Connect with us

RA'AYI

Ya Zama Wajibi A Jinjina Wa Gwamna Baba Gana Zulum – Dakta Fatima Goni

Published

on

Kamar yadda yake a al’adar ‘yan siyasa musamman a Nijeriya, gwamnatoci aka matakai daban-daban kama daga kan Shugaban Shugaban Kasa, Gwamnoni da sauran ‘yan siyasa da suke riKe da madafun iko, akan samu su yi bikin cikarsu kwanaki 100 a kan kujerar mulki.

Biki ne da ko wane dan siyasa ke baje kolin ayyukan da ya aiwatar cikn wadan nan kwanaki 100 domin su zama zakaran gwajin dafi ga shekarun da zai shafe a mulkinsa idan Allah ya ba shi yawan rai, sannan kuma da nufin sake hangen zango na biyu a idan shekarar zabe ta zagayo.

Kamar haka ne al’ummar Jihar Maiduri yankin da ya sha fama da rashin kwanciyar hankali saboda hare-haren Kungiyar Boko Haram da aka shafe shekaru ana fama da shi. Wannan sauyin gwamnatin da aka samu KarKashin jagorancin Farfesa Baba Gana Umara Zulum ta zo sauyi mai ban al’ajabi, inda cikin kwanaki 100 da ta yi bisa kujerar mulki ta gudanar da ayyuka sama kwanakin da ta yi a karagar mulki kuma a zango na farko, kamar yadda al’ummar Jihar ke fadar albarkacin bakinsu.

Wakilin LEADERSHIP A Yau Juma’a  ya samu ganawa da daya daga cikin ‘yan asalin Jihar, wata hamshaKiyar ‘yan kasuwa kuma shaharriyar ‘yar siyasa, Sannan Shugabar Kungiyar Grassroots Mobilizers For Buhari & Osinbajo, kazalika Shugabar Gidauniyar nan da ke tallafa wa marayu zawarawa da marasa gata, Hajiya Dakta Gimbiya Fatima Muhammad Goni, da aka fi sani da Mama GMB, in da ta ce ai ita babu abin da za ta cewa wannan sabuwar gwamnatin sai ala san barka, domin a cewarta duk gwamnonin da suka kujerar mulki daga kan sabbin gwamnoni zuwa wadan da suka koma babu gwamnan da ya gudanar da ayyuka muhimmai kamar Mai Girma Gwamna Baba Gana Zulum.
Da aka tambaye ta ko menene dalilinta a fadin haka? Sai ta ce, dalilan a bayyane suke, kuma babu Karya balle Kage ko Karin gishiri, “ Sanin kowa ne duk wanda ya kwana ya tashi a Nijeriya, ba ma Nijeriya Afirka ko ma in ce maka duniya baki daya in da har yana sauraron kafofin yada labarai na cikin gida da na waje, to ya san irin tashin hankalin da Arewa maso Gabashin Kasar nan yake fama da shi musamman kuma a Jihar Borno, amma cikin yardar Allah da ikonsa yanzu abubuwa sun komawa daidai.

Ka ga ashe ya kamata ba ma ni kadai ba a ce duk wanda ke wannan Jiha ya yi jinjina ga Mai Girma Gwamna Baba Gana Zulum. Shi ne Gwamnan da farkon fara aikinsa ya fara ziyartar sakatariyar jihar don ya ga halin da ma’aikata ke ciki, ya samu suna nuna halin ko in kula da aikinsu, nan take ya ba da umarnin lallai kada ya sake dawowa ya samu irin wannan, don kowa ya shiga tatitayinsa kan aikin Gwamnati.

Aiki yake ba wai na zaman ofis kadai ba, idan an yi na ofis din sai kuma a fita waje a yi, sannan idan ya bayar da aikin  sai ya bi diddigi domin ganewa idanusa yadda abin yake tafiya. Haka kuma ake son Shugaba, ya zamto shi Shugaba ne kuma jagoran da zai kai al’ummarsa ga tudun mun tsira, kuma dama masu iya magana na cewa Juma’ar da za ta yi kyau tun daga Laraba ake gane ta.

Ko a ranar Talatar da ta gabata sai da Daraktan yada labarai na fadar Gwamnatin Jihar ya shaida wa manema labarai cewa, Mai Girma Gwamnan zai gina wata sabuwar Sakatariya ta a wajen gidan Gwamnatin Jiihar domin ya ci gaba da lura da yadda ma’akatansa ke gudanar da ayyukansu, sannan kuma wannan sabuwar Sakatariyar ita ce, za ta zama nan ne Kwamishinoni da manyan Sakatarori za su riKa halarta, kuma duk ya yi hakan ne domin a zaburar da su kan zage dantsensu kan aikinsu.

“ Rashin tsaro shi ne babbar matsalar da ke addabar yankin, domin sama da shekaru biyar al’ummar Borno sai dai su gani ko su ji labarin ana gudanar da bukukuwa ko wane iri ne a wasu wurare, amma a yau an wayi gari saboda zuwan wannan sabuwar gwamnati ana ta gudanar da bukukuwa ciki kuwa har da bikin babbar Sallar nan da ta gabata.

Ya yi ayyuka ciki da wajen Jihar baki daya kama daga kan babban birni zuwan Kananan hukumomi, da suka hada da ziyarori Kaddamar da ayyuka da kuma bude su, ziyarar wuraren da wannan rikici ya rutsa da su da sauran ayyuka muhimmai a garuruwa dabandaban.

Yankuna Rewacin Jihar Borno sun fa’idantu da wadannan muhimman ayyuka, ka ga kenan ba magana ta tsaya ana ta bayanin yadda al’amura suka kasance ba, domin duk wanda ya san irin yadda Jihar take wajen rashin kwanciyar hankali a da can yanzu idan ya je sai ya ga banbanci sosai, tsaro ya fara kankama manoma suna ta ayyukansu ba tare da tsangwama ko tunanin kai masu hari ba.

Da aka tambaye ta ko yaya za ta kwataanta kamun ludan wannan gwamnati da waccan?

Sai ta ce, ko wacce Gwamnati da irin nata tsarin, amma dai muna magana ne kan nasarorin da wannan gwamnatin ta fara samu cikin kwanaki 100, wadda kamar yadda na fada a baya babu wata gwamnatin Jihar da a yanzu ta zo abin mamaki na gani da ido kamarta. Muna godiya da jinjina ga Mai Girma Gwamna Farfesa Baba Gana Umara Zulum, da fatan yadda aka fara lafiya da nasara Allah ya sa a gama lafiya cikin nasarori amin.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: