Connect with us

TARIHI

Rayuwan Sayyadina Abubakar Da Ayyukansa Na Yaxa Addinin Musulunci (III)

Published

on

Cigaba daga inda muka tsaya a makon jiya.

 

Daga cikin siffofin jagorancin da Sayyadina Abubakar Radiyallahu Anhu yake da su, akwai zurfin nazari da hangen nesa, waxanda ya same su saboda tsawon daxewa tare da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Duba yadda su kayi da Sayyadina Umar ranar Hudaibiyah, ranar da mushrikai suka hana su shiga garinsu na asali, wato Makka, wanda suka nufa don su girmama xakin Allah, su yi Umrah sannan su koma wurin hijirarsu. A wannan ranar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya hangi wani abin da sauran Musulmai ba su hanga ba, wanda ya sa ya ce, a yau duk sharaxin da suka ba ni zan karba. Daga karshe mushrikai suka nemi Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya kwance haramarsa, ga shi kuwa yana dab da shiga garin Makka. Suka ce, sai ya koma har bayan shekara xaya za su yi masa izinin sake dawowa. Suka kuma dora masa alhakin mayar da duk wanda ya musulunta daga ranar nan idan ya yi hijira, a yayin da suka sharxanta ma kansu in wani ya yi ridda ya baro Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ba za su mayar da shi ba. Duk dai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce ya yarda. A nan ne Musulmai suka xaure fuska, Sayyadina Umar Radiyallahu Anhu kuwa yazo wajen Sayyadina Abubakar Radiyallahu Anhu yana so ya yi masa tambaya. Sayyadina Abubakar ya ce, bismillah! Sayyadina Umar Radiyallahu Anhu ya ce, ashe ba mu muke a kan gaskiya ba, su suke a kan karya ba? Sayyadina Abubakar Radiyallahu Anhu ya ce, haka ne. Ashe Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama bai gaya mana Allah ya yi alkawarin za mu shiga Masallaci mai alfarma ba? Ya ce, haka ne. To, don me za mu xauki wulakanci a addininmu?

A nan ne Sayyadina Abubakar Radiyallahu Anhu ya ce masa, shin ka san cewa shi Manzon Allah ne? Sayyadina Umar ya ce, eh. Ya ce, to, zai sava masa ne? Yace, a’a. Ya ce, to, da ya ce Allah ya yi mana alkawarin shiga Makka ya gaya maka cewa a wannan shekarar ne? ya ce, a’a. Ya ce, to, ka jira Allah zai cika ma Manzonsa alkawarin da ya yi masa, kuma ba zai tava tozarta shi ba. Mu lura da irin nazarinsa da hangen nesa da karfin imaninsa da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Wannan shi ya sa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya fi karkata ga ra’ayinsa idan aka zo wajen shawara kamar yadda ya faru bayan yakin Badar game da fursunonin da aka kama, Sayyadina Umar Radiyallahu Anhu yana ganin a kashe su a huta, a yayin da shi kuma Sayyadina Abubakar Radiyallahu Anhu yake ganin a fanshe su don a kyautata ma zumunta, a nemi qarin karfi da kudin fansar, a kuma yi fatar su shiriya a dalilin afuwar da aka yi mu su. Sai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya bi shawarar Sayyadina Abubakar Radiyallahu Anhu. (Sahihul Bukhari, Littafin Jihadi, Babin sharaxi awajen jihadi, Hadisi na 2529 da kuma Sahihu Muslim, Littafin yaqoqi, Babin Sulhun Hudaibiyah, Hadisi na 3338).

Tun kafin wafatin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya bayyana ma Musulmai sha’awarsa ga khalifantar da Sayyadina Abubakar Radiyallahu Anhu a madadinsa. Ga shi dai shi ne Amirul Hajji guda xaya da aka tava yi a zamanin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama, ga shi kuma ya umurce shi da ba da Sallah. Wasu mutane kuma sun nemi Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya faxa musu in da za su kai Zakkarsu a bayan rayuwarsa, sai ya ce, su kai ma Abubakar. A yayin da ya yi ma wata macce hukunci kuwa, ya ce mata, ki dawo lokaci kaza, sai ta ce, to in ban tarar da kai ba fa? Tana nufin in rai ya yi halinsa. Sai Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce ma ta, sai kije ki samu Abubakar. (Sahihul Bukhari, Kitabu Fada’ilis Sahabah, Babin faxar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama: “Lau kuntu muttakhidhan..” Hadisi na 3659. Da kuma Sahihu Muslim, Kitabu Fada’ilis Sahabah, Hadisi na 2386).

To, in ko har ya kasance Sayyadina Abubakar Radiyallahu Anhu shi zai jagoranci Sallah da Hajji da sha’anin Zakkah, kuma ya yanke hukunci a tsakanin mutane to, ina wani shugaba in ba shi ba?

Wani lokacin ma Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya kan yi umurni da a kira masa Sayyadina Abubakar Radiyallahu Anhu da iyalansa don ya ba da wasicci gare su amma kuma sai ya fasa yana mai qarawa da cewa, Allah ba zai bari a kauce ma Abubakar ba, Musulmai ma kuma ba za suyi hakan ba. Lokaci na karshe da haka ta faru shi ne a daren juma’arsa ta karshe a duniya, in da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce, a kawo masa takarda zai sa a rubuta alkawari wanda zai hana savani, amma sai Sayyidina Umar Radiyallahu Anhu ya ce, kar ku matsa ma Manzon Allah, ga littafin Allah a gabanmu, me kuke nema daga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama? Ai zafin ciwon da yake fama da shi ya ishe shi. Da aka soma maganganu akai sai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce, ku tashi ku ba ni wuri! Bai kuma sake wannan maganar ba a sauran wuni hudu da ya yi bayan haka a duniya.

Zamansa Khalifan farko

Ba zai yiwu ga duk wata al’umma mai cin gashin kanta ba, ta wayi gari kuma ta maraita ba tare da wani shugaba a kanta ba. Wannan shi zai fassara irin hanzarin da aka yi wajen tsayar da wanda zai gaji Manzon Rahmah Sallallahu Alaihi Wasallama.

A yammacin ranar Litinin ne Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya cika a cikinta (ya yi wafati), Sayyadina Abubakar Radiyallahu Anhu ya samu labarin cewa, Ansaru, mutanen Madina sun yi gangami a wani waje da ake kira Sakifa (can Arewacin birni madina), sun fara nazarin sha’anin khalifanci a bayan Manzo Sallallahu Alaihi Wasallama. Kai tsaye Sayyadina Abubakar Radiyallahu Anhu ya tasar ma wurin wannan taron na Ansar domin ya gane ma idonsa irin wainar da ake toyawa. A tare da shi akwai mutane biyu daga cikin manyan Muhajirai, su ne; Sayyadina Umar Xan Khaddabi da Amiru (Abu Ubaidata) Xan Jarrah Radiyallahu Anhuma waxanda bisa ga sa’a ne ya haxu da su ba tare da an je nemansu don su halarci taron ba.

Da Sayyadina Abubakar Radiyallahu Anhu ya iso wurin taron sai ya nemi su gabatar masa da bayanin abin da su ke ciki. Magabata daga cikinsu su kayi jawabai cike da yabawa ga kawunansu da bayyana irin matsayinsu a Musulunci. Sayyadina Umar Radiyallahu Anhu ya so a ba shi dama ya yi magana, amma Sayyadina Abubakar ya nemi ya dakata. Sannan shi Sayyadina Abubakar Radiyallahu Anhu ya yi wani gajeren jawabi wanda ya tabbatar ma Ansaru da duk abin da suka fadi na falala har ma da qari a kan hakan. Ya kara da cewa, amma kuma kun sani mutane ba za su iya miqa wuya ga wata qabila ba sai ta Kuraishawa. Wannan shi ya sa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ba da umurnin tsayar da khalifanci a cikinsu. Sannan ya tambayi xaya daga cikin manyan shugabannin Ansar, Sa’adu Xan Ubadah Radiyallahu Anhu (wanda shi ne Ansar su ke son su naxa a matsayin khalifa) cewa, ko ka ji wannan bayani daga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama? Sa’adu ya ce, eh. (Al Musnad na Al Imamu Ahmad wanda Sheikh Ahmad Shakir ya yi tahkikinsa, (1/18)).

 

Za mu dakata a nan, sai wani makon mai zuwa idan Allah ya kai mu da rai da lafiya za mu cigaba. Kar ku manta kuna tare da xan ‘yar uwarku, Mohammed Bala Garba, Maiduguri. 08098331260.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: