jaridar LEADERSHIP a matsayin Editan LEADERSHIP Friday da kuma LEADERSHIP Weekend wadda ke fita a ranakun karshen mako. Kafin shiga LEADERSHIP, gogaggen dan jaridar ya yi aiki da The Authority a matsayin Mataimakin Edita.

Bello wanda ya ji gishirin aikin jarida tare da kaiwa kololuwar matsayin aikin yada labarai ya samu shaidar kammala digiri na daya a fannin nazarin halayyar dan Adam a Jami’ar Bayero da ke Kano a 1994 da digiri na biyu a jami’ar Nile da ke Abuja. Sabon Kakakin Gwamna Tambuwal ya fara aikin jarida a Jaridar Triumph mallakar Gwamnatin Kano a inda har ya zama Mataimakin Editan Sunday Triumph. Haka ma ya yi aiki da jaridun The News, TEMPO da kuma PM News a matsayin wakilin yankin Arewa-Maso-Yamma da ke zaune a Kano. Bugu da kari ya taba zama mai aika labarai na Gundumar Funtua Kamfanin Dillancin Labarai, NAN,

Bello wanda ke da alhakin tallata Gwammatin Tambuwal tare da daga daraja da kimarta a idanun duniya ya taba zama Edidan THISDAY na shiyya a yankin Kudu-Maso Kudu haka ma ya taba zama mai daukar labarai a Fadar Shugaban Kasa da Majalisar Wakilai na jaridar a 2012-2015. Fitaccen dan jaridar ya taba zama da sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA) a Fatakwal tare da zama shugaban yankin na Daily Trust. Haka ma ya yi aiki a gajeren lokaci da kamfanin dillancin labarai na Kasar China, Xinhua da kuma jaridar The Will ta yanar gizo a matsayin dan jarida mai zaman kansa.

Bello dan shekaru 51 wanda ke da mata daya da ‘ya’ya hudu, kwararren dan jarida ne wanda ya san ciki da wajen aikin jarida tare da sanin makamar yayata, ayyuka, shiraruwa da manufofin Gwamnati. Bello ya samu ci-gaban zama mai magana da yawun Gwamnatin Tambuwal ne a yayin da Gwamnan wanda shine Mataimakin Shugaban Kungiyar Gwamnonin Nijeriya ya daga darajar Daraktansa na yada labarai, Malam Abu Shekara zuwa matsayin Babban Sakatare.

 

 
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: