Connect with us

LABARAI

Da Ya Soke Mahaifinsa Da Wuka Har Lahira

Published

on

’Yan sanda a Jihar Kano sun tabbatar da kama wani matashi mai shekaru 35 da haihuwa, mai suna, Habibu Ibrahim, da ke kauyan Asada, ta karamar hukumar Doguwa, a Jihar ta Kano, a bisa zargin da ake yi masa da sukar mahifinsa, Malam Ibrahim Salihu, da wuka wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar mahaifin na shi mai shekaru 80 da haihuwa.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, wanda ya tabbatar da aukuwan lamarin cewa ya yi wani dan’uwan wanda ake tuhuman ne mai suna Yahaya Ibrahim, ya kai rahoton aukuwan lamarin a ofishin ‘yan sanda da ke Asada, Doguwa, a ranar 15 ga watan Satumba, 2019, inda ya ce kanin sa mai suna Habibu ya soki mahaifinsu da wuka a ciki da misalin karfe 1:30 na asubahi.

A sakamakon samun wannan rahoton ne jami’an ‘yan sanda da ke wajen suka hanzarta kai wanda aka sokan babban asibitin da ke Doguwa a inda daga baya ya cika a can a lokacin da ake kokarin yi masa magani da misaln karfe 6:30 na safiya.

Kiyawa ya ce bayan gudanar da bincike a kan gawar mamacin an mika wa iyalansa gawar domin su yi masa jana’iza.

“Binciken farko da aka yi ya nuna cewa wanda ake tuhumar ya aikata laifin ne a lokacin da yake buge a cikin maye, da miyagun kwayoyi.

“’Yan’uwan wanda ake tuhumar sun koka mana a kan yanda Habibu yake tu’ammali da miyagun kwayoyi wanda hakan ne ya yi sanadiyyar mutuwar mahaifin na su.

Ya ce Kwamishinan ‘yan sanda, CP Ahmed Iliyasu, ya yi umurni da a tsare wanda ake tuhumar a sashen masu binciken aikata muggan laifuka domin ci gaba da bincikarsa sosai.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: