Connect with us

NISHADI

Tarihin Mawaqi DJ Abba A Taqaice

Published

on

Haruna Abdullahi (wanda aka fi sani da DJ AB) mawaqin waqoqin gambarar Hausa ta zamani ne. An haifeshi a garin Kaduna dake jihar Kaduna a watan Disamba na shekarar 1993. Ya yi makarantar firamare da sakandare a kwalejin gwamnatin tarayya (FGC) da ke Malali a Kaduna, yanzu haka yana kuma zuwa Jami’ar Ahmadu Bello da ke garin Zariya, inda yake karantar Quantity Survey (QS) yana aji na 4.
Abba ya fara waqoqin gambarar Hausa ta zamani (Hausa HipHop) a cikin qungiyarsu ta Yaran North Side kafin ya fara haxin gwiwa da wasu mawakan na Arewa kamar irin su BOC Madaki, Deezel, Classiq Morell da sauran fitattun mawaqan Hausa Hip Hop a Arewacin Nijeriya. Ya haura har wasu jihohin in da ya haxa gwiwa da wasu mawaqan na Nijeriya a kudancin qasar don waqoqi daban-daban.
DJ Abba ya yi waqoqi masu ximbin yawa da suka yi tashe a faxin Arewacin Nijeriya da ma gefenta a wasu qasashen kamar Nijar, Kamaru da Ghana. Yana da masu saurare da yawa musamman a qafafen Intanet daga qasashen turai da ma Amurika. A shekarar 2019 qungiyar Mr. Eazi wacce aka fi sani da Empawa suka zave shi cikin mutane 100 da suka can-canci a tallafa masu da kuxi ko wanne da dala dubu uku wanda za’ayi amfani da kuxin wajen yi ma waxannan mawaqa guda 100 bidiyo a faxin Afrika.

Ga Wasu kaxan daga cikin waqoqinsa da suka shahara a faxin duniya:
1. Girma : tare da Deezel da Classiq
2. Ga ni
3. Yi Rawa : tare da Young6ix
4. Kumatu
5. ‘Yar Boko
6. Babarsa
7. Totally
8. Gan Gan
9. Babban Yaya
10. My Woman
11. Soyayya
12 Su baaba ne
13. Tell Me : tare Sals Fateetee
14. A Zuba shi
15. An zo wajen
16. Bomba man
17. Da ban ne
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: