Connect with us

WASANNI

Luca Jovic Na Madrid Ya Sake Jin Ciwo

Published

on

Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid na gaba, Luca Jovic, ya sake jin sabon ciwo a wasan da ya wakilci kasarsa ta haihuwa, Serbia, da su ka fafata da kasar Crotia a wasan neman cancantar shiga gasar cin kofin nahiyar turai.

Dan wasan dai har yanzu wasanni uku kacal ya bugawa kungiyar ta Real Madrid bayan da aka fara kakar wasa shi kuma yana jiyya sai dai har yanzu bai fara burge kociyan kungiyar ba da kuma magoya baya. Wata sanarwa daga hukumar kwallon kafar kasar ta fitar ta bayyana cewa dan wasan yaji ciwo ne a kafarsa ta dama sai dai a cewar sanarwar daman tun farko yana da ciwon kuma bai gama warkewa ba hakan yasa bai buga wasan da kasar ta buga ba a jiya.

Kociyan kasar Serbia dai yafara buga wasansa da suka fafata da kasar Portugal ne da dan wasan gaba na Fulham, Aleksandar Mitrobc saboda ciwon na Jovic duk da cewa daga baya ya shiga wasan kuma ya zura kwallo a raga a wasan da sukayi rashin nasara daci 4-2 a hannun kasar Crotia.

Hakan ya sa a wasan da suka fafata ma a jiya Mitrobic ne ya fara wasan a wasan da su ka fafata da kasar Ludembourg kuma har yanzu maki daya suke da kasar ta Serbia inda suke mataki na biyu dana uku.

Ciwon da Jovic ya ji kari ne a kan ciwon da ‘yan wasan kungiyar su ke fama dashi bayan da a halin yanzu ‘yan wasa irinsu Edin Hazard da Isco da Marco Asensio da James Rodriguez da Brahimi Diaz duka su na jinya.

A ranar Asabar kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid zata karbi bakuncin kungiyar kwallon kafa ta Levente a wasa na uku na hudu na gasar laliga bayan da har yanzu Zidane bai samu nasara ba a gida tun lokacin da aka fara gasar.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!