Connect with us

WASANNI

Har Yanzu Akwai Sauran Aiki A Gaban Super Eagles – Gernot Rohr

Published

on

Tawagar kwallon kafa ta Ukraine da ta Super Eagles sun tashi wasan sada zumunta 2-2 a fafatawar da su ka yi ranar Talata kuma Super Eagles wadda ta bakunci Ukraine ce ta fara cin kwalo ta hannun Joe Aribo minti hudu da fara wasa, sannan ta kara ta biyu a bugun fenariti da Victor Osimhen ya buga.

Haka kuma aka je hutu Najeriya da kwallo biyu a raga, ita kuwa mai masaukin baki Ukraine na nema sai dai bayan da suka koma zagaye na biyu ne mai masaukin baki ta zare kwallo daya ta hannun Oleksandr Zinchenko, kuma saura minti 10 a tashi daga karawar ta kara zare ta biyu ta hannun Roman Yaremchuk.

Kasashen biyu sun buga wasan sada zumuntar ne, bayan da Ukraine ke hutun buga wasannin neman shiga gasar Turai ta 2020 ita kuwa Najeria ba ta buga karawar neman shiga gasar cin kofin duniya da za a yi a Katar ba, bayan hutu da ta yi a lokacin da hukumar kwallon kafa ta duniya ta ware.

Sai dai kyaftin din Super Eagles, Ahmed Musa bai buga karawar ba, sakamakon jinya da yake yi amma kuma wannan ne karon farko da Super Eagles ta yi wasa tun bayan mataki na uku da ta yi a gasar cin kofin nahiyar Afirka da aka yi a Masar tsakanin watan Juni zuwa Yuli.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!