Connect with us

BABBAN BANGO

Yadda Taron Koli Na Raya Abota Tsakanin Matasan Kasar Sin Da Na Afrika Ya Gudana

Published

on

A ranar 27 ga watan Augustan 2019 ne aka bude taron matasan Sin da Afrika karo na 4 a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin. Manufar taron ita ce, musayar al’adu da cudanya tsakanin matasan bangarorin biyu, domin kara dankon zumunta da ci gaba da raya dangantakar kasar Sin da kasashen Afrika, a matsayinsu na matasa manyan gobe.

Musayar al’adu da abota tsakanin matasan Sin da Afrika, daya ne daga cikin bangarorin da aka ba da muhimmanci karkashin Dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afrika wato FOCAC.

Yayin bude taron wanda ma’aikatar harkokin wajen Sin ta karbi bakuncinsa, mataimakin ministan ma’aikatar, Chen Xiaodong, ya ce shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sha cewa, nahiyar Afrika da Sin na da makoma ta bai daya. Ya ce a bana ake cika shekaru 70 da kafa Jamhuriyar Jama’ar kasar Sin, kuma cikin shekaru 70 da suka gabata, karkashin buri iri daya da bangarorin biyu ke da shi, an samu hanyar raya dangantaka irin ta moriyar juna. Ya ce musayar al’adu da cudanya tsakanin matasan bangarorin biyu na taka muhimmiyar rawa ga dangatakarsu. Ya kara da cewa galibin shirye-shiryen da aka gabatar karkashin dandalin FOCAC, na mayar da hankali ne kan matasa, ta fuskar horar da su da tallafa musu.

Ya jaddada cewa, duniya yanzu na fuskantar sauye-sauyen da aka dade ba a gani ba. Kara zurfafa dangantakar abota tsakanin Sin da Afrika, zai taimaka gaya wajen karawa kasashe masu tasowa karfi, da taimakawa wajen bunkasa huldar kasa da kasa da tabbatar da adalci da daidaito da kuma ingiza ci gaban duniya baki daya.

Ministan ya kara da cewa, suna fatan dangantakar matasan bangarorin biyu zai kara daukaka aminci da dagantakar Sin da Afrika da gina al’umma mai kyakkyawar makoma tsakanin Sin da Afrika da samar da zaman lafiya da ci gaba da wayewar kan bil adama.

Taron wanda aka gudanar a Beijing da kuma birnin Guangzhou, ya gudana ne tsawon kwanaki 10. Kuma cikin wadannan kwanaki, matasan sun ziyarci wurare da dama da suka hada da tarihi da al’adu da kamfanonin fasaha da garuruwan da aka raya da sauransu.

Daga cikin wadannan matasa da suka halarci taron, akwai Yeukai Hanyyani, ’yar asalin kasar Zimbabwe, mai shekaru 27, kuma ta shaidawa sashen Hausa na CRI cewa, abun burgewa ne yadda kowanne gari ke samun ci gaba a kasar Sin, “wato ba fadar mulkin kasa ba kadai”. Ta ce yadda ake samun ci gaba a baki dayan kasar ya cancanci yabo. A ganinta, wannan taron da aka yi somin tabi ne, ya kamata a kara samar da wasu shirye-shirye, kamar dandalin tattaunawa ta matasan Sin da Afirka,  irin na FOCAC, tana mai cewa, za a iya kara amfani da dandalin wajen inganta  musaya tsakanin matasa. Ta kara da cewa, gudummawar da za ta bayar ga raya dangantakar bangarorin biyu shi ne, kai abubuwan da ta gani gida, kamar sakamakon da ta gani karkashin manufar bude kofa da gyare-gyare, ta yadda za a samu a kwatanta aiwatarwa a kasarta, saboda akwai darrusa da dama da za a iya koya.

Shi kuwa Tourad Medou mai shekaru 33, dan kasar Mauritania, cewa ya yi, wannan taron ya masa dadi, kuma a ganinsa za a cimma nasara idan aka samar da karin dandalin musaya da tattaunawa tsakanin matasan Afrika da Sin. Ya ce lallai cikin shekaru 70 da kafa Jamhuriyar kasar Sin, an samu dimbin nasarori, domin a matsayinsa na masanin tattalin arziki, ya ga sauyi sosai tattare da tattalin arzikin kasar. Ya ce “a kullum kara ingantuwa yake yi. Na zo kasar Sin domin yin digiri na biyu a shekarar 2009, bayan shekaru 2 kuma, na koma kasata Mauritania. Zuwana a wannan karon, na ga sauyi sosai a zaman rayuwar Sinawa da komai da komai. A ganina tattalin arzikin kasar Sin na samun ci gaba ne saboda bude kofarta da ta yi na cinikayya da sauran kasashen duniya, shi ya sa kullum alkalumanta na GDP ke tashi sama. Ina ganin wannan wata dama ce ta kara fahimtarmu a kan al’adu daban-daban na kasar Sin kamar dai yadda aka yi a wannan taro. Kuma kamar yadda kowa ya sani, kasashen Afrika sun taimakawa Sin a MDD a baya, kuma yanzu kasar Sin tana taimakawa kasashen Afrika sosai. Zan yi misali da kasata Mauritania, duk wani gini mai kyau. Kasar Sin ce ta yi shi, ciki har da asibitoci da tashar jiragen ruwa, komai da komai dai mai kyau da za a gani a Mauritania, to kasar Sin ce ta yi, don haka, ina ganin dangantakar kasashen na da muhimmanci sosai, kuma shugabannin Afrika na kokarin raya ta. Zan iya tunawa, shugaba Xi Jinping ya taba cewa, babu abun da zai raba Sin da Afrika, kuma bangarorin biyu za su ci gaba da mu’amala da samun ci gaba”.

A ganin Eromosele Ehigie Daniel mai shekaru 40, da ya fito daga Nijeriya,  wannan ziyara ta sa ya kara fahimtar abubuwa game da kasar Sin. Ya ce turukan da suka halarta ya nuna masa cewa, akwai abubuwa da dama masu kama da juna tsakanin Nijeriya da Sin. Ya ce ya yi mamakin ganin jita da ganguna kamar dai irin na gida. Abun da ya fi burge shi a ziyarar shi ne, hawa jerin duwatsu da a Babbar Ganuwar Kasar Sin. Ya ce a Nijeriya ma akwai duwatsu, shi ya sa ya ce akwai kamanceceniya da dama tsakanin Sin da Nijeriya. Kana ya ga abubuwa da dama da yake gani a bidiyo a gida. “Gaskiya wannan ziyara ta burge ni”, a cewar Eromosele Daniel. Ya kara da cewa, “mun je hukumar dake kula da zirga-zirgar ababen hawa, inda muka ga wata ingantacciyar fasaha da ake amfani da ita wajen gano masu take dokokin hanya cikin sauki. Kuma ko da gilashi motarka baka ce wuluk, da abun da na gani yau, idan dai ka keta dokar titi, to za a iya ganinka. Fasahar ta cancanci a yi koyi da ita. Wannan ci gaba ne sosai, kuma mu ma a Afrika muna iyakar kokarinmu, amma dai ba mu kai matakin abun da na gani yau ba, sai dai da sannu za mu isa” har ila yau, ya ce a gaskiya duk da ranekun ba su da yawa, abubuwan da ya gani ya kuma fahimta, sun zarce yawon ranekun ziyarar.

Ya ce kasancewar kasar Sin daddadiyar kasa, ba zai yi mamaki da irin ci gaban da ta samu ba. Amma abun da ya fi ba shi sha’awa shi ne, yadda suka tabbatar da dorewar ci gaban da suka samu. “Shekaru 70 da kafa jamhuriyar jama’ar kasar Sin zuwa yanzu, ya nuna cewa, tsarin siyasar kasar Sin ya dace da kasar. Abu mafi muhimmanci shi ne, idan kana abu, kuma kana jin dadinsa, to sai ka ci gaba da yinsa. Ina ganin Sinawa suna farin ciki da yadda ake tafiyar da gwamnati. Zan yi misali da wani gari da muka je, wanda aka ce mana a da karkara ce, abun da  na gani a can ya ban sha’awa. Wato abun da ya fi muhimmanci a tsarin gwamnati shi ne, ayyukan da gwamnati ta aiwatar, don gaskiya abun da na gani ya burge ni kwarai, don kauyen ya zama maraya sosai. Bisa hikima da hangen nesa irin na shugaban kasar, ya ja hankalin kamfanoni zuwa yankin, idan su kuma suka dauki ’yan asalin wuri aiki, sannan ake samar da kaya a wajen. Baya ga haka an samar musu da sadarwar intanet, inda suke amfani da ita wajen tallata kayansu a kan intanet. Wannan shi ne abun da mutane suke bukata, ai gwamnati ta mutane ce, idan har kana hidimta musu, to ka gama komai”.

Har ila yau, da yake tsokaci kan dangantakar Sin da Afrika, Eromosele Daniel ya ce ana samun kyautatuwar alakar. Kuma daga abun da ya gani, ya ga wata irin kyakkyawar alaka tsakanin bangarorin biyu. Ya ce shugaban kasar Sin yana da hangen nesa da kaifin basira, la’akari da yadda yake iya hango abubuwa masu amfani kuma yake aiwatar da su, ko da kuwa a lokacin ba za a ga ribar hakan ba. Ya ce da irin kudin da ake kashewa, ya tabbata shugaban kasar ya ga wani abu mai amfani da zai auku a nan gaba. Ya kara da cewa, matasa su ne kashin bayan kowacce al’ummar, kuma shugaba Xi Jinping ya yi kokarin gano hakan. Akwai damarmaki mai dimbin yawa a nahiyar Afrika, kuma duk wata kasa mai basira da ta iya gano wannan, to ba za ta yi nadama ba. Domin wannan dangantaka za ta haifar da mai idona. Ya karkare da cewa, a matsayinsa na matashi, ya ma fara tunanin yadda zai bada tasa gudunmuwa wajen raya wannan dangataka. Ya ce la’akari da yadda ya yi cudanya da matasan Sin da sauran nahiyar Afrika, ya yi ammana cewa, kwalliya za ta biya kudin sabulu dangane da wannan dangantaka.

Maria Estria Mikue Owono daga Equatorial Guinea mai shekaru 27, ta ce daya daga cikin abubuwan da suka fi burge ta shi ne irin ci gaban da aka samu a fannin ilimi da kuma yadda aka samu ci gaba a fannin fasaha. Ta ce abun da ya kawo ci gaban shi ne tsaro, wato ci gaba ma da aka samu a fannin fasaha ya taimaka wajen takaita karuwar aikata laifuffuka da barkewar rikice-rikice. Ta ce “Wato suna amfani sosai da hikimar da suke da shi a fannin fasaha wajen kare jama’arsu, ta yadda za su yi rayuwa cikin aminci. Baya ga wannan, fasahar ta taimaka wajen saukaka musu rayuwa. Kamar amfani da hasken rana wajen samar da lantarki. Ni dai ba kwararriya ba ce a wannan fanni, amma kwararrun da muka tattauna da su a daya daga cikin kamfanonin da muka ziyarta, sun tabbatar mana cewa, amfani da hasken rana domin samun lantarki ya fi aminci kuma zai yi kyakkyawan tasiri akan kowanne dan  kasar, don haka idan mu ’yan Afrika muka gabatar da irin wannan tsari a kasashenmu, lallai zai yi mana amfani.”

A nasa bangaren, Olukonga Olasunkanmi Ibrahim, dan Nijeriya mai shekaru 36, ya ce yana godewa gwamnatin kasar Sin da ta ba shi damar zuwa, da hada matasan Afrika don cudanya da matasan Sin da nufin kulla dangantaka a tsakaninsu. Ya ce abun da ya fi daukar hankalinsa shi ne yadda kauyen da babu mutane da yawa ke da sadarwar 5G. Ya ce akwai wasu wurare a kasashe masu tasowa musamman na Afrika da ba su da sadarwar  4G. Ya ce “gaskiya kasar Sin ta ci gaba sosai a fannin fasaha. Kuma a yadda Sin ke taimakawa wasu kasashe, zan iya cewa kasashen Afrika ne suka fi cin gajiyarta, kuma wadanan shirye-shiryensu suka sa kasar Sin ta zama zakaran gwajin dafi.” Ya ce duk kasar dake son samun ci gaba, dole ne ta yi mu’amala da sauran sassan duniya. Kuma a ganinsa abun da ya sa kasar Sin ta fita daban shi ne, shugabanci na gari kuma mai karfi. Ya ce “a cudanyar da na yi da matasan kasar Sin, na gane suna girmama shugabanninsu sosai, kuma irin shugabancin da ake yi da karfafa musu gwiwa da tunkarar kalubele ne ya kai su ga samun ci gaba. Kasar Sin ta zuba kudi sosai a fannin samar da ilimi, kuma abu ne da kowa ya sani cewa, ci gaba na da alaka da ilimi mai inganci.” Dangane da tsarin siyasar kasar Sin kuwa, ya ce “kowace gwamnati tana da ’yancin zabar tsarin da ya fi dacewa da ita da al’ummarta, kuma shekaru 70 ke nan kasar Sin take bin tsarin siyasarta. Kuma ina ganin wannan tsarin yana musu amfani domin sun samu ci gaba sosai karkashinta. Kuma a gani na, wannan tsari ne ya fi dacewa da su.”

Game da dangantakar Sin da Afrika kuwa, Olukunga Ibrahim ya ce, akwai kyakkyawar dangantaka tsakaninsu. Duk da cewa kasashen Afrika na da alaka da kasashen da suka yi musu mulkin mallaka, cikin gomman shekarun da suka gabata, an ga tasirin kasar Sin a Afrika. Akwai babbar dangantaka mai inganci tsakanin Sin da Afrika, kuma wannan dangantaka ta samar da dimbin sakamako ga bangarorin biyu, domin ta moriyar juna ce. Ya ce, idan zai yi misali da kasarsa, Sin ta gina manyan ababen more rayuwa da dama a Nijeriya, kuma ta ba da bashi mai rangwame, sannan kamfanoninta sun zuba jari sosai a kasar. Kuma idan ka je, za ka samu Sinawa suna rayuwarsu kamar kowa, har ma suna da ungunwannisu da ake kira “China Town”. Ya ce “irin wannan dangantaka ake bukata. Zan iya bugun kirji in ce dangantakar bangarorin 2 na da karfi sosai.”

Ya kara da cewa, a matsayinsa na matashi, zai yi amfani da matsayinsa na ma’aikacin gwamnati ya kai abubuwan da ya gani ga gwamnatin kasarsa tare da ba ta shawarwari kan abubuwan da ya kamata ta koya ita ma, don ta aiwatar. Ya ce ci gaban da ya gani a kasar Sin abu ne da ya kamata gwamnatinsa ta yi koyi da shi, domin daga shekarar 2030, fasaha ce za ta ja ragamar komai. Ya ce shawararsa ga bangarorin biyu shi ne, ci gaba da yaukaka wannan dangantaka don ganin ta dore, domin kasar Sin ce ta fi dacewa da kasashen Afrika maimakon kasashen Turai da suke gindaya sharudda masu tsauri idan za su taimaka musu.

Shi kuwa Maman Garba, mai shekaru 47 daga Jamhuriyar Nijer, ya bayyana cewa, zuwansa kasar Sin ya ga kasar da ta bunkasa, kuma ya ganewa idonsa abun da yake gani a talabijin. Ya ce babu abun da bai burge shi ba domin ya ga abubuwan da bai san su ba. Ya kuma alakanta ci gaban kasar Sin da shugabanci na kwarai. Ya ce ya tabbata wannan siyasa da Shugaban kasar ke jan ragamarta, ita ce ta sa kasar ta bunkasa. Baya ga haka ya ce ya ziyarci wani gari da Sinawa ke kiransa da kauye, amma su wajensu birni ne, inda ya ga yadda gwamnati ta kyautata rayuwar mazauna wurin, ta kuma inganta musu hanyar samun karin kudin shiga, yana mai cewa “alamu ne na yunkurin gwamnatin kasar na yaki da talauci, tun da ko haraji ba ta karba daga hannunsu.” Ya ce idan kasashen Afrika suka yi koyi da tsarin siyasar kasar Sin, to dole ne su bunkasa. Domin tsarin ba shi da matsala ko kadan, kuma a ganinsa ta fi kowacce irin siyasa, domin tana bai wa talakawa damar samun wadata. Ya ce kamata ya yi a ce irin tsarin kasashen Afrika suka rungunma. Dangane da dangantakar bangarorin kuwa, ya ce ya kamata a samar da shirin da zai rika bibiyar dangantakar domin tabbatar da aiwatar da shirye-shiryen dake karkashinta. Bugu da kari, ya ce matasa su ne manyan gobe, kuma a nan gaba su ne za su kyautata dangantakar bangarorin biyu. Ya ce babu kasar da Niger ke dasawa da ita kamar Sin, kuma wannan ziyara za ta sa su kara fahimtar da sauran matasa kan kasar Sin. A karshe ya bayyana Sinawa a matsayin masu kyakkyawar tarbiyya a fannin tarbar bako, ya ce “yadda suke karbar baki ya yi kama da yadda ake yi a kasar Hausa, kuma wannan dabi’a na daga cikin dalilan da ya sa kasar ke bunkasa.”

Taron na bana wanda shi ne irinsa na 4. An yi a farko ne a shekarar 2016 a nan kasar Sin a biranen Beijing da lardin Guangdong. Sai na biyu da aka yi a kasar Afika ta kudu, uku kuma a Sichuan na kasar Sin, sai kuma na wannan karon da aka koma birnin Beijing da lardin Guangdong.

Taron na bana da aka kammala a ranar 4 ga watan Satumba, mai taken “hada burikan matasa domin samar da dangantaka tsakanin Sin da Afrika a sabon zamani”, ya samu halartar wakilai 95 daga kasashen Afrika 51, ciki har da wakilan Tarayyar Afrika AU.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: