Connect with us

Uncategorized

Bakonmu Na Mako

Published

on

Bakon namu na wannan makon daya ne daga cikin hakiman masauratar Katsina, wato, Alhaji Idris Sule Idris, Makaman Katsina na biyar, Hakimin Bakori kuma Sarkin adon Sarkin Katsina.
Gabatarwa
Sunana Alhaji Idris Sule Idris Nadabo, Makaman Katsina, Sarkin adon Sarkin Katsina. Ni ne Makama na Biyar a jerin Makaman Katsina, kuma sarautar Makama ita ce, ta takwas a cikin jerin sarautun Katsina. An haife ni a garin Bakori, a shekara ta 1967. An nada ni Makaman Katsiana, Hakimin Bakori, bayan rasuwar mahifinmu a shekara ta 2007.
Na fara makarantar firamare a Sultan Bello da ke Kaduna, wanda daga nan kuma na zo na karasa karatuna a wata firamare da ke Funtuwa. Daga nan na samu nasarar zuwa Kwalejin Katsina a shekara ta 1984.
Bayan nan na tafi makarantar share fagen shiga jami’a da ke Zariya. Bayan kammala wannan makaranta sai na shiga Kaduna Poly inda na yi Dufuloma a fannin “Accounting”
Daga nan, bayan na gama wannan karatu nawa sai na fara aiki a karamar hukumar Bakori. Ban dade ina aiki a wannan karamar hukuma ba, na bari na koma jiha daga shekara ta 1991 zuwa shekara ta 1994. Daga nan kuma, sai likkafa ta yi gaba na koma aiki a karkashin gwamnatin tarayya.
Ana cikin haka ne Allah ya yi wa mahaifinmu rasuwa a shekara ta 2007, wanda kuma cikin ikon Allah aka nadani a matsayin Makaman Katsina, Hakimin Bakori, kuma kimanin shekara biyu da suka wuce aka sake kara min wani matsayin na Sarkin adon Sarkin Katsina, wanda a halin yanzu wadannan su ne matsayin da nake da su a masarautar Katsina.
kalubalen Rayuwa
Kamar yadda kowa ya sani, rayuwa cike take da kalubale iri-iri. Babban kalubalen da na fara fuskanta a rayuwata shi ne, na karatu. Lokacin da na fara karatu, ban samu wanda zai ban shawarwari ba, kan yadda zan tafiyar da karatuna tare da karfafa min gwiwa kan in zage damtse wajen ganin na samu nasarar cinye dukkan jarabawar da ake yi mana. Wannan ta sa na samu rauni wajen kasancewa a cikin sahun gaba na masu kokari, amma dai duk da haka, cikin ikon Allah daidai gwargwado, an yi karatun, kuma an samu nasara gwargwadon iko. Wannan nasarar kuma ita ce, muke cin albarkacinta har yanzu.
Sai kuma kalubale ba biyu shi ne, lokacin da Allah ya ba ni wannan matsayi, na yi amfani da wannan dama wajen ganin na hada kan dukkan ‘yan uwa da abokan arziki domin kowa ya bayar da irin gummowar da zai iya bayarwa don ganin an samu nasara wajen tafiyar da wannan mulki. Bisa hakan ne na samu nasarar hada-kan ma fi yawa, amma wasu daga ciki, har yanzu muna ta kokarin ganin sun fahimci wannan manufa ta hada-kai, kuma kullum ana kara samun ci gaba, duk da cewa ita sarauta ta gaji haka, domin kuwa matsayi ne wanda duk dan gado zai so ya samu, sai dai in Allah bai nufa ba, saboda haka wani idan bai samu ba zai nemi ya burtse, dole sai a hankali za a shawo kansa har ya fahimci cewa, Allah ke bayar da mulki ga wanda ya so, a kuma lokacin da ya so.
Haka kuma wani babban kalubalen shi ne, in na kalli irin nauyin iyalina da ‘yan uwana da sauran al’ummar da ya doru a kaina, kullum tunanina shi ne, ya zan yi in sauke wannan nauyi da ke kaina. Cikin ikon Allah bisa kyakkyawar niyya da taimakon Allah da kuma gudummowar da nake samu daga makusanta, nakan ji cewa, kullum ina samun gamsuwa bisa kokarin da nake yi na sauke wannan nauyi.
Nasarorin Rayuwa
Hakina ina kara godewa Allah bisa nasarorin da na samu a tsawon rayuwata, wanda kuma har yanzu nake fatan ci gaba da samun ire-iren wadannan nasarori.
Nasara ta farko shi ne, na samu nasarar yin karatun addini da na zamani gwagwadon hali, sannan kuma bayan kammala karatuna na yi aikin gwamnati a wurare daban-daban inda na samu gogewa sakamakon hulda da jama’a, cikin ikon Allah duk inda na yi aiki na zauna da jama’a lafiya mun rabu lafiya.
Sannan nasara ta biyu, ita ce, ta samun wannan sarauta ta Makama, akwai wadanda suka so wannan sarauta, amma cikin ikon Allah, ya zabe ni, ya ba ni wannan matsayi, saboda haka ina kara godewa, Allah bisa wannan matsayi da ya ba ni.
Wata babbar nasara da zan iya bugun kirji da ita, ita ce, ta cikakkiyar biyayyar da nake samu daga al’ummar karamar hukumar Bakori, wannan kuma ta sa aka samu zaman lafiya da tabbatar tsaro a dukkan fadin wannan karamar hukuma.
Al’umma sun amince, mu kasance masu yi musu sulhu a dukkan sabanin da aka samu a tsakaninsu. Saboda haka wannan na dada nuna irin yadda al’ummar ke biyayya ga wannan masarauta bisa gamsuwar da suke da ita na cewa, ana kwatanta yi musu adalci.
Baya dukkan wadannan abubuwa, tun daga hawana karagar wannan sarauta, an samu ci gaba sosai a wannan karamar hukuma, ta hanyar samun gine-gine da fadada harkokin kasuwanci da noma da samun baki wadanda suka kawo ci gaba da bunkasa rayuwar al’umma. Saboda haka, wanda ya san Bakori shekara kamar goma da ta wuce, yanzu idan ya zo ya ga irin ci gaban da aka samu zai yi matukar mamaki, an samu ci gaba da yalwar arziki.
Haka kuma na samu nasarar kawo kotun daukaka kara zuwa wannan gari na Bakori domin saukakewa, al’ummar wannan masarauta zuwa nesa idan suna son daukaka kara.
Shawarwari Ga Al’umma
Babbar shawarata ta farko ita, mu dage da yin addu’ar neman zaman lafiya, kuma mu ci gaba da kokarin tabbatar da zaman lafiyar a tsakaninmu, Saboda haka dukkan abin da muke ganin zai kawo mana sabanin zaman lafiya to mu nesanta kanmu da shi. Mu taimaki ‘yan uwanmu, yadda za su samu ci gaban rayuwarsu.
Haka kuma, ina kira ga matasa da babbar murya cewa, su nesanta kansu daga shaye-shayen miyagun kwayoyi, domin rayuwarsu ta yi kyau, su yi dukkan iya kokarainsu wajen neman ilimin addini da na zamani da kuma samun hanyanyoyin dogaro da kai, yadda za su taimaki kansu da sauran al’ummar kasa baki daya. Saboda haka, fatanmu a kullum shi ne a samu al’umma ta-gari, wadda za a yi alfari da ita.
Burina A Rayuwa
Babban burina shi ne, in gama lafiya, in samu tsira duniya da lahira, kuma zuri’armu ta zama wadda za ta amfani kanta da sauran al’umma baki daya.
Haka kuma, ina da burin in ga an samu dauwamammen zaman lafiya, a karamar hukumar Bakori da jihar Katsina da ma kasa baki daya.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: