Connect with us

LABARAI

Shugaban NIS Ya Yi Ziyarar Aiki Ta Yini Daya A Kaduna

Published

on

Shugaban Hukumar Kula da Shige da Ficen kasa (NIS), Muhammad Babandede MFR, ya yi ziyarar aiki ta yini daya a ofishin hukumarsa na reshen Kaduna, a kokarinsa na tabbatar da dorewar nasarar da hukumar ke samu wurin zamanantar da ayyukanta.
Har ila yau, a yayin ziyarar, Babandede ya kuma ziyarci Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru el-Rufai, a fadar gwamnatin jihar ta Sir Kashim Ibrahim.
Shugaban na NIS, ya yaba wa Gwamna el-Rufai bisa goyon bayan da yake bai wa hukumarsa a jihar da kuma samar da kyakkyawan yanayi na gudanar da aikace-aikacenta wajen bunkasa hada-hadar kasuwanci a Kaduna da tabbatar da dorewar zaman lafiya.
A nashi bangaren, Gwamna el-Rufai ya taya Shugaban NIS, Muhammad Babandede murnar dimbin ci gaban da ya samar a cikin shekara uku kacal na shugabancinsa a NIS da kuma namijin kokarin da yake yi wajen tabbatar da kawo sauye-sauye masu ma’ana a hukumar.

Shugaban NIS Muhammad Babandede yayin da yake jawabi ga Gwamna Nasiru el-Rufai a fadar Sir Kashim Ibrahim

 

Ya nunar da cewa tasirin ayyukan da Babandede yake gudanarwa a NIS wajen habaka ci gaban kasar nan ba zai misaltu ba, musamman abin da ya shafi samar da sabon fasfo mai aiki na tsawon shekara 10, da yi wa baki rajista ta shafin Intanet da gine-ginen ofisoshin hukumar da samar da kayan aiki na zamani da sauransu.
Sanarwar da Shugaban na NIS, Muhammad Babandede ya fitar ga manema labarai ta hannun Jami’in yada labarai na hukumar, Sunday James, ta ce duka wadannan na zuwa ne a dai-dai lokacin da NIS ke murnar cika shekara 56 da kafuwa, wadda a karkashin haka aka gudanar da babban taron mahukuntan hukumar a Legas domin tsara daftarin ayyukanta a tsakanin 2019 zuwa 2023.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: