Connect with us

RAHOTANNI

An Bude Taron Tuna Wa Da Narambada A Jami’ar Bayero

Published

on

A jiya Litinin, 16 ga Satumba, 2019, ne a ka bude taron tunawa da mashahurin mawakin nan Marigayi Ibrahim Narambada Tubali a harabar jami’ar Bayero da ke Kano.

An bude dakin taron ne da misalin karfe 10:00 na safe a lokacin da manyan baki su ka fara isowa.

An bude taron ne da taken Najeriya , inda bayan nan a ka gudanar da addu’a, sannan kuma dakartan cibiyar jami’ar ta bincike (CRNLT&F), Farfesa Aliyu Mu’azu, ya yi jawabin maraba, inda ya gode wa mahalarta taron, musamman manyan bakin da su ka samu halarta da kansu ko su ka turo wakilci, kamar tsohon shugaban kasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, Minstan Ilimi, Malam Adamu Adamu, Shugaban Majalisar Malamai ta Kasa reshen jihar Kano, Sheikh Ibrahim Khalil, da sauransu.

Haka nan, ya kuma yi maraba da Babban Mai Gabatar da Kasida a wajen taron, wato Farfesa Aliyu Muhammad Bunza, wanda ya gabatar da takardarsa mai taken ‘Wane Ne Narambada?’

Gabadayan wadannan manyan mutane, Farfesa Mu’azu ya jaddada cewa, cancantarsu da dangantakarsu da taron ko kuma wakokin shi kansa Narambadan, inda ya bayar da misali da cewa, baya ga kasancewar sunansiu daya da Janar Ibrahim Babangida, bugu da kari, a kullum tsohon shugaban kasar ya kan saurari wakokin na Narambadan ko a lokacin da ya ke kan kujerar mulkin kasar.

Ya ce, Farfesa Bunza kuma shi ne shehin malamin da ya fayyace kuma ya fito da hakikanin ko wane ne Mawaki Narambada, sabanin yadda a baya ba a samu yin hakan ba yadda ya kamata, duk da irin dimbin baiwar da ya ke da ita.

Shi kuwa Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu, a sakon takardar da ya aiko ya yi matukar yaba wa jami’ar ta Bayero ne bisa wannan namijin kokari da ta ke yi na zakulo ayyukan masu fasaha ta na nuna wa duniya su, domin bunkasar harshen Hausa.

Taron dai na kwana biyu ne daga jiya Litinin zuwa yau Talata, inda za a bajekolin rayuwar Makadi Narambada, fasaharsa da gudunmawarsa ga adabin Hausa. Masana da dama ne su ka gabatar da kasidu a taron.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: