Connect with us

LABARAI

Yau Za A Fara Dawo Da ‘Yan Nijeriya Gida Daga Afrika Ta Kudu

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ce za ta fara jigilar maido da ‘yan Nijeriya mazauna kasar Afrika ta kudu, gida a yau Laraban nan, a sakamakon rikicin nuna wariya da ake yi a can kasar ta Afrika ta kudu.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ne ya bayar da umurnin a fara kwashe ‘yan Nijeriya din da suke a can kasar ta Afrika ta kudu, wadanda kuma suke son dawowa gida a kashin kansu ba tare da bata lokaci ba.
Jakadan Nijeriya a can kasar Afrika ta kudu din ne ya bayyana hakan a birnin Johannesburg, a jiya, inda ya bayyana cewa, wani Jirgin sama na kasar nan, “Air Peace, shi ne zai fara jigilar ‘yan Nijeriya din a yau Laraba, inda zai fara da kwaso ‘yan Nijeriya 320.
Bayansa kuma wani zai biyo da gaggawa. Shugaba Buhari ne ya bayar da umurnin hakan a bayan da ya karbi rahoton Jakadansa na musamman da ya aike da shi can kasar ta Afrika ta kudu, Ambassada Ahmed Rufai Abubakar, wanda shi ne babban daraktan hukumar binciken sirri ta kasa (NIA).
Shugaba Buhari, a cewar sanarwar da babban mai ba shi shawara a kan harkokin manema labarai, Femi Adesina, ya fitar, ya karbi sakamakon rahoton ne sannan sai ya umurci Ministan harkokin kasashen waje da ya ci gaba da yin amfani da hukumomin da suka dace wajen daukan matakan da suka kamata a kan lamarin ‘yan Nijeriya a kasar ta Afrika ta kudu.
Shugaba Buhari ya karfafa bukatar kasar ta Afrika ta kudu da ta hanzarta daukan matakan da suka dace na ganin ta dakatar da rikicin da ake yi din a kan ‘yan kasar nan da sauran ‘yan kasashen Afrika. Sai dai kuma, shugaban kungiyar ‘yan Nijeriya mazauna wajen kasar nan, (NIDCOM), Abike Dabiri, ya ce gwamnati ba za ta bayar da wani tallafi na kudi ba ga duk ‘yan Nijeriyan da suke da burin baro kasar ta Afrika ta kudu.
Da yake Magana da manema labarai a Abuja, bayan tattaunawarsa da shugaban kwamitin majalisar Dattawa a kan ‘yan Nijeriya mazauna kasashen waje da kuma kungiyoyin da ban a gwamnati ba, Sanata Surajudeen Ajibola Basiru, cewa ta yi duk wadanda aka dawo da su din za a sanya su a cikin shirin nan na gwamnatin tarayya na kyautata yanayi.
Dabiri-Erewa ta kuma bayar da tabbacin cewa, gwamnatin tarayya za ta ci gaba da matsa lamba na ganin gwamnatin ta kasar Afrika ta kudu ta biya ‘yan Nijeriya da su ka yi asarar kadarorin su diyya a hareharen na kwanan nan.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!