Connect with us

DAGA BIRNIN SIN

Yan siyasar Amurka ba za su cimma bukatar su ta goyon bayan masu neman ‘yancin Hong Kong ba

Published

on

Yau Alhamis gidan rediyon kasar Sin wato CRI, ya gabatar da wani sharhi mai taken “Yan siyasar Amurka ba za su cimma bukatar su ta goyon bayan masu ra’ayin neman ‘yancin yankin Hong Kong ba”, inda a cikin sharhin aka bayyana cewa, shugabar majalisar wakilai ta Amurka Nancy Pelosi, ta yi ganawa da Joshua Wong, da Denise Ho, da sauran masu ra’ayin neman ‘yancin Hong Kong a Washington a jiya, lamarin da ya nuna cewa, suna da makarkashiyar tayar da tarzoma a Hong Kong, amma ko shakka babu ba za su cimma burin su ba.

Sharhin ya jaddada cewa, Hong Kong yanki ne na kasar Sin, kuma ba zai yiwu gwamnatin kasar Sin ta amince da kasashen waje su tsoma baki a cikin harkokin Hong Kong, da harkokin cikin gidan kasar ba.
Daukacin al’ummun kasar Sin za su yi adawa ga makarkashiyar lalata manufar “kasa daya, tsarin mulki iri biyu”, da wadata da zaman lafiya na Hong Kong. Kaza lika idan yankin Hong Kong ya gamu da matsala, wadda gwammnatin yankin ba ta iya warwarewa ba, gwamnatin tsakiyar kasar Sin ba za ta gaza wajen kula da yankin ba. Ko shakka babu Sin za ta dauki matakai na wajibi cikin lokaci.
Sharhin ya ce ana sa ran ‘yan siyarar Amurka, za su daina tsoma baki a cikin harkokin Hong Kong, idan kuwa ba haka ba, za su kuka da kansu.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: