Connect with us

MANYAN LABARAI

Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin Ta Kalubalanci Amurka Da Ta Dakatar Da Matsawa Wasu Kamfanonin Sin Lamba

Published

on

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta bayyana a yayin taron manema labaru da aka shirya a yau Talata, cewa a cikin ‘yan kwanakin da suka wuce, gwamnatin Amurka ta mayar kamfanin Huawei na kasar Sin na’urorin sadarwar da ta kwace shekaru biyu da suka wuce, matakin da Amurka ta dauka a hakika ya nuna cewa, ta amince da aikin da ta yi na sabawa dokoki. Kasar Sin ta kalubalanci kasar Amurka da ta dakatar da matsawa wasu kamfanoninta lamba.

Ban da wannan kuma, Hua Chunying ta nuna cewa, ya kamata kasar Amurka ta saurari ra’ayoyin da bangarori daban daban na kasarta ke fada, da kuma daina fakewa da batun kiyaye tsaro tana matsawa wasu kamfanonin kasar Sin, kana da samar wa kamfanonin Sin yanayin cinikayya da ya dace a Amurka. (Bilkisu) Ma’aikatar kula da tsaron jama’a ta kasar Sin, ta bayyana cewa, daga ranar 20 ga watan Satumban wannan shekara, za a saukakawa matafiya ‘yan kasashen waje matakan neman lasisin tuki na wucin gadi da suke nema a kasar, inda za a rika ba su na dogon wa’adi.

Bugu da kari kuma, Liu Yupeng babban jami’i a ma’aikatar ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai, yana mai cewa, duk matafiyin da ya gabatar da takardar neman lasisin tuka mota ko babur na wucin gadi, ba sai ya gabatar da takardar bayanin koshin lafiya ba.

Muhimman takardun da ake bukata, sun hada da fasfo, lasisin tuka mota na Kasar da mutum ya fito sannan a fassara su cikin harshen Sinanci. Liu ya ce, daga yanzu wa’adin lasisin zai kasance na abin da bai gaza watanni uku ba, za kuma a iya kara wa’adin zuwa shekara guda, idan har mai lasisin zai zauna a kasar Sin na sama da watanni uku.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!