Connect with us

MAKALAR YAU

Ziyarar Masari Sansanin ’Yan Ta’ada Kallo Ya Koma Sama (1)

Published

on

Ta faru ta kare! Ya zuwa yanzu labari ya karade duniya cewa gwamna Masari ya ziyarci sansanin masu garkuwa da mutane domin neman kudin fasa da barayin shanu domin neman mafita a kan wannan al’amarin da yaki ci yaki cinyewa.
Sakamakon kazamcewar kai hareharen wuce gona da iri da ‘yan bindiga kai kaiwa jama’a ba dare ba rana, wannan tasa gwamnatin jihar Katsina karkashin gwamna Aminu Bello Masari ya yanke shawarar tattunawa da wadannan ‘yan ta’ada domin a samun zaman lafiya.
Wannan daukar matakin ya biyo bayan wani mummunar hari da ‘yan bindigar su ka kai a garin Wurma da ke karamar hukuma Kurfi, inda su ka yi awan gaba da mutane fiye da 50 da yawa daga cikinsu matan aure ne da ‘yan mata.
Sai dai kuma gwamna Aminu Bello ya shirya zuwa duk inda maboyar wadannan ‘yan ta’ada take domin tattaunawa da su tare da jin dalilinsu na kai wannan harehare, inda ya ziyarci Dajin Dan Kolo da ke karamar hukumar Sabuwa da kuma Dajin Kogo da ke karamar hukumar Faskari da kuma Dajin Dan Sabau da ke kankara. Garin farko da gwamna tare da rakiyar manyan jami’an tsaro da aka fara zuwa shi ne Dan Kolo wani gari ne wanda daga shi sai daji inda wadannan mutane su ke da zama, kuma nan ne idan sun dauke jama’a suke shiga da su kafin a kawo kudin fansa a karbe su.
Kamar yadda na fada wannan ziyara tana tattare da abubuwa da da yawan gaske, na farko akwai hasashe da zargezarge da ake yi wa wasu na kusa da gwamna cewa suna da hannu wajan aikata wannan ta’asa saboda haka ma lokacin da gwamna Masari ya ce shi da kansa zai je wajan wadannan mutane jama’a da dama musamman masu wancan zargi sun ji dadin haka.
Abinda suka ji shi ne, kila tunda gwamna da kansa zai je wajan, kuma wadanda suka yarda su ajiya makamansu kila su yi wata irin fallasa da zata tona asirin wadanda ake zargin suna rura wutar wannan rikici.
Allah daya gari banban, duk ba a ji haka ba, duk da cewa wasu sun sha ta dubu sun bayya wadanda suke taimakawa wannan ta’adanci musamnnan jami’an tsaro na Sojoji da kuma ‘yan sanda da masu rike da sarautun gargajiya kuma anyi wannan magana ne a gaban shugawanin tsaro na jihar Katsina da suka hada da kwamishinan ‘yan sanda da kuma shugaban sojoji da shugaban SSS da sarunasu.
Lawal Tsoho na daya daga cikin ‘yan sa kai na yanki Sabuwa wanda kuma yana da amince da manyan barayin shanu da mutane irin Dan karami da Maikomi da Dangote da da suke zaune a wannan daji. Wata majiya ta shaidamana cewa duk lokacin da za aje wajan wadannan ‘yan ta’ada idan har ba a sa Lawal Tsoho a gaba ba, yana da wahala a dawo lafiya, saboda yadda ya san su, kuma suna jin tsoransa.
Saboda shi kanshi ya bayyana cewa yana da kwararan hujjoji akan wadanda suke taimakwa masu garkuwa da jama’a don nemna kudin fansa, daga cikin wadanda ya ambata akwai ‘yan siyasa da ya ce idan gwamna yana bukata zai kama suna tare da bada hujja ta zahiri ciki harda maganganu da ya nada ta hanyar wayar salula.
Ya kara da cewa sojoji da aka tura wajan aikin babu abinda suke in banda hada baki da wasu mutane da ke wannan yanki ana cinyewa fulani dukiya, acewarsa me kawo a rika ba soja kyutar Saniya, shi da aka tura aikin kwantar da tarzoma domin tabbatar da zaman lafiya.
Lawal Tsoho ya kara da cewa hatta masu rike da sarautun gargajiya suna da sa hannu, a wannan barna sai gwamna ya dauki kwakwaran matakin kafin a samu zaman kafiya a wannan yanki, idan kuma aka sa ido haka ta cigaba da faruwa to Allah Ya sawake.
“ina da hujjujina wadanda zan bada ba wanda zan yi wa sharri ko kage, kafin in bayyana abu sai na yi bincike na gano gaskiyar lamari na ke fada, idan gwamna yana bukatar zan bayyana masa wadanda suke taimakawa masu garkuwa da mutane domin neman kudin fansa a wannan yankin na Sabuwa da Dandume.” Inji shi.
Wadannan kalamai na Lawal Tsoho sun canza tunanin jama’a musamman manyan shuwagabanin jami’an tsaro, wadanda kullin suke cewa mutanen su suna iyakar kokarinsu wajan ganin an samu zaman lafiya a wadannan yankuna sai gashi maganar ta sha banban da wanda Lawal Tsoho ya fada a gaban gwamna da sauran jami’an gwamnati da ‘yan jarida da mutanen garin Ko shakka babu, wannan ikirari ya sanya da yawan jama’a cewa idan aka cigaba da jin irin wadannan kalamai hakika za a iya samun bakin zaran warware wannan matsala cikin sauki.
A Dajin Kogo Na Faskira A wannan daji, anan aka yi maganganu wadanda ba ayi zato jin su ba daga bakin wadanda ke aikata wannan ta’asa, kamar yadda wani ya ce, “Na zo wajan nan, ko da kuwa ba zan koma gidana ba, na yi alkawarin sai na zo saboda na shiryawa duk abinda zai same ni” Abubuwan da suka banbanta haduwa da mutanen dajin Kogo da na Dan Kolo shi ne, manyan barayin da suka addabi yankin Sabuwa da Dandume ba su zo wajan taron ba, amma na dajin Kogo da ke Faskari manyan da kan su suka zo kuma aka ba su dama suka yi bayanin abinda ke ci masu tuwo a kwayar dangane da wannan matsala da kuma sasanshi da ake son yin tsakaninsu da jama’ar Hausawa da kuma gwamnati.
A dajin na Kogo a wani gari da ake kira unguwar Tsamiya gwamna Masari ya ce ana son a daina kai wadannan hare-hare a kowane bangare ba wai jihar Katsina kawai ba. Ya bayyana cewa tuni magana ta yi nisa akan tattaunawa tsakanisna da gwamna jihar Zamfara Muhammad Bello Matawalle, saboda haka ana kan hanyar laluba mafita game da wannan bala’I, in da ya ce so ake a cire abinda ke sa ana yin sata ayi maganin abun, sannnan duk wanda yaki amincewa da wannan maslaha, sai ayi masa taron dangi domin murkushe shi.
Daya daga cikin kwamandojin dajin Kogo, Alhaji Adamu ‘yan Kuza cewa ya yi sun dauki wannan mataki ne saboda wani mutun da ya halarta jininsu, inda suke ganin ana iya karar da su ba tare da sun farga ba. Ya ce ba zai ambata suna ba, amma anyi wani mutun a Zamfara da yake hawan munbari yana cewa jinin Bafullatani ya halasta a kashe, a yanka, asha jini, suna saurare kuma suna dubawa awayoyin salula ya ce wannan yana daga cikin abubuwan da suka ba su tsoro suka ce wanda baya da bindiga ya je ya sayo bindiga illa iyaka.
Alhaji Adamu ‘yan Kuza ya ce anyi abubuwa da dama, amma gwamnati taki daukar matakin da ya kamata, kuma ana hada kai da ‘yan uwansu Fulani wadanda suka koma cikin gari ana kamasu ana kashewa ana cinye musa dukiya ba gaira ba dalili Wannan kadan ne daga cikin irin abubuwan da aka ji wadanda ba ayi zaton ji ba daga bakin da baya karya, sai dai duk da haka akwai kalubale da jama’ar gari ke kallo akan wannan salhu, domin har gobe mutane suna cewa menene makomar wadanda aka yi wa barna ta asarar rayuka da dukiyoyi, su ba a ji gwamnati na kokarin yin magana da su ba.
Insha’Allahi sannu a hankali zan cigaba da kawo maku yadda ta kasance a wannan dazuzuka da muka kai wannan ziyara wajan manyan ‘yan ta’ada da ake son su ajiye makamansu su rungumi zaman lafiya. Sannan anan gaba zamu ji irin alfanun da wannan ziyara ta fara haifarwa.
Mu hadu sati mai zuwa idan Allah ya kaimu da rai da lafiya.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!