Connect with us

LABARAI

Hatsarin Mota Ya Cinye Iyali Guda A Nasarawa

Published

on

Wani mutum mai suna Tarvershima Jebe dan asalin jihar Binuwe a ranar Lahadi ya rasa matarsa da ‘ya’yansa uku a wani hatsarin mota da ya auku a Ciyawa a karamar hukumar Eggon dake jihar Nasarawa a hanyarsu ta zuwa birnin Makurdi daga Abuja.

Tarvershima Jebe ya rasa matarsa da ‘ya’yansa mata biyu da namiji daya cikin mutum 13 da suka rasu a hatsari tsakanin mota mallakin Kamfanin zirga-zirga na Binuwe inda a ciki ne mamatan suke.

Daya daga makusantan iyalin, ya shaidawa majiyarmu cewa; mutumin ya rasa komai na sa sakamakon hatsarin, domin su ke nan iyalan na sa. Inda ya tabbatar da cewa a ranar Larabar makon nan za a bizne mamatan.

Haka zalika gwamnan jihar, Samuel Ortom ya mika ta’aziyyarsa ga iyalai bisa wannan rashi da aka yi sakamakon hatsarin. Ortom ya bayyan rashin a matsayin wani abin bakin ciki ga kaftanin jihar.  Zirga-

Gwamnan ya umurci ma’aikatar ayyuka da zirga-zirga da su hada hannu da hukumar kiyaye hadurra wato FRSC da hukumar BLNL wanda da motarsu aka yi hatsarin da su tabbata wadanda suka rayu an kula da su. Sannan a kwashe wadanda suka rasa rayukansu a kai su zuwa Mutuware kafin a rufe su.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: