Connect with us

RIGAR 'YANCI

DisCos Ga Gwamnatin Tarayya: A Girmama Ka’idar Kwangilar Lantarki

Published

on

A ranar Talata ce, Kamfanonin rarraba hasken lantarki suka nemi gwamnatin tarayya da ta girmama ka’idojin yarjejeniyar kwangilar rarraba hasken lantarkin da aka cimmawa da masu zuba jari a sashen na samar da hasken lantarki na kasar nan.

A sakamakon yarjejeniyar da aka shiga a kan aikin samarwa da rarraba hasken lantarkin, ana sa ran kiyaye yarjejeniyar a tsakanin masu zuba jari da kuma gwamnatin tarayya a bisa yarjejeniyar mai saye da mai sayarwa.

Daga cikin ikon da ke cikin yarjejeniyar akwai kananan da kuma manyan abubuwan da suka shafi biyan kudin lantarkin, wanda ke karkashin ikon kamfanin kula da hasken lantarki na kasa tun daga shekarar 2015.

Babban daraktan bincike na kungiyar kamfanonin da suke rarraba hasken lantarkin, Barista Sunday Odutan, a jiya ya nanata cewa, gwamnatin tarayya tilas ne ta girmama ka’idojin yarjejeniyar da aka cimma da ita a kan ayyukan kwangilar.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: