Connect with us

Nahiyar Afirka

Yau Ake Zaben Shugaban Kasa A Kasar Tunusiya

Published

on

A yau Lahadi ne al’ummar kasar Tunusiya ke gudanar da zaben sabon shugaban kasar. Sama da mutum milyan 7 ne suka cancanci kada kuri’unsu a zaben shugabancin kasa da ake gudanarwar din.

Mutum 24 ne ke takara domin maye gurbin shugaba Caid Essebsi wanda ya rasu a cikin watan yulin da ya gabata.

An tsara bude rumfunan zabe da misalin karfe 8 na safe kafin a rufe a 6 na yamma domin bai wa jama’a damar kada kuri’unsu a wannan zabe mai cike da tarihi, lura da cewa Tunisia, ita ce kasar Larabawa ta farko da aka samu barkewar bore a shekara 2011 sannan aka gudanar da zabe irin na dimokuradiyya a cikinta.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: