Connect with us

WASIKU

Yadda Rayuwar ‘Yan Mata Ke Gudana A Sansanin Yan Gudun Hijira

Published

on

Falmata yarinya ce yar kimanin shekara 14, wadda ke zaune a sansanin gudun hijira a jihar Borno. Falmata, wadda ta tsinci kan ta cikin mawuyacin halin ni’yasu; a lokacin da mayakan kungiyar Boko Haram suka taba sace ta daga gidan su, wanda sai bayan shekaru uku ta samu kanta- tare da yi mata fyade ba adadi.

Falmata, tayi sa’ar gudowa daga hannun mayakan, a daidai lokacin da suke sharara munshari, yayin da tayi ta watan-garereniya a cikin kungurmin dokar dajin da ke makwabtaka da dajin Sambisa. Kwatsam, sai ga ta a sansanin yan gudun hijira, a matsayin wadda matsalar tsaro ta sauya wa rayuwa. Falmata ta ce, wata rana tana kwance a tantin su, sai ta ji motsin takon wani jami’n tsaro ya tunkaro ta wanda kan ka ce kwabo ya kutsa kai cikin tantin tare da cewa ta tashi ta fito waje- ba da wata gardama ba ta fito wajen.

Ta ce, sai yallabam ya dauke ta zuwa dakin sa tare da yi mata fyade. Ta ce, kuma bayan awa hudu da dawowar ta, sai ga wani ogan shima ya zo, wajen ta wanda shima ya sake sungumar ta zuwa dakin sa tare da yi mata fyade.

“A wannan daren kadai, a haka wadannan jami’an tsaro suka yi ta sukuwa a kai na suna yi mini fyade; daya bayan daya, kuma ga halama wani bai san wani ya zo waje na ba.” Inji Falmata.

Bugu da kari kuma, wata rana, cikin sulusainin dare Falmata ta farka daga bacci; bayan da ta tabbatar cewa kafa ta dauke a sansanin. Ta tashi a hankali; nan take sai ta ce, kafa me na ci ban baki ba, ta rinka gudu har Allah ya kai ta wani kauye wanda a nan ta ci karo da wata tsohuwa, wadda ta taimaka mata wajen nuna mata hanyar kubuta. Wanda a cikin wannan halin, sai ga jami’an tsaron soja, inda suka taimake ta wajen dauko ta zuwa matsugunin yan gudun hijirar Dalori.

A haka Falmata ta tsira da ranta- duk da har yanzu ana iya cewa an gudu ba a tsira ba. Nan ma dai ta sake tsunduma cikin taskun tsohon turken ta mai cabo da ta guje wa. Duk da a wannan karon ta samu cikakkiyar kulawar wasu masu tausayi, ba kamar a baya ba.

Ta ce a matsayin ta na wadda ta gudo daga mayakan Boko Haram, babu ko sisin-kwabo kuma ba ta san inda zata ba, saboda bata san kowa ba a cikin birnin Maiduguri, kuma ga halama har yanzu tsugunne bai kare ba. Ta nemi a bata dama ta fita waje domin zuwa kasuwa- wajen masu kula da sansanin.

Wata karamar yarinya yar shekaru 13 ta bayyana wa jaridar New-York Times cewa sau tari ami’an tsaro a Maiduguri kan zo su dauke ta zuwa wajen baccin su. Yayin da ta ce, an yi mata fyade har sau 10 a cikin wannan shekarar; a matsugunin yan gudun hijira da ta ke zaune, kafin gudun tsira da mutuncin ta. Ta sake nanata cewa, wasu daga cikin su sun girmi sa’anin baban ta.

Bugu da kari kuma, a matsugunin yan gudun hijira na Teachers Billage, nan ma labarin bai canja ba, yayin da mazauna sansanin suka koka dangane da yadda wasu jam’an tsaron ke aikata masha’a da kananan yara yan matan da rikicin Boko Haram ya tilasta musu zama yan gudun hijira, da sunan dafa musu abinci.

Hadiza tana daya daga cikin wadanda suka tsinci kan a lamarin, ta ce “da farko, babu daya daga cikin mu da yake tunanin fadawa cikin wannan halin. Amma a cikin bakin ciki, labarin ya canja a lokacin rayuwar mu a sansanin gudun hijira, kuma duk macen da ke dafawa wadannan mutanen abinci sai sun yi mata fyade.” Inji ta.

Hadiza ta sake tabbatar da cewa, bayan yan makonni da zaman ta a matsugunin ne sai aka dauke ta zuwa dafa abinci a dakin wani jami’in tsaron.

Ta ce, daga baya aka bata aikin kai wa wasu jami’an tsaro hudu ruwa zuwa dakunan su. Haka abin ya ci gaba da gudana, har mutum daya ya rage. Yayin da wata rana, ya tilasta mata shiga wani daki inda y yi mata fyade.

Kana kuma ta bayyana yadda ta ji rauni a dalilin wannan ta’asar, kuma ta ji tsoron zuwa asibiti domin gudun kar asirin ofisan da ya yi mata fyade ya tonu, wanda hakan na iya barazana ga rayuwar ta. Ta ce, a haka ta ci gaba da boye raunin cikin makonni, amma duk da haka jami’in tsaro bai hakura ba; yayin da ya sake yi mata fyade da karfin tuwo. Hadiza ta bayyana cewa an yi mata fyade daidai har sau 20 a sansanin da take zaune.

“Da zaran sun kyallara ido, sun gan ki budurwa ko kina da jini a jika, to sai sun yi lalata da ke, ko ta halin kaka. Kuma zai yi wahala daga fitowar rana zuwa faduwa ta shude ba tare da sun aikata masha’a da ke ba.” Ta bakin Hadiza.

Daga baya, Allah ya tarfa wa garin Malama Hadiza nono, inda yan uwan ta suka ci karo da ita, a lokacin da labarin yadda ake samun yawaitar yiwa yara fyade a sansanin gudun hijira na Teachers Billage ya bazu.

A baya, gwamnatin tarayyar Nijeriya ta sha daukar alkawarin bin kadun wadannan zarge-zarge na matsalolin fyade a matsugunan yan gudun hijira da wannan rikici ya raba su da muhallan su tare da karin bayanin cewa “wadannan labarai ne maras dadin ji wadanda kuma bai kamata a bar su ba tare da bincike ba”. Amma kuma har yanzu wannan matsala ta fyaden ba ta kau ba.

Har wa yau, a shekaru biyu da suka gabata, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umurnin binciko yadda wannan al’amari na fyade ke ci gaba da yaduwa a matsugunan, matakin ya zo bayan wani rahoto da kungiyar kare hakkin bil adama (Human Rights Watch) ta fitar wanda ya tabbatar da yadda matsalar ke ci gaba da kassara rayuwar kananan yara mata, ta dalilan fyade da cin zarafin mata daban-daban. Shugaban kasa ya bayar da umurnin daukar kwararan matakan magance wannan matsalar.

Bisa ga wannan ne ma ya jawo aka dauki mataki wajen horas da jam’ian tsaro na musamman bisa wannan bukatar, a ciki an horas da jami’an tsaro mata 100 tare da girke su a sansanonin yan gudun hijira daban-daban. Kuma matakin ya rage kaifin wannan matsalar, kamar yadda wani bincike ya tabbatar.

Ofishin jakadancin Amurika ya sha kwarmata yadda jami’an tsaron yan-sanda sun sha kama mutane masu kekasasshiyar zuciya, da dama wadanda ake zargi da yiwa mata fyade da cin zarafi mai dangantaka da fyaden. Bayanin ya jaddada cewa a cikin watan Disamban da ya wuce, a cikin wadanda aka damken, akwai jami’an yan-sanda 2 da ma’aikacin gidan yari daya. Sauran sun hada da yan kato-da-gora, ma’aikatan gwamnati tare da sojoji guda uku.

Amma a cikin wani bayani da ta fitar a shekarun da suka gabata, cibiyar ‘Army Special Board of Inkuiry’ ta bayyana cewa zargin da ake yiwa jami’an ta ba gaskiya bane, saboda binciken ta ya tabbatar mata kan cewa wadannan zarge-zargen basu da tushe bakle madogara. A gefe guda kuma, mai magana da yawun rundunar yan-sandan Nijeriya ta kasa- Jimoh Moshood, kan cewa suna kan gudanar da bincike a kan zargin.

Mista Mausi Segun, babban Daraktan hukumar kare hakkin bil adama na yankin Afrika, ya bayyana cewa, an samu ci gaba kadan dangane da umurnin da shugaban kasa ya bayar wajen yiwa wannan bangare na al’umma adalci. “akwai jan kafa bisa ga lamurran da suka shafi kare martabar dan adamtakar yan gudun hijira, wadanda kuma rayuwar su take cikin kunci”.

Ko a baya ma sai da wasu daga cikin yan gudun hijira suka shaida wa kungiyar Amnesty International, kan cewa, sai ta hanyar sayar da kawunan su suke samun abincin da zasu ci a kowace rana, idan kuma ba ta wannan ba, to dole su bayar da kan su ga jami’an tsaron ko yan sintiri sannan su samu abincin da zasu ci.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: