Connect with us

RIGAR 'YANCI

An Damfari Sanata Dan’Iya A Zamfara

Published

on

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Zamfara ta samu nasarar kama wani gawurtacen dan damfara mai suna Ibrahim Muhammad Mai Gandi, wanda ya damfari Dan Majalisar Dattawa mai wakiltar Zamfara ta Yamma, Sanata Lawali Hassan Dan’Iya.

Kakakin rundunar ‘yan sanda na Jihar Zamfara, SP. Shehu Muhammad, ne ya bayyana kamun dan damfara a hedikwatar ‘yan sanda da ke Gusau, babban birnin jihar Zamfara.

Kakakin rundunar ya bayyana cewa, “dubun Ibrahim Muhammad Mai Gandi da ke cikin karamar hukumar Zurmi ta cika ne a lokacin da ya yi amfani da sunan kwamishinan ‘yan sandan jihar, Usman Nagoggo, ya damfari Sanata Lawal Hassan Dan’Iya kudade kamar haka:

“Ibrahim Muhammad ya nemi sanata da ya ba shi barka da sallah a matsayinsa na kwamishinan ‘yan sandan jihar Zamfara Usman Nagoggo kuma ta hannun mai taimaka wa Sanata Dan’Iya (watau PA) ya turo ma sa Naira 200,000 a matsayin barka da sallah.

“Ganin ya samu nasarar amsar barka da sallah, sai kuma ya kira Sanata Dan’Iya ya ce ma sa akwai guraben ASP bakwai da gurbin sufeto tara, wadanda kowanne abinda sanata zai bayar shi ne Naira 200,000.

“Nan take sanata ya umarci mai taimaka ma sa da ya tura wa Ibrahim Kwamishina ‘Yan Sanda Naira miliyan daya da dubu dari shida, domin samun guraben da zai raba wa al’ummar mazabarsa.”

Dubun dan damfaran ya cika ne a lokacin bikin cika kwana dari a Gusau na gwamnatin jihar, inda Sanata Dan’Iya ya gaisa da kwamishinan kuma ya gabatar da kansa, amma ya ji bai yi ma sa wata magana ba a kan abubuwan da su ka faru a baya .

A nan ne Sanata ya shiga wasu-wasi, inda ya bayyana wa kwamishinan ‘yan sanda abinda ya faru. Daga nan ne kwamishinan ya amshi wayar dan damfarar kuma yanzu haka ya fada hannun rundunar ‘yan sandan.

Kakakin rundunar ‘yan sandan ya ce, sun kama dan damfarar ne a mota kirar Marsandi, inda a binkicensu sun tabbatar da cewa ita ma motar ta sata ce.

Ibrahim Muhammad ya bayyana wa ‘yan jarida cewa, ya aikata wannan laifi na damfara ne, saboda matsalar ruyuwa da ya shiga, amma kuma batun mota tashi ce, ba ta sata ba ce, domin da kudinsa ya saya Naira miliyan daya da dubu dari hudu.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: