Connect with us

KASUWANCI

Osinbajo Zai Kaddamar Da Sabon Tsarin Kiwon Dabbobi

Published

on

A jiya ne Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ya kaddamar da Sabon Tsarin Kiwon Dabbobi a Jihar Adamawa. Shirin mai suna ‘National Libestock Transformation Plan (NLTP), za a kaddamar da shi ne domin samar da mafita daga matsalolin rikice-rikice da kashe-kashen da ke faruwa tsakanin makiyaya da manoma a yankin.

Shiri ne na gwamnatin tarayya da zai fara daga mataki na farko, daga 2019 zuwa 2028, tare da hadin guiwar jihohi a karkashin inuwar Hukumar Inganta Tattalin Arziki. Ana son fara shirin ne domin ingantawa da habaka fannin kiwo ta yadda zai rika samar da kudaden shiga, ta hanyar fara shi a jihohi bakwai da suka hada da: Adamawa, Benue, Kaduna, Filato, Nasarawa, Taraba da Zamfara.

Sai dai kuma idan ba a manta ba, an samu rashin fahimta a lokacin da aka yi kokarin kafa shirin RUGA, inda Mataimakin Shugaban Kasa, Osinbajo ya nesanta ofishinsa daga hakkin kula da shirin. Sannan kuma Osinbajo ya ce RUGA da NLTP daban su ke, kowanne zaman kan sa ya ke yi.

Kwanaki kadan bayan bayanin da Osinbajo ya yi ne kuma sai Buhari ya dakatar da shirin RUGA, shirin da ya yi ta fama da shan suka da takaddama a wasu sassa na Ksar nan. Kaddamar da wannan shiri da ake kan yi a Adamawa zai kawo jihar a matsayin ta farkon fara amfani da wannan shiri, domin kawo karshen fadace-fadacen makiyaya da manoma da kuma wanzar da zaman lafiya a tsakaninsu.

Sannan kuma akwai manufa ta samun kudaden shiga da inganta harkar kiwo domin samar da sabbin dabarun yalwata yawan dabbobi, killace su, samar da masana’antun sarrafa madara da kuma naman shanu.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: