Connect with us

TATTAUNAWA

Ina Bakin Cikin Ganin Talakawan Da Suka Zabe Mu Na Cikin Hali Na Kunci – Hon. Safana

Published

on

HONORABUL AHMAD DAYYABU SAFANA, shi ne dan majalisa mai wakiltar Batsari, Dan Musa da Safana a zauren majalisar wakilai ta tarayya. A wannan tattaunawar da ya yi da AL-AMIN CIROMA, Hon. Safana ya bayyana halin kunci da al’ummar Jihar Katsina ke ciki da hanyoyin warware matsalar tsaro a jihar da matakan da suka dace shugabanni da hukumomi su dauka. Ga hirar kamar haka:

Hon. Safana, bari mu fara wannan ganawa da tambaya kan harkar tsaro, yadda lamarin ya kara a kullum kara tabarbarewa yake. Kwana baya, mun shaidi yadda ‘yan bindiga suka shiga kauyuka a jiharka ta Katsina, suka kashe na kashewa, suka kuma yi awon gaba da wadanda suka ga dama. To, a matsayin na dan majalisar dake wakiltar wani bangare na jihar Katsina a majalisar wakilai ta kasa, shin ya kake kallon tabarbarewar harkar tsaro a Arewacin Nijeriya, musamman jiharku?

Da farko dai ina godiya ga Allah da ya ba ni ikon tattaunawa da kai, bisa ga wannan harka ta tsaro. Alal hakika wannan harka ta tsaro a yanzu ita ce babbar matsalar da Nijeriya ta ke fama da ita, musamman a nan arewacin kasa, a takaice kuma ina cewa idan ka ture maganar Boko Haram da ke Jihar Barno.

To harkar tsaro da sace – sace na mutane da daukar mata a tafi dasu da neman kudin fansa bayan an kama mutane babu kamar jahar Katsina, kuma a jahar Katsina ma, kananan hukumomin da nake wakilta a majalisar, wato Safana da Batsari da Dan Musa, kullum sai mun samu rahoton cewa an shiga wannan garin ko an saci mutane, ko an saci dabbobi ko an kwashi mata ko kuma an kashe wasu. Wannan al’amari ya na tada mana hankali kwarai da gaske ganin cewa su talakawan da muke wakilta ko kuma suka zabo mu zo mu zama wakilan su, sun shiga hali na kunci, wanda kai da kake wakiltar su ba ka iya yi musu magani.

Kuma abin nan ana cewa an gano bakin zaren, an gano bakin zaren, ni ban ga alamar an gano shi ba, saboda ko ba komai jami’’an tsaron nan dai gasu akwai, akwai sojoji, akwai ‘Yansanda akwai makamai a hannun su,  kullum ranar duniya sai an yi wannan abun, misalign da zan baka kwanaki biyu da suka wuce anje wani gari da ake kira Zakka garin Hakimi ne mutanen nan sunje da Babura da makamai.

Sannan kafin suje Kanoman karamar hukumar ya sami labarin cewa zasu je, ya sanar da shugaban sojoji na jahar ya kuma sanarda kwamishinan ‘yansanda kuma su a matsayin sun a shuwagabanni sunyi abin da ya kamata sun tura jami’an su, sun je garin amma abin mamaki da al’ajabi suna zaune a garin mintuna talatin ya rage barayin su zo garin, jami’an tsaro su ka tafiyar su.

Saboda haka mutanen suka shigo, suka bi gida-gida, suka bugi wasu, suka kasha dukiya, suka tafi da mata biyar, suka farfasawa wasu jiki, saboda haka ka ga irin wannan abu sai ya daure ma kai, saboda idan zasu zo kafin lokacin kuma an sanarda jami’an tsaro mutanen za su zo mi ya sa zasu tafi, kuma ya kasance bayan minti 30, sannan suka zo ga wannan abin ya na da daure kai matuka Kuma sau da yawa nasha fadi bamu taruwa mu zama daya, jami’an tsaron nan akwai na kirki akwai bata gari, sau da yawa zaka ji, an tura su wajen aikin, sai ka ga sun kama hanya, sai dai kafin su kai wajen da aka ce su je, sai su ja su tsaya, sai mutanen sun gama taaddancin su, sun tafi, sannan su je, saboda haka wannan harka tana tadamin hankali.

Ina son yin amfani da wannan damar in kara kira gare mu, mu shugabanni da Allah ya dorawa nauyi, a kara bin abin nan domin tantance gaskiya, saboda ko ba komai yanzu talakawan nan  ba su da kowa a duniya babu kuma mai iya taimakon su, gwara mu shuwaganni idan abu yayi zafi kana iya dauko ‘yan uwanka ko iyayen ka ka kai su wani wuri, shi talaka ba inda zai kai su. Yanzu idan kaje Safana suna nan wata Sakandare school an tara su, haka suke layi kamar almajirai ana dama musu koko da safe da rana a dafa musu shinkafa da dare a yi musu tuwo, haka suke a Batsari, haka suke a Danmusa, saboda haka wannan lamarin Ni bana cewa ba a komai, ana iyakar yi, amma dai sai an kara abinda ake yi bai isa ba.

Irin wadannan maganganu da ka bayyana a yanzu, ansha jin su, musamman ma wasannin kwaikwaayo da ake yi tsakanin jami’an tsaro ko shugabannin rundunoni tsaro da sauransu, inda za a ce nan an kawo rahoto wasu zasu zo su kawo hari, wasu harda hotuna. Shin a zauren majalisar ku da kuke wakiltar talakawan da kake fadin ba su da kowa sai irin ku, wasu irin abubuwa kuke dorawa akan teburi wanda zai sa a kira shugabanni musamman kamar mahukunta na kasa su tabbatar da cewa rayuwar al’umma a koda wane lokaci suna salwanta, me kuke yi saboda an sha irin wadannan maganganu amma al’amura sai ka ga gomma jiya i yau?

Kamar yadda ka sani ne Ciroma, dan majalisa abin da kawai yake iya yi ya kawo kuduri na alamarun dake damuwar alummar shi, daga karshe ku cimma wata yarjejeniya a majalisa, na sani a majalisar nan an sha kiran shugabannin tsaro na kasa a zauna da su kuma a gaya musu ga abubuwa da ake tuhumarsu  da sun a ma’aikatan su dake aikatawa, wanda ba bisa ka’ida yake ba. Kuma ba su yin abin da ya kamata kuma a gaya musu, suce za a gyara, sannan tsakaninmu da majalisar zartaswa iyaka ai abinda muka fahimta ne matsala zamu kawo kuma mu bada shawara, amma bamu da hakkin mu hukunta su.

Su jami’an tsaron nan saboda ba mu muka nada sub a, don haka gwargwadon hali in kana sauraran zauren majalisar tarayya kusan kullum aka je sai kaji wani ya kawo kuduri na harkar tsaro kuma daga

kowane bangaren kasan nan. Wannan shi ya jaza daga karshe ma aka tattara komai akai kwamiti, aka ce kwamitin nan ya kira dukkanin jami’an tsaron nan shuwagabannin su a tattauna majalolin nan da majalisa ta kawo. A nuna musu shi sannan suyi bayani kan mi ya sa haka ke faruwa.

Idan an yi wannan ya kare ko mun gamsu ko bamu gamsu ba abinda muke iya yi kawai shi ne mu sanar da fadar shugaban kasa cewa ga abubuwan da muka gano ga kuma shawarar da muka ba yar, idan mun tura idan anyi daidai in ba a yi ba bamu iya wani abu, bamu muka nada su, bamu iya sauke su, saboda haka. Amma abu mafi a’ala shi ne doka, misali idan ka lura mafi yawan abubuwan suna bukatar gyara a tsarin mulkin Nijeriyo kuma Allah ya sa wadanda suka shirya tsarin mulkin nan na kasan nan a 1999, sun yi shi a dukunkune yadda gyara shi ya na bayar da wahala domin sun baiwa wasu bangarori karfin iko da yawa wanda canza wannan ikon ya na bukatar canza tsarin mulkin. Sannan gyara wannan tsarin mulkin yana bukatar bin wasu matakai, wadannan matakan sunda wahala saboda sun shafi ‘yan majalisar dokoki na jahohi wanda muna bukatar samun kashi biyu bisa uku na ‘yan majalisar jahohin kasan nan 36, kafin mu iya yin wani gyaran a tsarin mulkin kasan nan.

Sau da yawa idan ana son yin wani gyaran bai kuwa yiwa gwamnonin jahohi dadi ba sai su hana ‘yan majalisar johihinsu yin wani abu idan kuma ba suyi ba, mu bamu da iznin gyara tsarin mulkin nan, saboda haka abubuwa ne sun dukunkune kuma gyaran su yana da wahala. Amma ni a nawa ra’ayi dan ilimin da na samu cikin harkar siyasa da kuma shaanin mulki tun da na yi shugaban karamar hukumar. Na yi dan majalisar jiha kuma yanzu ina majalisar tarayya, ni na san idan za a fitar da son zuciya a fito fili a goyawa wadannan masu aikinsa kai da aka ce an hanasu gudanar da aikinsu. Lalle za su iya maganin wannan matsalar.

Sai na biyu mutanen da suke gayyato baki don su ayi wannan ta’addancin   gindin lalatar, ‘yan gida ne, an san su, an san iyayen su, su barayin sai dai ace yau wane dan gidan wane ne ke sata wuri kaza, amma yanzu ya bar gida ya shiga daji. Idan da za a yarda  ni ra’ayi na wadannan dangin nasa a kamo su wajen hukumar sai su wadancan sun daina, sannan suma a sake su tunda na ga anyi ba day aba, ba biyu ba, kuma naga yayi amfani.

Malam Suleman wanda aka kama sai ya biya miliyan 300 da aka cewa sojoji sun kwato, nasan cewa ba sojoji suka kwato shi ba, domin wanda ya kamashi yana Karamar hukumar Dan Musa ne abin da aka yi zuwa a kai aka kama mahaifiyarsa shi Bahillacen tana Maidabino aka rike a wajen ‘yan sanda aka yi waya da shi, ya dauka wata Magana ce, aka ce masa to mahaifiyarka, na hannunmu idan ba ka sako Malam ba ita ma zamu kashe ta, shi ya zo ya kawo Malam din da kansu. To ashe ka ga idan gaskiya ne, mutanen nan an san su, kuma akwai hanyoyi da yawa da ake iya bi ayi maganin su ta hanyar wannan dubarar tunda sun san dadin ‘yan uwan su, sun san dadin jinin su, kuma iyayen su na nan mun sansu, kuma yanzu Safana na san wani Fulani dukkanin ‘ya’yansa barayi ne, sarakunan mu sun sani, jami’an tsaron mu sun sani to amma kullum lallashin sa ake.

To, amma a nan ba ka ganin idan ba an riga an kama mutum ba ne ya aikata laifi, akwai hatsari aje kawai ayi cune ace wane mun sanshi barawo ne?

Wato abin da nake so ka gane Malalm Ciroma, ba ka ce ba a kama shi ba, ai duk wanda kaji ance barawo ne a karkara, ai an san barawon ne, an taba kamashi, kuma an kamashi yana yin satar ne, amma wani tsarin ne na dokarmu wanda duk shi ke kawo mana wannan rudun, yake sa muna shiga wannan halin, ace barawon da ba a kama ba, sunan sa Muhammadu! Amma ga shi an san shi yana satar, kuma aikinsa ke nan, yanzu haka suna nan da yawa a karkararmu, Fulanin suna daji basa zama cikin gari, kuma ansan su suna zuwa cikin garuruwan da makamai, idan ka ga bahillaci misali da bindiga kirar ‘AK47’ ya shigo gari ya sayi wani abu, ka sani cewa barawo ne, mi zaiyi da ‘AK47’, farko ma shin wa ya bashi izinin rike da ‘AK47,’ idan ma ba barawo ba ne, me yake da ita? Abubuwan nan bayyana suke idan za a tashi tsaye a maganin wannan matsalar sai ayi domin kuwa wallahi tallahi za a iya maganin su.

 
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: