Connect with us

ADABI

Wane Ne Narambada?

Published

on

Wane Ne Narambada?

Daga Farfesa Aliyu Muhammadu Bunza

 

Sharar Fage:

Yau Ne Taron Tunawa Da Makada Ibrahim Narambada Tubali:

Jagora: Wa Dandada wa Alu nan wa ne Gurso,

‘Y/Amshi: Wa ne Jankidi da Zamau mai dan kotso

Jagora: Debe batu Nagaya ko Akwara yat taso

‘Y/Amshi: Ko shata da shi da Kurna yayan Kwairo

Jagora: Ba su kama da Iro mai murya ratata.

Gindin Waka: Gwarzon Shamaki na malam toron giwa

Babban dodo ba a tamma da batun banza.

Shekarar Makadi Ibrahim Narabada 56 da rasuwa, amma saboda gagarumar gudunmawar da ya bayar a bangaren waka da duniyar adabi ba za ta taba mantawa da shi ba. Jami’ar Bayero da ke Kano , karkashin shugaban Centre of Nigerian Languages Farfesa Aliyu Mu’azu ta shirya wannan gagarumin taro na kasa da kasa don karawa juna kan makada Ibrahim Narambada wanda za a gabatar a sabuwar jami’ar daga 15-17 ga watan satumba 2019. Manazarta da masana da dalibai da masu sha’awar waka daga ciki da wajen kasar nan za su halarta.

 

Wane Ne Narambada? Ibrahim Narambada Buhari Maidangwale Abdulkadir Tubali (1890-1963)  Daga Aliyu Muhammadu Bunza,

Tsangayar Fasaha da Ilmi, Sashen Harsuna da Al’adu, Jami’ar Tarayya Gusau

Takardar “Jagora” da aka gabatara a taron kara a juna sani na kasa da kasa wanda Centre for Research in Nigearian Languages, Translation and Folklore ta gabatar a kan Life History, Wisdom and Contributions of Ibrahim Narambaɗa Tubali to Hausa Studies, 15-17 ga watan Satumba 2019, domin karrama Janar Ibrahim Badamasi Babangida, karkashin jagorancin Ministan Ilmin na Кasa Alhaji Adamu Adamu.

 

Tsakure

Na yi wa takardata take: “Wane ne Narambada” domin share fage masu ayyukansa da masu son su san shi. A binciken an yi amfani da ra’in kamar Kumbo kamar kayanta domin a fito da hoton Narambada cikin wakokinsa. Domin kai ga nasarar bincike. An gabatar da rangadi, garin Tubali da masarautar da ya yi wa waƙoƙi. An tattauna da su, da iyalansa, da abokansa da masana waƙoƙinsa da halayensa. An yi ƙoƙarin kwatanta abubawan da aka samo da shahararrun waƙoƙinsa. Don haka, an leko fitattun wakokin Narambada (40) aka tsinto diyan wakoki (51) aka dora nazarinsu a fasula (16). Taken takardar an dora shi a kan tambayoyi (12) wadanda ake hakikanin cewa binciken ya fito da amsoshin su. Binciken ya gabatar da shaharar Narambada a fagen wakokin Sarauta kuma har ya bar duniya sai dai a ce kaico! Kama da wane ba wane ba ne. An ci nasarar fito da sakamakon bincike (5) da shawarwari (5) domin taskace ayyukan Narambada. An haifi Ibrahim Narambada Buhari Maidangwale Abdulkadir a Tubali kasar Shinkafi jihar Zamfara 1890 ya rasu 1963 ya na dan shekara 73, a yau shekarar 2019, yana da shekara 56 da rasuwa. Allah Ya gafarta ma sa. Amin!

 

Gabatarwa

Da wuya a fadi wani abu sabo a kan makada Narambada da magabata ba su hango ba. Duk da haka, ba a rasa tsintuwar dami a kala ba. Makasudin wannan dan bincike shi ne tattaro gutsattsarin labarai da bayanai da suka shafi Narambada domin a tace fitaccen batu da zai fito da hakikanin hoton Narambada a duniyar adabin Hausa. Babban buri shi ne, fayyace takaitaccen tarihinsa da fasaharsa da halayensa da gurbinsa a duniyar mawakan baka na Hausa. Nazarin zai yi madogara da yadda wakokin Narambada ke bayyana wane ne Narambada ga wadanda suka san shi da wadanda ba su san shi ba. Shaharar Narambaɗa a duniyar ƙasar Hausa ta fi ta ƙasar Isa da Sarkin Gobir da yake yi wa waƙa. Waƙar Ɗanhilinge hujja ce:

Jagora: Sarkin Gobir na da doki irin :Irin dokin ga da yay yi suna

Yara: Ga talitta komiy yi suna :Mutane na shagalin ganinai

 

Dabarun Bincike

Binciken da na yi a kan makada Narambada na tsawon shekaru 5-10 ya ba ni damar fahimtar wane ne makada Narambada? Kundin digirin farko da ya fara leƙo Narambaɗa shi ne Udu (1972). Haka kuma, Bello (1979) ya ƙyallaro rayuwar makaɗa Narambaɗa da waƙoƙinsa. Babban aikin PhD na Sada (1982) ba a kammala shi ba a SOAS, Jami’ar Ingila (ɗalibin ya rasu). Gusau (1987) ya juya jerin wasu waƙoƙinsa. Bunza (1998) ya yi yunƙuri irin na wannan takarda ya taƙaita su ga falsafar waƙoƙinsa. Shinkafi (1998) ya Harari shahararrun waƙoƙinsa. Matsakaicin aiki da aka yi kan Narambaɗa shi ne Bunza (2009) a matsayin wallafaffen littafi kan rayuwar makaɗa Narambaɗa da waƙoƙinsa. Ratsa waɗannan ayyuka ya ba ni ƙarfin guiwar shiga mataki na biyu na bincikena. Na tattauna da abokansa da diyarsa Hajo da mutanen garinsu Tubali da mutanen unguwarsu da wadanda suka san shi suka nazarci wakokinsa a Zamfara da kewayenta. Hannayena sun kai ga ayyuka da dama da aka yi a kan Narambada jiya da yau. Na samu kai ga dukkanin shahararrun wakokinsa da suka bayyana a gidajen rediyo da na garmaho da bakunan wasu hazikai masu sha’awar wakokinsa. Bayan na yi kakaci cikin wakokinsa sosai sai na shiga hira da tattaunawa da wadanda suka san shi a raye suka yi hulda da shi, suka zaune shi, suka san wani sirri daga cikin sirrin wakokinsa. Wannan ya ba ni damar tunanin cewa, lallai ina iya fitowa da kyakkyawan tarihin Narambada da halayensa bisa ga luguden wakokin da ya zuba a rayuwarsa. Shirin shiga ruwa tun tudu ake kimtsa shi domin makada Narambada ya ce:

Jagora: Ah ji wanda bai san hanya: Ya yi sabko amma fa ya bace ya dawo

Yara: Ila da yat tahi bai dora tambayan kowa ba Gindi: Ginshimin Haliru uban zagi na Malam Isa

:Gagarau jikan Shehu Iro toron giwa

 

Ra’in Bincike

Ina daya daga cikin daliban da ke da ra’ayin cewa, a fagen ilmi, lokaci ya yi ga kowane tsuntsu ya yi kukan gidansu. Matukar muna tsayi a yi kare jini biri jini mu kwato ‘yancin kanmu mu tabbatar da kasarmu ta gado bisa ga dokokin da suka dace da al’adunmu, dole ilminmu na cin gajiyar duniyarmu ya rausaya amon gangarmu ta gado. Ban ce, a yi watsi da ra’o’in bincike na Turai ba, amma da wace hujja za mu dunkule namu idan suna isar da sako daidai da tunaninmu? Na dora wannan bincike a kan tunanin Bahaushe da ke cewa: “Kamar Kumbo kamar kayanta”. Idan a ka sa natsuwa aka dubi tarkacen Kumbo da kyau, za a gano ina ta fito? Ina za ta? Ina kayanta na asali? Ina wadanda ta saya? Ina wadanda a ka ara ma ta? Wane labari tarkacenta za su bayar na halayenta? Babu shakka, kayan da Narambada ya taskace cikin manyan wakokinsa sun isa su fito da cikakken hotonsa.

 

Gudummuwar Narambada da ta karfafa ra’inmu ita ce:

Jagora: Dan bajini shi ka zama bajimi Yara: Yai bobakali yai tozo

:Dan akuya na kallo.

Gindi: Na rika ka da girma Abdu kanen mai daga.

 

Tambayoyin Bincike

Irin wannan bincike yana bukatar a daidaita akalarsa ga manyan turakun da ake son a daure shi. Babbar tambaya a nan ita ce, yaya al’umma ke kallon makada Narambada da yadda shi ya ke kallon kansa? Wane gurbi yake ciki daga cikin gurabun mawakan Hausa? Yaya shahararsa take a cikin shahararrun mawakan Hausa? Me ya bambanta shi da sauran mawaka a cikin sana’ar waka? Wadanne ne shahararrun wakokinsa? Wace ce bakandamiyarsu? Wane sirri ke cikin wakokinsa na ratsa zukatan masu sauraro? In an samu dacewa da fashin bakin wadannan tambayoyi sai mu ce, komai ya yi an ba gwauro ajiyar mata. Wadannan tambayoyi da na tsara bayaninsu makada Narambada ya ce:

Jagora: Taro na tambaye ku :Shin kowag ga wuta

Yara: An ka ce a debo, wa ka zuwa? :Wanda yag gani ka zuwa

:Kowas shaida shi ka shan rana :In bai tai ba yai batun banza

:Ko can dauri shi batun banza :Dadin hwadi garai

Gindi: Ya ci maza yak wan shi na shire :Gamda’aren Sarkin Tudu Alu.

 

Za mu cigaba in sha Allah.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: