Connect with us

RIGAR 'YANCI

Gwamnatin Katsina Ta Nanata Kudirin Karfafa Hanyoyin Samar Da Aiki

Published

on

Gwamnatin jihar Katsina ta kara nanata kudurinta na marawa bangarorin samar da aikin yi, wadanda ba na gwamnati ba, don karfafa masu gwiwa tare da dorewarsu. Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ya bada tabbacin a lokacin kaddamar da kashi na biyu na kwasakwasan diploma a kan dabarun koyarwa da kuma ilimin adana litattafai wadda makarantar Engr. Muttaka Rabe Darma ke gudanarwa.

Gwamnan ya yabawa kokarin mahukuntan cibiyar na sanya mata da yawa a cikin shirin. Ya bayyana cewa samarwa mata aikinyi zai basu damar tallafawa mazajensu tare da dawainiyar yaransu. Gwamna Masari don haka sai ya bukaci mahukuntan cibiyar dasu rubutowa gwamnati rokon a sama masu fili don fadada cibiyar.

Ya lura da cewa cibiyar bazata iya daukar adadin daliban dake neman shiga makarantar ba. Gwamnan ya karfafa bukatar dake da akwai na samar da ilimi ingantacce.  Ya kuma nemi cibiyar da ta hada hannu da makarantar ilimi domin yin amfani da manhajarsu.

Gwamna Aminu Bello Masari ya yabawa kokarin Engr. Muttaka Rabe Darmana sauya harsashi mai inganci wanda zai sanya alfahari a cikin al’umma. A nashi tsokacin shugaban cibiyar kuma wanda ya assasa ta Engr. Muttaka Rabe Darma ya yaba wa kokarin Gwamna Masari na bawa bangaren ilimi fifiko. Engr. Muttaka Rabe Darma ya lura da cewa Gwamnatin jiha na kashe kimanin sama da kashi sha hudu (14) cikin dari na abinda take samu a wata wanda ya kai Naira Miliyan dari (100) a kan albashin malaman makaranta.

Sai ya bukaci malaman da su maida hakali su zage damtse wajen gudanar da aikinsu yadda ya kamata.

Coordinator na makarantar Dr. Mustapha Alkasim yace kimanin malaman Primary da Secondary tamanin ne (80) suka kammala karatun Diploma a makarantar. Sai ya yabawa gwamnatin jihar Katsina ganin dorewar shirin.

Haka nan kuma, gwamnatin jihar Katsina ta nemi goyon baya da hadin hakn sarakuna iyayen kasa da masu ruwa da tsaki domin samun nasarar gudanar da shirin bunkasa samar da ilimi don al’umma su amfana wato BESDA a nan jiha.

Babbar sakatariya a ma’aikatar ilimi Hajiya Halima Lawal Usman tayi wannan rokon lokacin da ta jagoranci jami’ai daga hukumar ilimin bai daya ta kasa da na jiha a wata ziyarar ban girma ga fadar mai Martaba Sarkin Katsina.

Kamar yadda tace shirin na bunkasa samar da ilimi don al’umma su amfana an bullo da shirin ne don magance matsalar yaran da basu zuwa makaranta. Ta bayyana cewa shirin na BESDA ayyukan tallafi ne na bankin duniya inda jiha na cikin jihohin da za su ci gajiyar shirin.

A nashi jawabin shugaban gudanarwar hukumar ilimin bai daya ta kasa na shiyyar Arewa ta yamma Sanata Abubakar Sadik Yar’adua yace shirin na BESDA na son mayar da yara fiye da miliyan daya da basa zuwa makaranta.

Sanata Sadik Yar’adua ya yaba wa gwamnatin jihar Katsina game da farfado da bangaren ilimi. Mai Martaba Sarkin Katsina Alh. Dr. Abdulmumini Kabir Usman ya bada wadansu hanyoyi da za a bi domin bunkasa bangaren ilimi.

Mai martaban ya bada tabbacin goyon bayan majalisarsa don samun nasarar aiwatar da shirin na BESDA a nan jihar.  Ya ba iyaye kwarin guiwar sanya yayansu makaranta da kuma yan mata.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!