Connect with us

Uncategorized

Zaman Duniya A Yanzu Sai Da Mace Mai Ilimi – Fauzia

Published

on

Masu karatu kamar ko wane mako, a yau ma mun yo muku tsaraba a shafin naku mai farin jini na Duniyar Makarantu. Bakuwarmu ta yau, ba wai kawai ta yi makarantar gaba da sakandare ba ce, a’a, yanzu haka malama ce mai koyarwa. A cikin hirarmu da ita, ta bayyana muhimmancin ilimin ‘ya mace a zamantakewar rayuwa musamman bangaren abin da ya shafi aure. Wakazalika ta yi tsokaci kan rayuwarta ta makaranta mai ban sha’awa da masu shirin shiga makarantar gaba da sakandare za su yi koyi da ita. A karanta hirar har karshe domin jin wadannan da ma sauransu birjik:

Da farko za ki fadawa masu karatu cikak-ken sunanki da sunan da aka fi saninki da shi?

Sunana Fauzia M. Bala, amma ana kirana da Me Agogo a Socail Network.

Ko za ki fada wa masu karatu dan takaitaccen tarihinki?

Alhamdulilah, takaitacen tarihina shi ne an haifeni  a Kano a unguwar kundila zoo road a shekarar 1992, mu twins (‘yan biyu) ne, ni Fauzia ita Faiza. Ina da aure da yara biyu na gode.

To ya batun karatu fa, masu karatu suna so ki bayyana musu yadda ya kasance a gareki?

Alhamdulillah na yi firamare a Kano na yi sakandare  Kano sanan na yi NCE da  B.ed dina a Kano FCE Kano, yanzu kuma ina aiki. Na gode.

Da kyau! Idan muka koma baya, kafin kammala makarantar sakandare dinki wacce makaranta kika yi burin cigaba cikinta?

Toh a gaskia na taso da burin zama lawyer (lauya) amma daga baya saboda  malamin makaranta yana mutukar birgeni kawai na karkata da hanklina kai, kuma Alhamdulillah ina alfahari da zamowata malamar makaranta.

Masha’Allah! Ya za ki bayyanawa masu karatu irin gwagwarmayar da kika sha wajen neman admission?

A gaskia babu abun da zancewa mahaifina (Allah yaji kansa ya gafarta masa amin ya Allah) a shekarar dana gama secondary school a shekara na samu admission, baba na ya ce mun na zo na tafi FCE Kano na yi rajista, admission har gida baba ya kawo mun kawai dai da kaina na yi rajista, na gode.

Ko za ki tuna sabbin abubuwan da kika ci karo da su tun daga farkon cike form har zuwa rajistar shiga makarantar?

Abubuwa ba’a magana kam kin san sabon shiga babu abunda ban matawa iren wani layi da na ga an yi sababbin students (dalibai) iri na karbar lambar rajista sai da na yi kwana hudu a jere ina zuwa kafin na samu na karba, sannan zagayen sign (rattaba hannu) shi ma ba na mantawa.

Gaskiya ne, bayan da kika shiga makarantar FCE ko za ki iya tuna mutanen da kika fara cin karo da su a makarantar?

Farkon shiga ta, na hadu da mutane da dama, haduwar da bana mantawa ita ce wata,haduwata da Agathaj chisom, ita ba ta taba zuwa Kano ba sai da ta samu admission a FCE, a gaskia ba ta jin Hausa kuma tana jin son tasha ruwa, kuma ba ta san yanda za ta kira me ruwa ba muna tare a lokacin muna harkar signing kawai sai tsintar muryar ta na yi tana bin me ruwan siyarwa (me pure water) tana kiransa da ‘Sanyi’! hahhaa ranar na yi dariya kamar me, ba na manta ranar gaskiya.

Ya farkon shigarki aji ya kasance?

Na dan ji wani abu, amma daga baya sai na ware tunda ina haduwa da su Agatha Chisom muna yin karatu kamar a sakandare.

Ya darasin ranar ya kasance?

Mun shiga class (aji) around (kamar misalign karfe) 8:40am sai aka ce malama Asiya ce zat a shigo ta na daukan Geography (Kimiyyar sanin kasa), muna zaune ta shugo ta fara da rubutu subject (darasi) da topic (batu) da date (kwanan wata), sai kuma ta rubuta population (batun yawan jama’a) ta yi tambayar cewa waye ze gaya mata menene ma’anar population? A lokacin ina daya daga cikin wanda suka daga hannunsu ganin da ta yi mun Bahaushiya ya sa ta nuna ni da hanunnta a kan na tashi na fada mata meaning din (Ma’anar) population. Alhamdulillah haka na tashi na bata, wasu daga cikin ‘ya’yan Hausawa sai kallona suke, saboda kin san hausawan mu suna jin kunyar magana a cikin jama’a.

Gaskiya ne, in na fahimce ki ba ki ji wuyar darasin ranar ba kenan?

Gaskia don ba karamin hadda nake yi ba ina sakandare, shi ya sa na tashi da karfina na ba da amsa.

Kasancewar rana ce ta farkon zuwanki makarantar, shin ba ki ji wani abu ba lokacin da kuke zaune aka fara yi muku darasi kafin a zo ga tambayar ba?

Na ji wani abu tunda na ga a class (aji) har da sa’anin mahaifana, sai na godewa Allah da na fara karatu a karancin shekaruna.

Da kyau! Kusa da wa kika fara zama a farkon shigarki aji?

Toh fa! bari muga na ta fi tunani, gaskia I can’t recalling (ba zan iya tunawa ba), kawai dai nasan mun kai muna da yawa a gurin.

Da suwa kika fara kawance a makarantar, kuma mene ne musabbabin haduwarku?

Na fara kawance da Rahama Ahmad da Sumayya Yahaya B2rai, musabbabin kawancen mu shi ne a massalaci muke haduwa sai muka ga department (Sashen karatu) din mu daya shi ne muka zama Friends (kawaye).

Masha’Allah! Ya zirga-zirgar zuwa makarantar ta kasance?

Ai ba a cewa kumai, saboda yanayin abun hawa amma an sha gwagarmaya.

Me ya fara ba ki tsoro ga makarantar FCE Kano?

Carry ober (maimaita darasin baya)! Na ga yanda aka ringa korar mutane a edams (jarrabawar) din first semester (zangon karatu na farko) a NCE 1 (shekarar karatun NCE ta farko).

Ya zamantakewar rayuwar makarantar take kamar yanayin shigarsu da kuma mu’amular maza da mata na makarantar?

Kin san jami’a kowa na da ‘yancin kansa, Kowa shigarsa yake yi son ransa kuma mu’amalar mata da maza sai dai a yi kawai saboda kin san yanayin irin yarukan da suke cikin makarantar.

Haka ne, toh ya batun da ake cewa wasu in suka shiga makarantun gaba da sakandare dabi’unsu sukan canja su dauko dabi’ar da ba tasu ba, haka kuma wajen shigar kaya (dressing) wasu sukan fito daga gidansu da kayan kamala da mutunci  idan suka fito sai su canja su shiga makaranta a haka shin ya zancen yake?

Toh, abun ne sai addu’a wallahi, mun ga irinsu ba su da adaddi daga Hausawan mu har wani tribe sauran yaruka) din za ki ga yarinya ta saka hijab har kasa a gidansu tana shigowa za ki ga ta cire ki ganta daga ita sai kananun kaya ita ala dole ga ‘yar Jami’a, sanan ki ga wata da abaya ashe a kananan kayan na ciki sai dai kawai ki gansu a masallaci suna canja shiga, Allah dai ya shirya mana zuri’a amin kawai.

Ya kike ji a zuciyarki a duk sanda kika ci karo da masu irin wannan hali?

Ina musu fatan Allah ya shirye su, ya sa su gane hanyar ba me bullewa ba ce.

Wacce shawara za ki bawa masu irin wannan halin?

Shawarar da zan basu itace, don Allah su dena saboda su ma in yaran su suka yi musu ba za su ji dadi ba, kuma dukkan abun da suke Allah na kallon su.

Wanne darasi ne yafi baki wuya kuma me ya sa?

Maths (lissafi) kenan ba na son shi ko kadan wallahi saboda yana caja mun kai ko one plus one (daya a tara da daya) ba na so. Balllantana a je ga kan manyan lissafi.

Wanne darasi kika fi so, kuma me ya sa kike sonsa?

Ina son darasin social studies (nazarin zamantakewa) saboda ina mutukar gane shi, a gaskia ma ina son a bagaren karatu fagen da ba lallai sai edplains din teacher (bayanin malami) ba za ka yi amfani da understanding (fahimta) dinka.

Da kyau! Wacce dalibace ta fi burgeki kuma me ya sa take burgeki?

Ina son dalibar da ta fi kowa kokari da saurin ganewa nama fi kula irin su ko dan na karu a har kar karatu

A bangaren maza fa wa ya fi burgeki kuma me ya sa yake burge ki?

Maza akwai Ayuba Salis Kargi, sosai yake ganewa don kusan 4 point (babban maki) yake dauka to shi ma a lokacin yana birgeni saboda karatun yake yi sosai.

A bangaren malamai wanne malami ne ya fi burgeki kuma me ya sa yake burgeki?

A gaskiya akwai wani lecturer (malami) din mu Dr kazeem   education department yake. Ina son koyarwar saboda ina ganewa, curriculum yake daukan mu kusan duk semester (zangon karatu) yana daukan mu shiyasa nake son.

Mene ne burinki kafin ki kammala makarantar FCE a lokacin?

In yi aure na haihu.

Akwai wasu maza masu cewa ba za su auri yarinyar da ta yi makarantar gaba da sakandare ba gwara su nemo wadda ba ta karasa ba su aura, shin me za ki ce a kan hakan?

Ai shi ilimin mace na da amfani a rayuwarmu ta yanzu. Ni a gaskia na jahilci maganar saboda a zamanin yanzu, ko ba komai zaman duniyar ma yanzu sai da mace me ilimi, yanzu duk kyan ki in ba kida ilimi shi kansa namijin kunyar fitar da ke cikin jama’a yake, kuma kodan zuri’ar da zaka haifa kaso mace me ilimi,ba karamin taimakawa mahaifiya take bawa yaran ta ba, menene amfani yaro yazo da home work gida mahaifiyarsa na turasa makota ayi masa? ag askia ina bawa maza shawara kodan yaranka ka nema musu mahaifiya me ilimi, na gode.

 

Mene ne ra’ayinki game da ci gaban karatun mata na gaba da sakandare?

Gaskiya ni a ra’ayina yana da kyau mace ta ci gaba da karatu koda yana yin rayuwa, yau da gobe sai Allah, yanzu ko business (kasuwanci) din mace za ta yi sai da ilimi, mene ne ilimin shi ne yanda za ki sadar da kayan yanda za ki yi magana da me so. In babu cigaban karatun wallahi akwai matsala sosai gaskiya ma yanzu, komai ya zama sai da Masu ilimi shi ya sa nake ganin gwanda mace ta ci gaba da makarantar gaba da sakandare.

Ya za ki bambanta wa masu karatu bambancin macen da ta yi karatun gaba da sakandare da kuma na wacce ba ta yi ba?

To a gaskiya akwai banbanci iri-iri amma abu na farko kowane na da balues (daraja), before (a baya) in mace ba ta yi karatun gaba da sakandare ba; za ki ga babu matsala ko kadan saboda da dama iyayenmu na da duk basu yi karatun gaba da sakandare ba, amma suna zaune lafiya a dakunan su, saboda halayyar da data yanzu ba daya ba, amma yanzu fa inda aka yi wa yarinya aure daga gama sakandare wallahi sai kin ga bambaci fa.. wallahi ko ta yanda mace za ta zauna da mijinta sai kin yi kuka saboda ba ta da wani edperience (basira) a kan abun, in kuwa mace ta cigaba da makarantar gaba da sakandare ba ma sai an fada maka ba za ka gane ko dan wayewa da yanayin zamantakewarta, duk da dai wani lokacin auren wuri na da fa’ida a kan cewa sai yarinya ta gama jami’a.

Gaskiya ne, a naki hangen wanne amfani karatun ‘ya mace yake da shi?

Shi ilimin mace ai zurfi gare shi, yanzu kamar a makarantun firamare wallahi baby class and nursery (ajin yara kanana) duk mata ne malaman, saboda mace ita ta san yanda za ta iya da yaro, namiji babu ruwansa mace za ta jure komai a kan kowani irin situation (yanayi), namiji fa wallahi ba zai jure ba. Na san ana cewa in ka ilimitar da mace daya za ta ilimatar da mutum goma ko fiye da haka ma, kuma gaskiya a yanzu women’s education is not end the kitchen (ilimin mace ba ya tikewa a dakin girki).

Haka ne, ko za ki bawa masu karatu labarin yadda kika kammala karatunki na FCE tun daga farko har karshe a takaice?

Toh, Alhamdulilah babu abin da za mu ce wa Allah. Duk wani karatu da za ka yi akwai fadi-tashi, toh tunda neman ilimi ka fito yi dole sai ka yi hakuri, na yi karatun successful (cikin nasara) a FCE, matsalata daya gurin karbar result (sakamako) ne sai da na yi kamar zanyi hauka. 1 year (shekara daya) ina abu daya saboda yanayin kasarmu, amma Allahamdulilah sai da na fara fid da rai sai kuma Allah ya bani ikon karba.

Shin kin taba fuskantar matsala game da jarrabawa?

Toh, eh zan ce ko a’a, amsa daya ce dai na sani na samu matsala da missing scripts (bacewar takardar amsar jarrabawa) amma daga baya komai ya wuce.

Wacce shawara za ki bai wa masu kokarin shiga makarantun gaba da sakandare?

Shawara daya ce ita rayuwa da mutane suke gani ba matabbaciya ba ce, magana ce me zaman kanta, Manzon Allah ya ce ku nemi ilimi daga nan har birnin Sin, kin ga babu laifi dan an nemi ilimi.

Ko kina da wadanda za ki gaisar?

Yes ina da Wanda zangaisar, Ina gaisar da Mahaifiyata Hajiya Saratu Maitama Farouk da megidana SSG na gode.

Me za ki ce ga masu karanta wannan shafi na Duniyar Makarantu?

Ina yi wa masoyan Duniyar makarantu fatan alheri, Allah ya bar kauna.

Amin, me za ki ce da ita kanta jaridar LEADERSHIP A Yau Juma’a?

Ina yi wa gidan jaridar LEADERSHIP fatan alheri, Allah ya kara daukaka ya kara ci gaba amin ya Allah, ya kara nasara da ci gaba a kan dukkanin al’amura amin.

Muna godiya Malama Fauziyya da bamu lokacinki da kika yi.

Ni ma ina godiya da gayyatata zuwa Duniyar makarantu.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: