Connect with us

LABARAI

Asibitin Gwamnatin Tarayya Dake Keffi Ya Nemi Hadin Kan Kafafen Watsa Labarai

Published

on

Dr.  Yahaya Adamu, Babban Daraktan asibitin gwamnatin tarayya dake Keffin jihar Nasarawa, ya nemi hadin kan kafafen watsa labarai domin ganin an yi wani tsari da za su rika yada ayyukan asibitin ga al’umma.

Adamu ya yi wannan kiran ne a ranar Litinin a yayin da yake karbar bakuncin membobin Progressives Chapel, a karkashin kungiyar ‘yan Jarida ta NUJ a ofishinsu dake Keffi. Ya shawarci kafafen watsa labaran da su tabbata sun rika yada labarai cikin adalci ga kowa don gudun ka da su rika sauya hakikanin abin da ke faruwa a asibitin.

Ya ce; ba yadda za a yi su yi aiki cikin nasara ba tare da sun yi aiki da ‘yan jaridar ba. Ya ce za su ci gaba da kasance abokan juna, kuma za su kare wannan huldar da ke tsakaninsu da kafafen watsa labaran.

Ya jinjinawa gwamnatin Nasarawa bisa ba da fili mai girman Hekta 23.8 domin gina mazaunain dindindin na cibiyar. Ya bayyana tsohon gwamnan, Sanata Tanko Almakura a matsayin wanda ya amince da ba da wannan filin.

Sai dai Adamu ya karyata rahoton dake cewa sun kara kudin da suke karba a asibitin daga naira dubu 30 zuwa 60. Ya ce; sam ba su kara ba, a don haka al’umma su yi watsi da wannan jita-jitar.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: