Connect with us

WASANNI

Na Kusa Sayen Messi A Arsenal – Arsene Weger

Published

on

Tsohon kociyan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Arsene Wenger, ya bayyana cewa lokacin da yana koyar da kungiyar ta Arsenal ya so sayan dan wasan Barcelona, Leonel Messi a lokacin da dan wasan yana da shekara 16 a duniya.

Messi dai shine dan wasan da babu kamarsa a kungiyar ta Barcelona inda ya kasance shine jagoran kungiyar kusan shekaru goma da suka gabata kuma ya lashe kofuna da dama da kungiyar sannan ya zura kwallaye 603 cikin wasanni 687 daya buga a duniya.

Wenger ya bayyanawa wata jarida a kasar Faransa cewa lokacin da Messi yana matashi har ya tuntubi Barcelona akan ko zasu sayar masa da dan wasan sai daga baya shugaban kungiyar na wancan lokaci ya ce baza su sayar da dan wasan ba.

“Munyi Magana da Messi a lokacin da muka sayi Cesc Fabregas daga Barcelona saboda  a lokacin tare suke buga wasa suna matasa shine mukaga yakamata mu hada su waje daya amma sai Barcelona suka ce baza su bamu mutum biyu ba” in ji Wenger

Wenger ya cigaba da cewa “A lokacin akwai matasan ‘yan wasa masu jini a jiki wadanda kuma zasu taimakawa kungiyar musamman idan suka girma irinsu Gerard Pikue da Messi da kuma Fabregas sai dai Pique da Fabregas sunzo Ingila Messi kuma yayi zamansa”

Wasu rahotanni a kwana kwanan nan dai suna cewa kungiyar kwallon kafa ta Barcelona tana shirin karawa Messi sabon kwantiragi wanda zaisa ya cigaba da zaman kungiyar har lokacin da zai daina kwallo a duniya duk da cewa akwai kuma wani rahoto da yake bayyana cewa dan wasan ya fara tunanin komawa kasar Amurka da cigaba da buga wasa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!