Connect with us

LABARAI

Mutanen Da Mahara Suka Addaba A Neja Sun Fara Bore

Published

on

Sun Toshe Wata Babbar Hanyar Gwamnatin Tarayya

  • Sun Bayyana Yadda Maharan Ke Cin Karensu Ba Babbaka

 Dubban ‘yan gudun hijira da suka fito daga kauyukan Madaka, Hana Wanka da Kukoki, Wayam da Malawai da ke kan iyakokin kananan hukumomi Rafi da Shiroro sun toshe hanyar shiga garin Kagara a ranar Larabar nan.

Al’amarin dai ya auku ne a sakamakon tunzurin da ‘yan kauyen suka yi game da irin cin mutuncin da suka ce mahara na yi musu tare da iyalansu.

Wadanda suka zanta da wakilinmu da suka yo gudun hijira zuwa Kagara, sun bayyana yadda maharan ke cin karensu ba babbaka a yankunansu da suka ce sun mamaye.

Da yake zantawa da wakilinmu, Dagacin Durumi da ke gudun hijira, Malam Muhammad Abubakar ya ce dukkanin jama’ar garinsa sun yi kaura zuwa garin Kagara sakamakon hare-haren masu garkuwa da mutane.

A cewarsa, “yanzu haka rahoton da ya zo muna a Larabar nan da misalin sha biyu na rana, barayin sun yi awon gaba da mutane biyar daga Durumi kuma sun yi ma wani yankan rago kuma har zuwa yanzu (Laraba) sun ki ba da gawar. Kimanin watanni takwas ke nan muke ta fuskantar barazanar wadannan mutanen kuma mun sanar da gwamnati amma ba wani matakin da ta dauka.

“Jama’ar garuruwan Madaka, Hana Wanka, Kukoki da Malawai, har zuwa Fangu gari, da Natsira, Zuwa Durumi duk sun watse duk wadannan garuruwan da na kira ma idan za ka tafi yanzu ba za ka tarar da kowa ba sai wadannan batagari,” in ji shi.

Har ila yau, Dagacin ya bayyana barnar da ‘yan bindigan suke musu ta sace-sace na rashin imani.

“Bayan mun wuto mun samu labarin suna shiga gidaje suna kwashe kayan sawa na jama’a, abinci da sauran abin da suka tarar. Mu fa yanzu ko sansanin ‘yan gudun hijirar da aka ce gwamnati ta bude ba ta iya daukar kashi bakwai cikin gomar jama’ar da cikin garin nan ba, taimakon Allah jama’ar gari sun amince da baiwa mata da yara mafaka, amma maganar abinci kan babu shi domin kowa na cikin halin kuncin rayuwa.

“Daga cikin ‘yan gudun hijirar akwai matar da ta haihu bayan kazamin wahalar da ta sha na tafiya, daga Kukoki zuwa Kagara kimanin tafiyar awa daya da rabi. Mata dai ba su tsira a hannun bata garin a kan irin hare-haren da suke kai masu wanda bayan fyade da walakantasu yanzu haka akwai matar da ke kwance a wani asibitin kudi wadda ta ce maza goma sukai mata fyade wanda zuwa yanzu tana zubar da jini,”in ji shi.

Rahotanni da dama sun nuna sama da watanni takwas ke nan da ‘yan ta’addan barayin shanu da garkuwa da mutane suka kaddamar da hare-hare a iyakokin karamar hukumar Rafi da Shiroro wanda zuwa yanzu dubban mutanen suka tarwatse daga garuruwansu da har yanzu ‘yan’uwansu ba su san inda suke ba, bayan daruruwan da ke hannun ‘yan ta’addar da ‘yan uwansu ba samu kudaden karbo su ba.

Rahotannin dai sun tabbatar da ire-iren hare-haren da ‘yan ta’addan ke kaiwa ba su tsaya kan mutanen karkara ba domin ko a satin da ya gabata sun kai hari cikin garin Kusharki inda bayan awon gaba da wasu mutane sun bar mutane da dama da raunukan harsasan bindiga.

Malam Muhammad Abubukar, Dagacin Durumi da ke masarautar Kagara, ya yi wa wakilinmu karin hake inda ya ce, “mutanen suna shigowa cikin kauyuka da mashuna sama da ashirin wanda a kowani za ka yana dauke da mutum biyu ko uku kuma dukkansu dauke da makamai. Yanzu haka sun yi sansani a cikin garin Kukoki sun tara mashunansu wuri daya inda suka mamaye yankin suna tafka ta’asarsu ba tare da tsoro ko fargaba ba; har ma suna ikirarin cewar yanzu su ne masu gari.”

A nata bangaren, wata da abin ya shafa, Malama Aisha wadda ta fito daga kauyen Wayam, ta ce, “tun muna jurewa sun fara shiga cikin dakunan matan aure suna abin da suka ga dama, wani lokacin ma sukan bukaci a yi masu girki kuma dole abin da suke so ne za a girka masu, yanzu haka akwai yarinyar da aka kawota daga Kukoki tana zubar da jini wanda ta ce mutane goma ne sukai mata fyade, yau laraba da safe (hekaranjiya) mun yi yunkuri komawa gida dan dauko kayanmu, amma sun rufe hanya sun ce ba shiga kuma ba fita, sun shiga gidajen jama’a suna kwashe suturun jama’a da abinci.

“Maganar cewar fulani ne ba gaskiya ba ne, domin ba irin yaren da babu a cikin su dukkansu suna sanye da kayan sojoji ne. Mazajenmu dole sun watse sun bar gonakinsu a lokacin da ake shirin fara aikin gonar domin muna gab da fara aikin masara ne wannan bala’in ya sauko,” a ta bakinta.

Zuwa yanzu dai tun bayan kammala sharar daji na sojoji da aka yi wa lakabi da ‘tseren mage’, wato “Akwai Akpatuma” a yankin na tsawon kwanaki goma sha hudu ba wani jami’in soja ko dan sanda da aka kai dazukan.

Malam Muhammad Kagara, daya daga cikin jagororin shirya zanga-zangar lumana da tare babbar hanyar Kagara zuwa Birnin Gwari wanda mallakin gwamnatin tarayya ne, ya yi bayanin cewa, “yau kimanin sati daya ke nan da ‘yan gudun hijirar ke ta kwaroruwa zuwa cikin garin Kagara amma har yanzu gwamnati ko hukumar kula da agajin gaggawa ta jiha ba wani matakin da ta dauka a kai, yanzu haka babu wani gida a garin nan ‘yan uwa da ma wadanda ba a sansu ba da ba su aje da kananan yara da matan aure a kallan mutum goma ko ma sama da hakan, wanda ganin hakan ya sa muka fito dan yin wannan gangamin duk da haka Gwamna ko wani jami’in gwamnati ba wanda ya ce mana ko da ‘ci kan ku’.

“Tau, tunda haka ne muna nan sai abin da Allah ya yi, domin yanzu haka da muke magana da ku ‘yan jarida ruwan sama ake yi fa, kuma kana kallon ga mata nan da kananan yara ba su da mafaka, wanda muna jin tsoron abin da hakan zai haifar.”

Da aka tambaye shi ba su ganin sun shiga hakkokin masu bin wannan hanyar da suka ja daga a kai? Malam Mahmuda ya amsa da cewa, “Maganar cin zarafin matafiya kuwa, ba mu ne muka ci zarafinsu ba gwamnati ce ta ciki zarafinsu domin ta kasa daukar matakin kare rayukan jama’a da dukuyoyinsu wanda ta bari har ‘yan ta’adda sun fi mutanen kirki kima a idon gwamnati, dan ba ta nuna damuwarta a kansu ba duk da irin halin fargaba da cin zarafinsu da ‘yan ta’addan ke yi duk da cewar suma suna da hakkin kare rayuwarsu da dukiyioyinsu saboda su ma sun yi zabe kamar kowa,”in ji shi.

Lokacin da wakilinmu ya leka sansanin ‘yan gudun hijira da ke Makarantar Firamare na yankin (Central Primary School) da misalin 12 na ranar larabar nan dan ganin ‘yan gudun hijirar da aka tantance suke ciki, ya tarar da shinkafa buhu bakwai, masara buhu shida, manja galon daya, bokitin roba guda ashirin da sabulun wanka katon uku wanda aka ce hukumar kula da agajin gaggawa ta jiha ( NSEMA) ta kawo wanda dubban jama’ar da ke sansanin ke ta nuna takaicinsu a kai.

Har zuwa hada wannan rahoton dai ba wani jami’in gwamnatin jiha ko ta karamar hukumar Rafi da Shiroro da ya yarda ya ce uffan a kan lamarin.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: