Connect with us

Uncategorized

Tsakanin Sarkin Kano Sanusi I, Mamman Shata Da Danmani Caji

Published

on

A zamaninsa, Sarkin Kano murabus Sir Muhammadu Sanusi I, ya taba hana karuwai su wala a kasarsa, musamman ma a Kano, birni mafi girma a arewacin Nijeriya. Ya ce kowace mace ta je ta yi aure. Sir Sanusi babban malami ne.

Sai ‘yan doka na hukumar En’e su ka shiga kamen karuwai, ana yi masu tara. Su kuma su ka dinga gudu ko boyewa ko fakewa da wasu sana’o’in, kamar tuwotuwo da saida shinkafa. Wasu, maneman su su ka rika ba su mafaka a boye. A na kiran wannan al’amarin da “korar karuwai a Kano”.

Saboda yadda karuwai ke gudun buya, sun ki barin garin ko sana’ar, sai Alhaji Mamman Shata ya yi wakar nan ta “Na Ga Jahilci Wurin Karuwai” inda ya ke cewa a na korar mutum kamar kare shi ko ya like
kamar angulai. To, sai Malam Danmani Caji Bauchi, wanda ya na daga cikin manyan mawakan kasar Hausa a lokacin, ya yi wa Shata martani da wakar nan mai amshin “Haka Ne Malam Na Maude” inda ya ce, shi bai ga laifin karuwai ba, a’a, laifin masu neman su ya kamata a gani. Akwai inda ya ce:

“Yau mutum da abin sayarwa,

Ya kasa bai san wani mai saye ba,

Gobe ya kasa ya kwashe,

Bai san wani mai saye ba,

Jibi ya kasa ya kwashe,

Bai san wani mai saye ba,

Gata ya kasa ya kwashe,

Ya kwan bai sam saye ba,

Labudda barin garin ya ka yi!”

Manufarsa ita ce duk abin mutum zai sayar, ciki har da abin da karuwai ke sayarwa, idan babu mai saye to tilas ya sake wuri ko kuma ya bar sana’ar kwata kwata.

A wakar, ya ambaci Shata baro-baro, ya nuna cewa dora laifin karuwanci da Shata ya yi kan matan ba daidai ba ne; laifin mazan ne. A zamanin, ba mawakin da ka iya kalubalantar Shata, don haka sai a ka ga lallai Malam Danmani ya yi bajinta. Kuma ba wannan ba ne karo na farko da Shata da Danmani su ka gwabza.

A shekarar farko ta mulkin Sir Sanusi ma sun kara a wani babban bikin aure na ‘ya’yan sarki su 12, taron da a ke kira da Bikin ‘Yan Sarki. A bikin, Shata ya yi manyan makada zarra, ciki har da Danmani Caji, Ibrahim Dabalo, Hamza Caji, Inu Caji, da sauran su. Daga bikin ne ma yawanci su ka fara sanin Shata a Kano.

Kowane mawaki so ya ke ga wallen Shata tun daga lokacin, amma a na shakkar tabo shi, sai ka ce wani dodo! Sai ga dama ta samu, Danmani ya tabo shi. Shi kuma Shata sai ya ga kamar an takale shi ne. Sai su ka shiga zaman doya da manja shi da Caji. A na wannan zaman sai a ka hadu a bikin auren fari na Alhaji Babangida, dan wani babban attajiri a Jos mai suna Alhaji Sa’adu (aminin Alhaji Ibrahim Nashe ne, mahaifin yallabai Injiniya Abdullahi Ibrahim Nashe).

A wurin bikin auren, manyan makada sun hallara, ciki har da Shata da Danmani Caji. To sai ‘yan birni su ka ce su na so a yau dai a raba gardamar nan ta Shata da Danmani kan wa ke da laifin karuwanci tsakanin matan bariki da mazan da ke neman su.

A ka ce Shata ya rera wakar nan tasa ta “Na Ga Jahilci Wurin Karuwai”, sannan Danmani zai zo ya yi tasa ta martani. Sai Shata ya ce a’a, sai dai Danmani ya fara, Allah basshi shi sai ya zo da tasa. Tilas a ka yarda da hakan. Ba a san dabarar Shata ba!

Danmani ya zo tsakar fage ya rera wakarsa. A ka yi tafi a ka yi ma sa liki, ya ja baya. Da Shata ya shigo fage, duk an bude hakora a ji wakar nan da ya yi. Shi kuwa gogan naka da ya kalli ‘yan amshi da makadansa, sai ya ba su sabon amshi, ya ce, “Don Sallah Da Salatil Fatih Don Allah Mata Ku Yi Aure”. Sai wuri ya kaure da sowa da ife-ife da tafi.

Shata ya shiga waka fa, ya na cewa, “Tun daga Lawwali har ga Risala, Hak Kur’ani babban kundi, Ina ayar da ta kankare aure?” A wakar, ya nuna cewa auren dole na jawo shiga karuwanci ga ‘ya’ya mata. Saboda zakin muryar Shata da fikirarsa da salon wasansa (wato showmanship), nan take ya c gari.

‘Yan birni su ka ce lallai hujjojin Shata sun fi na Danmani karfi. Haka kuma su ka ce, “Kai Malam Danmani daga yau ka bar takalar Shata!” Da a ka watse daga wannan biki sai magana ta dinga yaduwa cewa Shata ya doke Danmani a waka.

Hakan bai yi wa Danmani da yaran sa dadi ba; su ka dinga jin haushi. Bayan wani lokaci, Shata ya je Kaduna, Danmani ma ya je. Sai yaran su su ka yi arba da juna a wani gidan mata mallakar Hajiya Hauwa Maikoko da ke Titin Bachama a Tudun Wada (gidan na nan kusa da makarbartar Chanchangi, dama da hanya in ka kalli gabas).

A nan, sai yaran Danmani su ka shiga takalar na Shata, wato su Lalo (wanda daga baya ya zama mawaki mai cin gashin kansa, har na sha ganin shi ya na wasa a kauyenmu). Abin kamar za a dambace, amma a ka raba su. An ce da Danmani ya ga abin da ke faruwa, ya goyi bayan yaransa. Da labari ya kai kunnen Shata, sai bai ji dadi ba.
Mafari kenan Shata ya yi wa Danmani Caji zambo a dai wannan waka ta “Don Sallah Da Salatil Fatih…”

A ta farkon, babu zambo, amma sai ya dinga maimaita ta a wurare daban-daban, ya na ragargazar Danmani. A wata, ya na kiran sa da “kadon Bauchi”, wanda kabilanci ne da Fulani kan yi wa Hausawa. Sannan ya kira shi da “dugunzuma”, kuma ya ce, “Sai a littafin Malam Danmani, ya ja baki ya kai wata aya, sai na ji ya ce ‘Kak kui aure!’” duk da ya ke a zahiri Danmani bai ce hakan ba, tsiya ce kawai ta zambo don a muzanta mutum.

A wakar, Shata ya tabo tarihin dalilin wakar, ya ce:

“Mun sabani a Jos,

Mun daidaita rannan a bukin Babangida,

Sai a Kaduna ta koma danya,

Ya zagi su Lalo gidan Maikoko.”

Shi ko Malam Danmani, bai rika maimaita wakarsa ba tun daga lokacin da ya yi ta a ka dauka a faifai. A wata hira da Yusufu Ladan ya yi da Shata a Rediyon Nijeriya na Kaduna a 1970, Shata ya bayyana cewa wakar Malam Danmani ita ce zambo na farko da ya yi inda ya ambaci sunan mutum muraran.

Kuma ina jin a yawancin wakokin zambo da ya yi daga bisani ba ya ambatar sunan mutum, sai dai ya yi kwatance ta yadda za a gane wanda ya ke yi wa zambon. Allah Ya ji kan su bakidaya, amin. An dauko ainihin wannan mukalar kan Shata ne daga zauren Makada Da Mawaka, inda a ka taba wallafa ta a LEADERSHIP A YAU LAHADI.

Malam Ibrahim Sheme fitaccen marubucin rayuwar Marigayi Alhaji Mamman Shata ne kuma dan jarida a Babban Birnin Tarayyar Najeriya, Abuja. Yanzu haka Malam Sheme shi ne kakakin Jami’ar NOUN na kasa bakidaya mai rike da mukamin darakta
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: