Connect with us

FITATTUN MATA

Hasina (Sheikh) Wazed: Fira Minista Ma Fi Dadewa A Tarihin Bangaladesh

Published

on

*Ko Kun San?

 Hasina ita ce Fira Ministar kasar Bangaladesh, kuma ta 36 a mahukunta masu daraja ta daya a duniya?

An haifi Hasina ranar 28 ga Satumba 1947 a birnin Tungipara Upazila, cikin kasar Bangladesh. Sannan ita ce Fira Ministar kasar Bangladesh tun daga Janairun 2009 zuwa yau. Kafin wannan lokacin, an tabbatar cewa Sheikh Wazed ta taba rike wannan mukamin daga shekarar 1996 zuwa 2001, sannan ta rike gidauniyar siyasar lardin Awami a kasar ta Bangladesh a shekarar 1981.

Kamar yadda bayanai suka gabata, Hasina na daya daga cikin manyan mahukunta da duniya ke tinkaho da su. Ita ce ta ke a lamba ta 36 cikin jerin shugabannin. Ta shafe akalla shekara 40 tana cikin sansanin ikon kasar, bayan jan ragamar adawa da ta rika yi a kasar a siyasance.

A yayin irin wannan gwagwarmayar adawar siyasa, Hasina ta tsallake rijiya da baya a yanayi daban-daban a shekarar 2004. Haka kuma ta gamu manyan jarrabawa daban-daban a yayin fafutikar neman kafuwa a matsayin shugabar ragamar adawar kasar. Wannan ta sa sai da aka kama ta, gami da gurfanar da ita bisa zargin cin hanci da rashawa a shekarar 2007, wanda jami’an mulkin soja suka yi mata a yayin rikon kwaryar da aka ba su, sakamakon rikice-rikicen siyasar kasar da ya munana daga 2006 zuwa 2008.

Duk da haka, jarumar ba ta yi kasa a gwiwa ba, ta ci gaba da gwagwarmayar siyasarta, inda ta sami rinjaye da galaba mai karfi a zabukan da aka shirya a kasar a shekara ta 2008. Haka kuma a shekarar 2014 ta kasance Fira Minista a karo na uku, inda ta rika yin galaba a siyasance, kasancewar ‘yan kasar mafi rinjaye suka ci gaba da mara mata baya. Duk da matsin lambar da ta rika samu daga abokiyar hamayyarta Khaleda Zia, Sheikh Wazed ta ci gaba da jan ragamar siyasarta daidai yadda za ta rika samun yarda da rinjaye daga masoyanta.

*Shin Wace Ce Sheikh Hasina?
Kamar yadda bayanai suka gabata, haifaffiyar kasar ta Bangladesh, Hasina ita ce diyar Shugaban Kasar Bangladesh na farko, Sheikh Mujibur Rahman. Kamar yadda ta rika bayyanawa a mafi yawan tattaunawa da take yi a kafafen yada labarai, Hasina na cewa ta taso cikin tsoro da fargaba, musamman idan ta yi la’akari da rin gwagwarmaya, hadurra da kalubalen da mahaifinta ya rika fuskanta a duniyar siyasarsa.

Tana bayyana irin tashin hankalin da ta gamu da shi a yayin tarzomar siyasar da mahaifinta ya fuskanta a shekarar 1970, wanda ya tilasta mata fadawa sansanin ‘yan gudun hijira, karkashin kulawar kakarta. Ta kan bayyana cewa, wannan tashin hankalin, ya haifar mata da ci-baya ainun a harkar karatunta.

A cikin tarzomar siyasar ne aka bindige mahaifinta, ranar 15 ga Agusta, 1975, a lokacin da take sansanin na gudun Hijira da kakarta. Duk da hakan, ba su sami damar komawa kasar tasu ba, har sai lokacin da ta kammala karatu ta shiga siyasa, aka zabe ta shugabar gwagwarmayar jam’iyyar yankin Awami a watan Fabrairun 1981.

Babban abin da ya fi daukar hankalin manazarta tarihi game da wannan baiwar Allah shi ne, irin tashin hankali da kalubalen da ta rika fuskanta, tun daga tashinta zuwa yanzu da take gadon mulki. A tarzomar siyasar da ta yi awon gaba da mahaifinta, wanda yake bisa mulkin kasar a lokacin, daga ita Hasina sai kanwarta da kakarsu kadai suka rayu. Hakan kuwa bai sa ta ja da baya ba.

A yau, Hasina na daya daga cikin fitattun matan da duniya ke alfahari da su, musamman idan aka yi la’akari da irin salon siyasarta.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: