Connect with us

KASUWANCI

Tallafin Bashin Naira Biliyan 614: Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Cire Kudadenta Daga Jihohi Cikin Watan Satumbar 2019

Published

on

Ministar kudi, Zainab Ahmed, ta ce, Gwamnatin Tarayya za ta fara cire kudadenta naira biliyan 614 da ta tallafa wa gwamnatotcin Jihohi da bashi a wannan watan da muke ciki, cire kudaden zai zama an yi shi ne kai tsaye daga asusun ko wace Jiha ko wane wata daga asusun kwamitin kasafi na gwamnatin tarayya (FAAC) na ciyarwa- ministar kudin ta kara da cewa, dawo da kudaden zai zama an aika da su ne babban Najeriya CBN, Gwamnatin Tarayya za ta fara dawo da naira biliyan 614 na tallafi da ta ba wa Gwamnatocin Jihohi a wannan watan da muke ciki na Satumba.

A nata bangaren cewa ta yi kundin rahoton Jaridar The Nation ya fitar. Jaridar ta ruwaito cewa, Ministar kudin ta bayyana haka a yayin da take gabatar da matsakacin daftari na dabarun yadda za a kashe kudaden shekarar 2020 zuwa 2022 ranar Talata 10 ga watan Satumba. Ministar kudi, Zainab Ahmed, ta bayyana cewa wadan nan kudade da za a karba daga Gwamnatotcin Jihohi a ko wane wata, za a cire su ne daga asusun Gwamnatin Tarayya na ko wace Jiha kai tsaye a mayar da su izuwa asusun kwamitin babban bankin Najeriya (FAAC) na ciyarwa.

Ahmed ta kara cewa, mayar da kudin zuwa babban Najeriya zai fara tun da FAAC na ciyarwa mai zuwa, nan da makonni biyu masu zuwa.  “ Kai tsaye za mu cire a matakin farko mu tura zuwa babban bankin Najeriya CBN,” Ministar kudin ta nanata cewa,.

“ Kudaden da aka turawa Jihohi naira biliyan 614 ba wai an tura musu ne a matsayin wani bangare na kudaden shiga ba, an bayar da su ne akan bashi don kasafi, bashi ne da babban bankin Najeriya ya riga basu, kuma biyan zai kasance izuwa ga babban bankin,” a cewarta.

Ta sake tunasar wa inda ta ce, gwamnatin tarayya ta ce, gwamnatin tarayya tana da kwamiti da ta samar don aikin karbar wadan nan kudade na bashi da ta raba wa Jihohi 35 tun cikin watan Agusta.

Wadan nan Jihohi sun karbi kudin tsakanin shekarar 2015 zuwa 2017 yayin da suke fuskantar matsalar rashin kudi saboda halin rikice-rikice, da janyo ba za su iya biyan albashin ma’aikatansu ba.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!