Connect with us

RIGAR 'YANCI

Shekaru Hudu Gwamnatin Kebbi Ba Ta Biya Ni Garatutina Ba, Cewar Tsohon Malamin Makaranta

Published

on

Wani tsohon malamin Sakandare Mai suna Malam Muhammed Magaji Gulma (The Kyu) wanda ya kwashe shekaru hudu da ajiye aiki ya koka bisa ga rashin biyansa hakkinsa. Ya yi wannan koken ne jiya a garin Argungu yayin da ya ke zantawa da wakilinmu.

Malam Muhammed Magaji ya ce shi tsohon malamin Sakandare ne wanda ya ajiye aiki a makarantar gwamnati ta arabiyya da ke garin Argungu a karkashin ma’aikatar ilmi a bangaren Arabic board wanda kuma ya bayyana cewa tsawon aikin gwamnati da ya yi na shekaru talatin da biyar duk ya yi shi ne yana koyarwa.

Malam Muhammed Magaji ya bayyana wannan a matsayin rashin Imani wajen shugabanni saboda idan mutum zai bata shekarunsa yana yi wa gwamnati hidima da zummar idan ya ajiye aiki zai sami madogara amma daga karshe kuma sai abin ya gagara, wannan ba adalci ba ne.

Kuma a bisa tsari na gaskiya a duk lokacinda mutum ya ajiye aiki ykna tsammanin a biya shi ba tare da Bata lokaci ba amma sai ga shi yanzu abin ya canza.

Malam Muhammed Magaji wanda malami ne da ya yi koyarda harshen turanci ya kara da cewa bayan ya ajiye aiki sai da ya yi shige da fice sannan sannan aka soma ba shi fansho amma fitowar garatuti ya faskara.

Daga karshe kuma ya yi kira ga wadanda ke da alhakin al’umma a kan su day su gaggauta biyansu hakkokansu su kaucewa danasani saboda su sani fa mulki kowa yana da wa’adi.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!