Connect with us

RAHOTANNI

Gwamnatin Bauchi Da UNICEF Sun Yunkuro Don Shawo Kan Matsalar Tamowa

Published

on

Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad Abdulkadir, ya amince da maida wa hukumar kula da yara ta UNICEF a jihar Bauchi Naira miliyan 15 a bisa gaza aiwatar da aiyukan hadaka da kudaden da tsohowar gwamnatin jihar ta gaza yi.

Amincewar ya biyo bayan wani ganawa ta musamman da jami’an UNICEF a karkashin jagorancin babban jami’in hukumar a jihar, Bhaw Pathak tare da gwamnan a gidan gwamnatin jihar, kamar yadda sanarwar da babban mai taimaka wa gwamnan jihar kan yada labarai Muktar Mohammed Gidado ya fitar.

Gwamna Bala Muhammad wanda yake maida bahasi dangane da bukatar da UNICEF ta yi wa gwamnatin jihar na ta maido mata da tsabar kudin har naira miliyan 15 da suka yi hadaka da gwamnatin jihar a karkashin hukumar lafiya a matakin farko ba tare da yin amfani da kudaden ba a lokacin gwamnatin da ta shude.

Gwamna Bala ya nuna takaicinsa ta yadda tsohowar gwamnatin jihar ta hallaka naira miliyan 732 ba tare da yin amfani da su yadda ya kamata ba, yana mai shaida cewar kwamitin kwato kadarori da dukiyar jama’an jihar za su tabbatar da kwato dukiyar daga hannun wadanda suka wawushe.

Bala ya bai wa UNICEF tabbacin cewar gwamnatinsa za ta tabbatar da sake kudaden hadaka a kan lokaci domin jihar ta samu cin gajiyar ayyukan hukumomin bayar da agaji daban-daban don kyautata jihar.

Dangane da batu kan cutar nan ta Tamowa wanda a ke samunta a sakamakon karancin abinci mai gina jiki a jikin yara kanana, Gwamna Bala Muhammad, ya tabbatar wa UNICEF cewar zai tabbatar da bayar da kudaden hadaka domin samar wa yaran da su ke fama da cutar ta tamowa mafita a jihar.

Ya sanar da UNICEF cewar tunin gwamnatinsa ta sanya dokar ta baci a kan harkokin lafiya domin tabbatar da kawo karshen matsalolin da suke fuskantar harkar lafiya a ciki da wajen jihar don tabbatar da ci gaba mai ma’ana a jihar.

Tun da fari, babban jami’in UNICEF a jihar, Bhaw Pathak, ya shaida wa gwamnan cewar ita UNICEF a shirye take wajen taimaka ta fuskacin aiwatar da shirye-shirye guda biyar da su ka hada da lafiya, ilimi, tsaftar ruwa da ta muhalli (WASH), abinci mai gina jiki da kuma kare yare.

Ya shaida cewar tunin UNICEF ta ware naira miliyan 270 domin shawo kan matsalolin cutar Tamowa (karancin abinci mai gina jikin yara) a jihar, ya na mai bukatar gwamnan jihar da ya tabbatar da kara tasa azamar wajen shawo kan matsalolin karancin abinci mai gina jiki a fadin jihar.

Mr Bhaw Pathak ya ce za su taimaka wa jihar wajen shawo kan matsalolin da suke akwai musamman wajen tabbatar da shawo kan matsalolin yara da ba su zuwa makaranta a jihar.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: