Connect with us

RIGAR 'YANCI

Gwamnatin PDP A Bauchi Ta Gaza Cika Alkawura A Kwana 100 – APC

Published

on

Jam’iyar adawa ta APC a jihar Bauchi, ta shaida cewar jam’iyyar PDP da ke mulki a jihar, ta gaza wajen cika alkawuran da ta dauka wa jama’an jihar a farkon kwana 100 da ta yi a kan mulkin jihar.

Jam’iyyar ta zargi PDP da gwamnanta Bala Muhammad Abdulkadir da cewar ba za su iya gudanar da kyakkyawar shugabanci a jihar Bauchi ba, sun yi zargin cewar an fara shigo da karerayi tun da kwanaki 100 na farkon gwamnatin jihar.

A cikin wata kwafin sanarwar manema labaru da jami’in watsa labarai na APC a jihar Bauchi, Adamu Aliyu Jallah ya fitar, APC ta zargi gwamnatin Bala da gazawa da kasa daukar mikatin iya cika alkawuran da suka dauka wa jama’an jihar a cikin kwanaki 100 da shigarsa ofis. APC ta zargi gwamna Bala da cewar a lokacin yakin neman zabensa yayi alkawarin zai biya kudin hutu na shekara-shekara ga ma’aikatan jihar, zai kuma biya dukkanin bashin giratuti da tsoffin ma’aikata ke bi, kana zai kuma gudanar da zaben kananan hukumomi, ‘Amma duka ya gaza yi,’ in ji APC.

Jam’iyyar ta zargi gwamna mai ci da gaza samar da wadattun magunguna a cikin asibitocin jihar, gaza iya biyan albashin ma’aikata kafin sallah, kasa bunkasa harkar ilimi da ta lafiya, gaza samar wa jama’an jihar wadattun ruwan amfanin da kullum.

APC ta kuma zargi gwamnan da cewa ya bayar da wasu Kwangiloli shinfida tituna ba tare da an shigar da aiyukan a cikin kasafin kudi na 2019 ba, APC din ta bayar da misali da ayyukan shinfida tituna a Azare, Burra, Akuyam, wadanda ma ta ce kashi 50 cikin dari na kudaden kwantiragi da Gwamnan ya ke ce ya biya hakan ya zarce kason da a ka shigar cikin kasafin kudi na shekaran don haka ne jam’iyyar ta nuna gayar mamakinta kan hakan.

“Abun da kawai gwamnatin PDP ta iya yi shine surutai amma ta gaza gudanar da kyakyawan aiyuka a jihar. “Kodayake, al’umman jihar Bauchi su ne za su yanke hukunci. A lokaci guda, mu na kira ga al’umma da su kara yi wa jiharmu addu’a domin Bauchi ta samu kubuta daga halin da ta tsinci kanta a ciki,” in ji sanarwar.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: