Connect with us

JAKAR MAGORI

Mutum 11 Sun Mutu, Hudu Sun Jikkata A Hatsarin Mota A Nasarawa

Published

on

A ranar Litinin ce, hukumar kiyaye hadararruka ta Jihar Nasarawa, ta bayyana cewa, an samu mummunar hatsarin mota a babban hanyar Akwanga zuwa Lafiya, wanda ya rutsa da motoci guda uku, inda hatsarin ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 11, yayin da mutum hudu su ka samu mummunan raunika. Kwamandar sashe na hukumar, Mista Ismaila Maiwada-kugu shi ya bayyana wa kamfanin dillancin labarai hakan ranar Litinin a garin Lafiya. Maiwada-Kugu ya kara da cewa, hatsarin ya faru ne a wani wuri wanda a ke kira da suna ‘Many Habe Gone’ da ke kauyen Wowyen cikin karamar hukumar Akwanga ta jihar da misalin karfe 10.25 na safiyar Litinin.
“Hatsarin ya rutsa da motoci guda uku da kuma mutane guda 15. Mutum 11 sun mutu, yayin da mutum hudu su ka jikkata. Motocin dai sun hada da wata mota kirar Boder da kairar Sharon da babur da kuma tirela,” in ji shi.
Maiwada-Kugu ya cigaba da cewa, jami’an hukumar kiyaye hadararruka sun isa wurin da lamarin ya afku, inda su ka kwashe gawarwaki da kuma wadanda su ka samu raunika zuwa asibiti na kusa da wurin. “Jami’anmu sun isa wurin da lamarin ya faru cikin gaggaea, inda su ka agaza wa wadanda lamarin ya rutsa da su. A bayanin da na samu, tirela ce ta murkushe wata mota wacce ta ke tafiya a kan wannan babban hanyar.”
Maiwada-Kugu ya shawarci direbobi da su dunga kulawa duk lokacin da su ke gudu ko kuma lokacin da su ka zo wuce motar da ke gabansu, domin kaucewa faruwar irin wannan mummunan hatsari
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!