Connect with us

LABARAI

Jami’an Karbar Kudaden Shiga Na Samun Goyon Baya A Giwa—Girgije

Published

on

Shugaban kwamitin kula da tattara kudaden shiga na karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna, Sulaiman Ahmad Girgije ya bayyana cewa, jami’an da ke karbar kudaden shiga na samun cikakken goyon baya daga dukkan ‘yan kasuwar da ke gudanar da kasuwanci a karamar hukumar ta Giwa wajen biyan kudaden da suka kamata ba tare da sai an kai ruwa rana ba.
Ya ci ‘yan kasuwar sun san muhimmancin bayar da kudin shigar domin kuwa sun fahimci cewa, da irin wadannan kuade ne ake gudanar da ayyukan raya kasa da gina abubuwar ci gaban rayuwae al’umma.
Shugaban ya ce, gwamnatin jihar Kaduna na matukar kokarin ganin ta cika alkawarun da ta yi wa jama’a musamman lokacin da take yakin neman zabe. Haka kuma ya ce, a karamar hukumar Giwa gwamnatin ta samu nasarar tabbatar da hadin al’umma da kuma bunkasa nomad a harkokin kasuwanci.
Girgijen ya kara da cewa, karamar hukumar Giwa na alfari da samun shugabanni na-gari wadanda hakan ta sa suka samu ci gaban da ake gani a halin yanzu.
Ya ce, matasa da mata na daga cikin wadanda za su shaida samun wannan nasara domin kuwa da yawa daga cikinsu sun samu hanyoyin doro da kai da kara fadada iliminsu.
Saboda haka a karshe sai ya yi kira da babbar murya ga al’ummar karamar hukumar Giwa das u ci gaba da zama tsintsiya madaurinki daya ta hanyar bai wa gwamnatin karamar hukuma da ta jihad a ma tarayya cikakken goyon baya domin samun nasarar aiwatar da aikace-aikacen ci gabanta.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: