Connect with us

WASANNI

An Fitar Da Sunayen ’Yan Wasa 10 Da Babu Kamarsu A FIFA

Published

on

Hukumar kwallon kafa ta Fifa, ta fitar da matsayin fitattun ‘yan wasan kwallon kafar wasan kwamfuta na Fifa na shekarar 2020 wato Fifa 20 wanda hukumar takeyi duk shekarar wasa kuma  a irin wannan watan.

Akan fito da wasan kwallon kwamfuta na Fifa duk shekara ne, inda ake bai wa kowanne dan wasa sabon matsayi gwargwadon kokarinsa a gasar shekarar da ta gabata ciki har kokarin da dan wasa zai yi a kasarsa ta haihuwa.

Fifa 20, wadda ake fitarwa a kowace ranar 24 ga watan Satumba, za ta nuna taurarin ‘yan wasa irinsu Eden Hazard da kuma Virgil Van Dijk na Livepool a matsayin fuskar wasannin na Fifa 20  sai dai ba su shiga jerin ‘yan wasan da suka fi yawan maki ba a sabon jerin sunayen ‘yan wasan da aka fitar.

A madadin haka, Lionel Messi shi ne kan gaba cikin wadanda suka fi kowa, inda ya doke tsohon abokin hamayyarsa Cristiano Ronaldo sannan Messi na kan gaba da maki 94, shi kuma Ronaldo na da maki 93.

Sai kuma fitaccen dan wasa wanda tauraronsa ke haskawa wato Neymar na PSG na biye da su da maki 92, sai Hazard da kuma abokin wasansa a tawagar kasar Belgium wato Kebin De Bruyne a matsayi na hudu dana biyar.

Bayan wasu ‘yan wasanni da mai tsaron ragar Manchester United David De Gea ya yi, inda bai tabuka abin a zo-a-gani ba, yanzu ba shi ne golan da ya fi kowa iya kama kwallo ba amma yanzu Jan Oblak na Atletico Madrid ne ke kan gaba.

Sai dai babu sunayen fitattun ‘yan wasa irinsu Harry Kane na Tottenham da Sergio Aguero na Man city da kuma Kylian Mbappe na PSG, wadanda ba sa cikin sunaye goman farko a jerin fitattun, inda kowannensu ke da maki 89.

Ga jerin Fitattun ‘yan wasa 10 na Fifa 20:

1) Lionel Messi: 94

2) Crisiano Ronaldo: 93

3) Neymar: 92

4) Eden Hazard: 91

5) Kevin de Bruyne: 91

6) Jan Oblak: 91

7) Virgil Van Dijk: 90

8) Mohamed Salah: 90

9) Luka Modric: 90

10) Marc-Andre ter Stegen: 90
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: