Connect with us

SOYAYYA

Higar So A Cikin Zuciya

Published

on

Assalamu alaikum, LEADERSHIP A YAU Asabar. hakika na yi farin ciki da kirkirar wannan shafi na musamman domin masoya tare da isar da sakon da muke son isarwa ga ‘yan’uwa masu gudanar da soyayya. Muna muku addu’ar Allah ya kara muku hikima da basirar aiki da kuma bunkasar wannan jarida mai farin jini baki daya. A yau ina son in yi wa masoya bayanin yadda so yake shiga cikin zuciya.
So yana shiga a cikin zuciyar mutum ne a lokacin da bai yi zaton faruwar hakan ba, ta hanyar kallo ko jin muryar wanin da ya ji. Lokacin da saurayi ya hadu da budurwa a zahiri, to idan har ya kalle ta ya yaba, zai iya jin ta shiga masa rai.A nan take zai iya jin yana sonta, har ma idan son nata ya shige shi da karfi, ba zai iya hakura ba har sai ya tunkare ta don sanar da ita.Haka nan kuma idan son ya shige shi a lokacin, amma bai yi karfin da har ya kasa daurewa ya barta ba tare da ya furta mata ba. To idan ya koma gida, ko ya isa wani guri da zai zauna ya iya yin tunani, to zai iya shiga kogin tunanin ta kawai.Haka nan kuma idan saurayi ya ji muryar wata budurwa, iya jin muryar tata kawai da zai yi ma zai iya jin yana sonta. Don haka zai iya bin hanyoyin da za su hadu a cikin sauki ta yadda zai kulla soyayya da ita.Sai dai a zuciyarsa zai yi tunanin kalarta da kamanninta da yadda tsarin halittar jikinta yake. Ba zai taba sanin hakan ba sai idan sun hadu ido da ido. To da zarar sun hadu ya same ta kyakkyawa, kuma mai cikakkiyar halitta, sai ya kara jin son ta ya kara shigar masa cikin rai.Don haka shi so babu wanda zai iya tsayar da shi zarar ya shiga cikin zuciyar dan’adam. Lallai shi so yana iya shiga cikin zuciyar mutum lokaci daya, amma kuma ba ya iya fita nan take.
Sakon soyayya daga masoyinku Mahmud Sani, KD
08151693170

Abubuwan Da Ke Sa Soyayya Ta Rushe
Assalamu alaikum, LEADERSHIP A YAU Asabar. hakika na yi farin ciki da kirkiran wannan shafi na musamman domin masoya tare da isar da sakon da muke son isarwa ga ‘yan’uwa masu gudanar da soyayya. Muna muku addu’ar Allah ya kara muku hikima da basirar aiki da kuma bunkasar wannan jarida mai farin jini baki daya. A matsiyana na masoyin masu karatu, ina so in yi bayani a kan wadansu abubuwa da ke sa soyayya ta rushe a tsakanin masoya.
Zaman soyayya sai da hakuri dole kuma a samu kyakkyawar fahimta a tsakanin juna. Kowa mai laifi ne, saboda haka sai an rika hakuri da juna. Karamar matsala ka iya kawo rabuwar dangantakar da aka dade ana fama.Idan aka samu irin haka, to dole a tsaya a duba a ga inda barakan ta ke domin a gyara.Kowa sai ya duba ya ga inda ya samu sakaci, sai ya yi kokarin gyarawa. Idan ba ka san matakin da za ka dauka ba, ga kadan daga cikin wasu abubuwan da ke kawo matsala a cikin soyayya:

-Zaman takaici na cikin abinda ke warware dangantaka, an san da cewa ba shi yiwuwa ace kodayaushe za a kasance tare cikin raha. Amma kuma ba a son a kyale juna na dogon lokaci. Idan kana daukan dogon lokaci ka manta da abokin zamanka, sai a gyara. Wata rana kwatsam sai ku dan fita shakatawa, don shan iska.
-Idan mutum ya samu canji a wurin aiki ko ma wurin aikin gaba daya, dabi’unsa duk za su canza. Lokacin dawowa aikin sa zai canza, ba kamar yadda aka saba ba. Dole sai mutum ya rika bayanin abon da ke faruwa ga masoyinsa. Gudun zargi da sauran su.
-Muddin har ba ka da sha’awar ko biyar da sha’awar danuwanka, to abu ya baci. Gamsar da abokin zama na cikin jiga-jigan zama. Idan danuwa ko yaruwar ki (ko ka) bai da sha’awa gare ka/ki, sai ki nemi yadda za kiyi domin shawo kan wannan matsala ta kowace irin dabara za ayi.
-Akwai lokacin da mutum zai shiga wasu harkokin ya ma mance gaba daya da aboki/abokiyar zamansa. Misali mutum na tsakiyar karatu zai rubuta jarabawa, ko kuma fama da rashin lafiya, sai ka ga mutum ya rasa lokacin da za su tattauna da junansu. To, tun wuri gara mutum ya gyara, ba sai kagama rubuta jarabawarka, alhali babu wanda zai taya ka murna.
-dan’adam bai san a rika yawan damunsa, ana kushe sa a kodayaushe. Ko da mutum bai yi dai-dai ba, akwai yadda ake magana ba tare da an bata wa mutum rai ba. Magana cikin hikima ya kan sa mutum ya gyara kuskuransa. Yana da kyau masoya su kasance masu yi wa junansu magana mai taushi idan suka yi kuskure.

Sakon soyayyaDaga Mammam Barista, Kaduna.

08078497517
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: