Connect with us

KIWON LAFIYA

Yaya Cutar Maleriya Ta Ke?

Published

on

Ta Ya Ya Zamu Iya Kawar Da Malaria? Duk da cewa ana iya kare kai da kuma samun sauki har yanzu cutar zazzabin cizon sauro ko kuma Maleriya na ci gaba da kisan mutane masu yawa a duniya: ta na kashe kananan yara 2 kowacce dakika 30, ko kuma yara 3000 ko wadanne minti 2’yan kasa da shekara 5 a cikin minti biyu kuma sama da mutum miliyan 300 zuwa 600 ke kamuwa da cutar a kowacce shekara, a cewar Hukumar lafiya ta duniya.

A ‘yan shekarun baya da suka wuce ana samun canji akan yadda ake yaki da cutar Maleriya, a shekarar 2015 alkaluma sun nuna ci gaban da ake samu a yakin da ake yi da cutar . Rahoton Hukumar lafiya ta duniya, WHO a shekarar2018 ya nuna ana samun raguwar yawan masu kamuwa da cutar tsakanin 2015 zuwa 2017.

Ana Iya Kare Kai Da Samun Sauki Daga Cutar Maleriya?

Ranar 25 ga watan Afrilun aka ware a matsayin ranar yaki da cutar Maleriya a duniya, wadannan su ne abubuwan da ya kamata a sani kan cutar: Malaria cuta ce da ke barazana ga rayuwar al’umma wadda kwayar cuta ta halitta mai suna Plasmodium da suka hada da P. falciparum, P. malariae, P. obale and P. bibad. ke kasancewa sanadiyar kamuwa da ita. Macen sauro da ake kira Anopheles moskuitoes ke yada ita cutar ta hanyar cizo a jikin dan adam.

Ana Iya Kare Kai Da Samun Sauki Ko Kuma Warkewa Daga Cutar?

A 2017, mutane miliyan 291 ne aka kiyasta na fama da cutar a kasashe 87 a cewar WHO. Mutane 435,000 cutar maleriya ta kashe a shekarar2017. Cutar ta fi illa a kasahen Afirka – a 2017, kashi 92 cikin 100 na masu fama da cutar a kasashen Afirka ne kuma kashi 93 cikin 100 na wadanda suka mutu a nahiyar su ke. An tattara kudaden da yawansu ya kai $3.1bn domin yaki da cutar a 2017.

Alamomin Cutar?

Alamomin Maleriya – zazzabi mai zafi da ciwon kai da ciwon gabobi 4- wanda ke somawa bayan kwana 10 zuwa 15 bayan cizon sauro.

Alamomin na somawa ne kadankadan kuma a wasu lokutan ba a saurin gano Maleriya ce, idan ba a gaggauta soma shan magani ba cikin sa’o’i 24 cutar ta kan yi kamari wasu lokutan ma ta kai ga sanadiyar mutuwa.

Wa Ke Cikin Barazana?

Jarirai sun fi barazanar kamuwa da cutar Maleriya ko kuma zazzabin cizon sauro A shekarar 2017, kusan rabin al’ummar duniya sun fuskanci barazanar kamuwa da maleriya.

Yara kanana ‘yan kasa da shekaru biyar su ne rukunni mutanen da cutar ta fi yi masu illa: a 2017, kashi 61 cikin 100 (266,000) na wadanda cutar ta yi ma illa a duniya yara ne. Sauran rukunin mutane da suka hada da mata masu wadanda suke da juna biyu da dai sauran rukunin mutane da garkuwar jikinsu babu karfi su suka fi barazanar kamuwa da cutar.

A Wadanne Yankuna Ne Cutar Ta Maleriya Tafi Kamari?

Maleriya ta fi illa a kasashen da suke kudu da hamadar sahara ne da kuma nahiyar Asiya Alkalumar WHO sun nuna cewa akasarin wadanda suke fama da cutar da cutar da kuma mace-macen ana samun su ne a kasashen kudu da hamadar saharar Afirka, sai dai yankunan kudu maso gabashin Asia da gabashin Mediterranean da yammacin Pacific da kuma Amurkawa su ma na cikin barazanar kamuwar.

A 2017 Kasashe Biyar Na Afirka Su Ke Dauke Da Kusan Rabin Masu Fama Da Cutar A Duniya: Nijeriya ( kasha 25), Jamhuriyar Demokradiyar Congo (kasha 11), Mozambikue (kasha 5), Indiya (kasha 4) da kuma Uganda mai ( kasha ).

Yadda Cutar Ta Ke Yaduwa:

Macen Sauro Ce Ta Yada Cutar Maleriya: A lokuta masu yawa cutar Maleriya na yaduwa ne ta hanyar cizon macen sauro da ake kira da suna Anopheles mosquitoes -akwai sama da jinsin sauron Anopheles 400, wanda kusan 30 ke yada ita cutar ta Maleriya.

Jinsin wadannan saurayen na cizo ne tsakanin dare zuwa asuba. Saurayen na nasa kwai a cikin ruwa, bayan nan kuma shi kwan ya kyankyashe kan sa sannu a hankali ya girma ya zama sauro; macen sauro na shan jini a matsayin abinci.

Rigakafin Cutar Zazzabin Cizon Sauro: A 2017, kusan rabin al’umma sun yi amfani da gidan sauro wajen kare kansu daga barazanar da maleriya ta ke haifarwa kamar dai yadda ita Hukumar lafiya ta duniya WHO ta bayyana. WHO ta bada shawarwarin kariya daga kamuwa da cutar da dabarun da take ganin su ne mafita.

Hanyoyin kariyar sun kasu gida biyu ne – da akwai amfani da gidan sauro da kuma feshin maganin sauro – wanda akasari aka fi yi a lokuta masu yawa. Bacci da gidan sauro na rage damar da sauro ke da ita na cizon mutum.

Feshin maganin kwari a gidaje da gine-gine, akalla sau daya ko biyu a shekara na taimakawa sosai. Ana iya kare kai daga cutar Maleriya ta hanyar shan magungunan rigakafi da ake kira anti-malarial drugs ga matafiya, mata masu junabiyu da kuma kananan yara. Gano ta da shan magani

Tarbar Maleriya Da Kuma Maganceta Da Wuri Na Kawo Sauki:

Maleriya cuta ce da ake iya shan magani kuma a warke – ana iya gane ta idan mutum na dauke da ita a cikin minti 30 ko kasa da haka ta hanyar gwajin jini. A cewar WHO, gano cutar a kan lokaci da shan magani na rage barazanar da take haifarwa, hana saurin kisa da kuma rage karfin yaduwarta.

Bijirewa Magunguna:

Abu ne mai muhimmaci a gwada jini a kai a kai domin kare kai daga cutar Maleriya WHO ta yi gargadi akan cewar sauron shine ke yada cutar maleriya na bijirewa magunguna feshi da na sha – wanda hakan barazana ce ga kokarin da ake na kawo karshen cutar maleriya. Abin damuwar a yanzu shi ne kokarinarin kariya da shawo kan cutar na neman daina aiki.

Sababbin alkaluman da suke kunshe a rahotan Maleriya na bana sun nuna cewar cikin kasashe 68 da aka ruwaito zazzabin cizon sauro na barazana, kashi 1 cikin 5 na amfani da magungunan rigakafi da ke nuna turjiya.

Turjiyar da magungunan yaki da wannan cutar ke nuna wa na sake zama kalubale. WHO ta ce akwai bukatarc da a sake daukar matakai masu karfi don ganin lallai an kawo karshen cutar baki daya. Hukumar na son ganin an bullo da wasu hanyoyin tunkarar turjiyar da magungunan Maleriya ke nunawa.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: